Babi Na Farko

Babi Na Farko

BABI NA FARKO


TARIHIN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) A TAƘAICE:

SALSALARSA:
Tarihi mafi inganci da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayar da kansa, ya faɗi cewa asali iyayensa sun fito ne daga Magrib (Moroko); Daga nan suka zo birnin Shingidi na tsohuwar daular ƙasar Mali, amma yanzu birnin na Shingidi mai tsohon tarihi yana ƙasar Mauritaniya ne, daga garin Shingidi kakanninsa suka yo ƙaura zuwa birnin Mabruk da ke ƙasar Mali, daga nan kuma suka zauna a birnin Timbuktu, daga birnin Tumbuktu ne kuma suka taho wannan ƙasa Nijeriya cikin karni na 12. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 09 zuwa 11).

NASABARSA:
Salsala ko nasabar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta jero ne kamar haka; Shaikh Ibraheem dan Ya’aÆ™ub, É—an Aliyu, É—an Muhammad Tajuddeen, É—an Liman Hussain Batoronke, shi Liman Hussain Bafulatani ne daga kabilar Toronkawa wanda ya zo kasar Hausa daga Mali a zamanin Shehu Usman bin Fodiye, inda ya zama babban limami a garin da yake zaune a yankin Sakkwato. Daga bisani sai É—ansa Malam Tajuddeen wanda almajirin Shaikh Usman bin Fodiye ne ya biyo tawagar wakilin Danfodiye na Zazzau, wato Sarkin Zazzau Malam Musa suka taho Zariya tare dan ya rika karantarwa.
Mafi yawan tarihin da ake rubutawa na salsalar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) yana tukewa ne akan Liman Hussain, watakil don gudun tsawaitawa, domin jerin nasabar Shaikh (H) tana tukewa ne ga Imami na biyu cikin limaman shiriya na Ahlul-Bait (AS), wato jikan Manzon Allah (S) Imam Hasan Al-Mujtaba bin Aliyu bin Abi-Talib (AS), É—an Sayyida Fatimah Az-Zahra (SA), wan Imam Husain shahidin Karbala (AS).

MAHAIFINSA:
Sunan mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Malam YaÆ™ubu Aliyu, ana masa laÆ™abi da Malam Magaji, tarihi bai ambaci taka meme shekarar da aka haifi Malam YaÆ™ubu Aliyu ba, Amma ana kyautata zaton an haife shi ne a shekarar 1902. Ya taso a gidan malanta da ilimi, dan haka ya taso ne da karatu da riÆ™o da addini, tun tasowarsa mutum ne mai haÆ™uri da sanin ya kamata, an shaide shi da kyawawan dabi’u da aiki da abin da ya karanta. Sana’arsa ita ce koyarwa da kuma Noma da Kiwo. Ana kyautata zaton ya rayu a duniya ne tsawon shekaru 70 daidai (1902 – 1972), ko shekaru 72 a Æ™idayar Hijiriyyah.

Allah ya yi wa mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Malam YaÆ™ubu Aliyu rasuwa ne a watan Fabarairu na shekarar 1972, ya rasu ne a wani kududdufi da ke bayan unguwar Kwarbai cikin birnin Zariya, a lokacin da ya je ceto wata Akuya da ta faÉ—a cikin kududdufin lokacin da ta je shan ruwa, kuma an yi masa jana’iza aka binne shi a maÆ™abartar da ke kusa da kududdufin, yanzu haka kabarinsa yana wurin. Ya rasu ya bar ‘ya’ya 16, maza takwas, mata takwas.

MAHAIFIYARSA:
Malama Salaha Muhammad Gidado, wacce aka fi sani da Hajiya Hari Jamo ita ce mahaifiyar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Bafulatanar usuli ce daga kabilar Fulani Toronkawa, kakanta Malam AbdulÆ™adir ya taho ne daga Æ™asar Mali ya aza zango a Zariya. LaÆ™abinta na “Hari” a harshen Fulatanci yana nufin “Wacce aka haifa a Damina”. An haifi Hajiya Salaha ne a shekarar 1924 a cikin birnin Zariya. Ta haifi ‘ya’ya 12 da mijinta Malam Yakubu, amma 5 daga ciki sun rasu tun suna kanana, kuma Shaikh Zakzaky (H) shi ne da na biyar a wurinta.

Mahaifiyar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) Hajiya Salaha (Hari Jamo) malama ce mai ilimin addini, ta kasance tana karantar da mata makwabta da matan unguwa da kuma Æ™ananan yara a cikin gida. An shaideta da yawan ibada, musamman karatun AlÆ™ur’ani da yawan addu’a. Ta rasu ranar 17 ga watan Nuwamba na Æ™arshen shekarar 2014 (25-Muharram-1436), sakamakon jinyar da ta yi fama da ita, kuma ta rasu tana da shekaru 90 daidai a kidayar Bature (1924-2014), ko shekaru 93 a kidayar Hijira. Ta bar ‘ya’ya 6 da jikoki masu yawa, kabarinta yana Hubbarenta da ke unguwar Jushi a cikin birnin Zariya.

ƳAN UWANSA:
Mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wato Malam YaÆ™ubu Aliyu, ya rasu ya bar ‘ya’ya goma sha shida ne cif a duniya, takwas maza, takwas mata, su Shaikh Zakzaky (H) su bakwai ya bari ta wajan mahaifiyarsu Hajiya Salaha, wato wanda suka haÉ—a uwa É—aya uba É—aya, maza huÉ—u, mata uku, ga su a bisa jerinsu;

  1. Abdulƙadir Yaƙub
  2. Maryam Yaƙub
  3. Fatimah Yaƙub (Goggon Ƙaura)
  4. Ibrahim Yaƙub (Sheikh Zakzaky)
  5. Badamasi Yaƙub
  6. Yahya Yaƙub,
  7. Sai ‘yar autarsu
  8. Maimunatu Yaƙub.

Ta É“angaren sauran ‘yan uwan Shaikh Zakzaky guda 9 kuwa, sun haÉ—a mahaifi ne kawai da su, wato mahaifinsu É—aya, Amma mahaifiyarsu ita ce Hajiya Aminah wacce ake kira (Iya mai Manja), su tara ne, maza huÉ—u, mata biyar, ga su a bisa jerinsu;

  1. Muhammad Sani Yaƙub,
  2. Ramatu Yaƙub
  3. Karimatu Yaƙub
  4. Usman Yaƙub (Sarkin Malaman Fadar Zazzau)
  5. Maryam Yaƙub
  6. Abubakar Yaƙub
  7. Salihu Yaƙub
  8. Zaliha Yaƙub
  9. Sai ‘yar autarsu
  10. Hajara Yaƙub.

A jumlace, wadannan sune ‘yan uwan Shaikh Zakzaky (H) na jini, kuma Shaikh (H) ne da na shida a wajan mahaifinsu, Amma na biyar a wajan mahaifiyarsa, (bisa lissafawa da wansa Zubairu Yakub, wanda ya rasu yana karami).

HAIHUWARSA:

An haifi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne gab da hudowar Alfijir na ranar Talata 15 ga watan Sha’aban 1372 Hijiriyya, wanda ya yi daidai da Talata 5 ga watan Mayu shekara ta 1953 Miladiyya. An haife shi ne a bayan Fada da ke unguwar Kwarbai cikin birnin Zariya jahar Kadunan Nijeriya.

SUNA DA LAƘABINSA:
Sunan jagora shi ne Ibraheem, lakabinsa kuma Al-Zakzaky, wanda fassararsa ke nufin mutumin Zariya, wato mutumin ƙasar Zazzau, ko Bazazzagi a taƙaice. Lakabin Al-Zakzaky ya samo asali ne a lokacin yana makaranta, sai ya zamo su biyu sunansu ya zama iri ɗaya (Ibrahim Yakubu), sai aka ce kowa ya kara suna ɗaya a jikin nasa, sai Shaikh ya kara Zakzaky a jikin sunansa, daga nan ake kiransa Al-Zakzaky.

Wani lakabinsa da ya shahara shi ne laÆ™abin da Shaikh Usman bin Fodiye ya laÆ™aba masa tun sama da shekaru 200 kafin haihuwarsa, wato lakabin Sharafuddeen, wanda fassararsa ke nufin “Mai ÆŠaukaka Addini”. Sai kuma laÆ™abin Ibraheemul-Magriby, wanda ke nufin “Mutumin Yamma” wanda shi ma laÆ™abi ne da ya samo asali daga zantukan waliyai magabata. Sannan akwai laÆ™abin “Khaleel” wanda iyalinsa Malama Zeenatuddeen ce kaÉ—ai take kiransa da wannan laÆ™abi. A taÆ™aice Shaikh (H) yana da laÆ™ubba guda uku, wato Zakzaky, da Sharafuddeen, da Al-Magriby, sai kuma na khass da iyalinsa ke kiransa da shi, wato Khaleel.

SIFFOFINSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) baƙin fata ne mutumin Nijeriya a Afirka ta yamma. Matsakaici ne a tsawo Amma ya fi kusa da gajarta. Yana da matsakaiciyar kiba. Kyakkyawa ne mai kyan sifa da kyan diri. Yana da manyan idanu matsakaita girma. Yana da faffaɗan goshi, da faffadan ƙirji, da karan hanci. Yana da hasken fata da madaidaitan kunnuwa. Yana da mayalwacin gemu Amma bai da ƙasumba. Yana da tsaga bibiyu a kwibin idanuwansa biyu, wanda hakan ke alamta cewa shi Bamalle ne a kabilar Fulani. Ta ko ina bai da nakasa a halitta. Yana da cikar kwarjini da Haiba. Yana da izza a cikin tafiya da zamansa. Haziƙi ne mai fikira da hangen nesa. Fasihi ne mai fasahar magana. Ɗan baiwa ne a ilimi, Fikira da sanin fannoni.

YARINTARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya taso a gida na addini da tarbiyya, dan haka tun yana yaro ƙarami ya gudanar da yarinta ce mai tsabta, sam ba a san shi da ƙin jin magana, ko faɗa da yara, ko mugunta da ƙeta, ko nuna fin ƙarfi ga wanda ya fi ba. An san shi ne a matsayin yaro mai dattaku, mai tarbiyya, mai girmama na gaba, mai ladabi ga iyaye, mai tausayin kanne, mai taimakon tsofaffi, mai son karatu, kuma mai ƙwazo da rashin kasala.

Iyaye da ‘yan uwan Shaikh Zakzaky (H) sun tabbatar da cewa tun yana Æ™aramin yaro bai taÉ“a zuwa neman Æ™arin miya ba, wato in an zuba masa abinci komai Æ™arancin miya ba zai ce a Æ™ara ba, kuma in yana cin abinci miya ta Æ™are, to ko bai Æ™oshi ba haka zai haÆ™ura, Amma ba zai je ya ce a Æ™ara masa miya ba. Wannan yana nuna halin dattaku da Makarimul-AkhlaÆ™ É—in Shaikh (H) ne tun yana Æ™aramin sa.

Wanda suka san tasowa da yarintar Shaikh Zakzaky (H) sun tabbatar da kyawawan halayensa na yarinta. Dattijo kuma É—an Sarkin Zazzau Aliyu ÆŠan Sidi, wanda aka fi sani da Alhaji Basiru Aliyu ÆŠan Sidi ya faÉ—i cewa; “A wancan lokaci (na yarinta), sanin da na yi wa Malam Ibraheem Zakzaky yaro ne mai hankali da biyayya ga na gaba da shi, tare da dattako, ban kuma taÉ“a jin wani abu na laifi ko kuma aibu akansa ba!” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 84).

Shi ma MagayaÆ™in Zazzau Alhaji Abubakar Jibrin ya faÉ—i cewa; “Ni dai na san shi (Ibraheem Zakzaky) yaro ne mai kawaici, sannan bai cika maganganu haka barkatai ba… A makarantun da ya yi yana da ladabi da biyayya ga duk na gaba da shi a yawan shekaru, domin mu nan ba mu samu wani abu da za mu soka ga me da shi ba” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 82).

Wata dattijuwa ‘yar kimanin shekara 100 daga zuriyar gidan su Shaikh Zakzaky (H), wacce ake kira Goggo Fatimah, ta bada kyakkyawar shaida akan yarintar Shaikh É—in, ta ce; “Shi dai lokacin da aka haife shi mun ga abin mamaki… tun farko mun ga alamar zai zama wani abu. Yana da biyayya Æ™warai da gaske. Mutum ne mai zumunci, ya san nasa, duk inda suke zai sa Æ™afa ya bi su da alheri, dama (tun asali) da alherinsa ya taso, ba yanzu ne ya fara ba, tuntuni haka yake… Tun yana yaro bai san faÉ—ace-faÉ—acen nan na yara ba, ba ruwansa, shi ya taso kamar Dattijo ne, tun yana yaro kamar dattijo yake, irin sakarcin nan ma na yara shi ba ya yi, sai ma idan yara sun yi abun da bai dace ba, sai ka ga ya tsawatar musu” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 68).

Wani abokin Shaikh da suka taso tare, mai suna Malam Wadan Mai Rakumi yana cewa; “Ibraheem mutum ne wanda tun yana yaro ba ya son wasa ko wulaÆ™anta addini, (sannan) shi ba ya irin mugun wasannin nan da yara kan yi, ko a unguwa ko a makaranta, idan mun zo muna yin (mugun wasa) sai ka ga ya koma gefe guda abinsa” (Mujallar Gwagwarmaya, fitowa ta 3, shafi na 24).

A taÆ™aice, Shaikh Zakzaky (H) rinin Allah ne, tun tasowarsa ya taso ne a matsayin kamili mai halin dattaku, duk wani sheÉ—anci na yara bai yi shi ba, da kamala da kyawawan halaye ya taso. Kenan halaye da É—abi’un Shaikh Zakzaky (H) rinin Allah ne, tun ran gini ran zane !

KARATUTTUKANSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ma’abucin ilimi ne da ya yi karatu mai zurfi a fannonin ilimi guda biyu, wato karatun addini da kuma na zamani (Boko), kuma a lokacin yin wadannan karatuttuka ya bi ta hanyoyi biyu ne da aka saba bi bisa al’ada, wato tsarin karatun gida (karatun Zaure), da kuma tsarin karatun Nizamiyya na makarantun zamani.

  1. Karatunsa na Zamani:
    A fannin karatun zamani na Boko, ko mu ce karatun Nizamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara karatun ne yana da shekaru 17 a duniya, dan haka bai yi karatun Primary kai tsaye ba. Ya fara shiga makarantar horar da malaman Larabci da ake kira “Fada Provincial Arabic School, Zaria” ne a shekarar 1969 zuwa 1971. A shekara huÉ—u ake gama wannan makarantar, Amma saboda basirar Shaikh da hazaÆ™arsa ya kammala ta ne cikin shekaru biyu kacal. A lokacin da yake karatu a wannan makaranta ta FPAS yana koyarwa a makarantun Islamiyyah har guda huÉ—u, É—aya a unguwar Kwarbai, É—aya a unguwar Kakaki, É—aya a unguwar Lemu, É—aya kuma a Rimin Tsiwa duk dai a cikin garin Zariya.
  2. A tsakiyar Shekarar 1971 ya tafi makarantar koyon harshen larabci “School for Arabic Studies” da ke birnin Kano don zurfafa karatun harshen Larabci, Amma bayan an yi masa gwaji (Interview) an ji ya iya turanci, sai shugaban makarantar ya canza masa ra’ayi daga karatun harshen Larabci zuwa karanta darussan Turanci. Ya kammala wannan makaranta ne a shekarar 1975.

    A lokacin da yake karatu a S.A.S Kano ya gwama karatun “Grade Two” É—insa ne da karatun darussa huÉ—u na “Advance Level”, darussan kuwa sune; Economics, Government, Islamic Studies, da kuma Hausa, dan haka bayan ya kammala jarabawar “Grade Two” sai kuma ya zarce da ta “Advance Level” a lokaci guda. Da jarabawowin guda biyu suka fito, sai ya zamo duk ya ci su, takardunsa duk sun yi kyau, wannan ne ya ba shi damar samun karatun digiri kai tsaye a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ya kasance yana halartar karatuttukan addini a zaurukan manyan malamai da dama na birnin Kano a lokacin da yake É—alibta a can.

    Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU Zariya) ne a shekarar 1976, inda ya karancin fannin tattalin arziÆ™i (Economics). Ya kammala digirinsa a shekarar 1979, Amma a lokacin da yake jarabawarsa ta Æ™arshe ta kammala karatun, sai jami’an tsaro suka kama shi suka tsare bisa tuhumar hana wasu mashaya giya yin taronsu na fasadi a harabar makarantar, wannan ya sa bai samu damar yin wasu takardu (Papers) na jarabawarsa ba, har sai da aka sako shi daga kurkukun Inugu a 1984, sai hukumar makarantar ta ba shi damar Æ™arasa jarabawar tasa, amma bayan ya rubuta jarabawar suka ga ya yi nasara, sai suka riÆ™e sakamakon suka hana shi, wato har zuwa yau hukumar jami’ar ba su ba Shaikh Zakzaky (H) digirinsa ba. Amma rahotanni sun tabbatar da cewa shi ne É—alibi mafi hazaÆ™a a wannan shekarar, wato ya fita da “First Class” ne.

    A jumlace, za mu iya cewa, karatun Boko daga fara shi zuwa kammala digiri, ana yinsa ne a tsawon shekaru goma sha tara (19), amma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya kammala karatun zuwa digiri ne a tsawon shekaru Goma (10) kacal! Domin karatun shekaru bakwai na Firamare, ya yi shi ne a shekaru biyu kacal a FPAS Zariya. Karatun shekaru shida na Sakandire kuma, ya yi shi ne a shekaru huÉ—u kacal a S.A.S Kano. Sa’annan ya yi digirinsa a ABU Zariya cikin shekaru 4. Wannan zai nuna baiwa da hazaÆ™a ta musamman da Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Zakzaky (H) ne.

    Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a lokacin É—alibta ya riÆ™e muÆ™amai a Æ™ungiyoyin É—alibai na cikin makarantun da ya yi, Amma mafi fice shi ne muÆ™aman da ya riÆ™e a Jami’a. A shekarar 1978 ya zama babban sakataren Æ™ungiyar É—alibai musulmi “Muslim Students Society” (wato MSS a taÆ™aice) a jami’ar Ahmadu Bello, sannan daga baya ya zama mataimakin shugaban Æ™ungiyar ta MSS na Æ™asa baki É—aya mai kula da harkokin Æ™asashen waje a 1979.

  3. Karatunsa na Addini:
    Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya taso ne a gida na ilimi da addini, gidansu gidan malamai ne masu riÆ™o da addini da koyarwar musulunci, dan haka Shaikh ya taso ne da karatun addini wanda ake kira “Karatun Zaure”. Ya fara karatun AlÆ™ur’ani ne a gaban mahaifinsa tun yana É—an shekara huÉ—u da haihuwa, ya kuma fara karatun ilimin Nahwu ne a wajan kakarsa Malama Hajara, wacce ake wa laÆ™abi da “Mai Karatu”.
  4. Tun Shaikh yana Æ™arami ya yi karatun addini mai zurfi, domin ya kasance yana haddace duk karatun da aka yi masa, har ma yana haddace karatuttukan na gaba da shi da aka yi a gabansa. Ya yi karatu a gaban manyan malamai da dama a birnin Zariya. Kusan ya karanta duk wani littafin addini da ake karantawa bisa tsarin karatun zaure, kuma ya karanta dukkanin fannonin ilimi da ake karantawa a Zaure, kama daga karatun AlÆ™ur’ani, FiÆ™hu, Usul, Hadisi, Tarihi, Luga, Sarf, Nahwu da sauransu.

    Ya yi waÉ—annan karatuttuka ne a gaban mahaifinsa Malam YaÆ™ubu, da kakarsa Malama Hajara Mai Karatu, da fitattun gidajen ilimi na Zariya, daga ciki ya yi karatu a gidan Ladanai, da wajan Malam Sani AbdulÆ™adir Fateh, da Malam Sani Na’ibi, da Malam Isa Kwarbai, da Malam Ibrahim Nakakaki, da Malam Aminu na Madaka da sauransu.

    Sannan ya zurfafa karatun fannonin ilimi a zamansa na Kano a gaban Shaikh Nasiru Kabara, da Shaikh Isa Waziri (babban limamin Kano), da Malam Nuhu limamin Unguwar Yola, da Malam Datti Ahmad (Æ™wararren malamin Luga da Adabi), da Malam Ibrahim Babarbare, da kuma Shaikh Abdur-Ra’uf Usman (wani malami É—an Æ™asar Masar). Duk waÉ—annan masana Shaikh (H) ya yi karatuttukan fannonin addini ne a wajansu.

    Shaikh Ibraheem Zakzaky ya ci gaba da halartar gaban manyan masana da malamai yana zurfafa bincike akan mas’alolin addini da faÉ—aÉ—a Bahasi a Æ™asasen waje. Misali; ya yi karatu na tsawon lokaci a Æ™asar Ghana, a gaban wani babban masani É—an Æ™asar Iran Sayyid Tabataba’i. Sannan tun a shekarar 2000 har zuwa 2015, kusan duk shekara yana zuwa Æ™asar Iran na tsawon wata biyu dan zurfafa karatu a gaban manyan malamai da masana fannonin ilimi daban-daban. Yana karatu mai zurfi a fannonin nazari da bahasi akan wasu mas’alolin addini, tare da zurfafa karatu a fannonin ilimin Falsafa, Irfani, ManÉ—iÆ™, Usoul, Shari’a, da sauransu.

SHARIFTAKARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sharifi ne, wato jikan Manzon Allah (S) ne ta nasabar mahaifinsa, wannan dalilin ne ya sa ake ce masa ‘Sayyid’ wato Sharif kenan a Hausance. Salsalar nasabar Shaikh Zakzaky ta tuÆ™e ne ga jikan Manzon Allah Imam Hasan Al-Mujtaba (AS), kamar yadda Shaikh É—in da kansa ya tabbatar a “Decumentry” da gidan talabijin É—in Æ™asar Indiya ‘MAULA-TV’ ya yi a kansa a shekarar 2015.

Ya ce “Asalin iyayenmu sun fito ne daga Magrib (Morocco kenan ta wancan lokacin)…. Sun tashi daga sassa zuwa sassa har suka zauna a Mali, Malin da ba Malin yanzu ba. Ana cewa suna daga cikin Sulala É—in Imam Hasanil-Mujtaba (AS), wanda suka zauni nan Æ™asar Magrib tukuna suka gangaro suka zauni Mali, sannan suka gangaro suka zo nan (Nijeriya)”.

Tun kafin Shaikh (H) ya bayyana shariftakarsa a fili, an samu wasu masana da suka sha cewa shi jinin Manzon Allah (S) ne, sai dai Shaikh Zakzaky (H) bai shelanta Shariftakarsa ba sai a wajajen shekarar 2004, bayan ya yi tafiya takanas zuwa ƙasar Mali don sada zumunci ga danginsa da kuma ƙarasa bincike akan nasabarsa mai alfarma.

A ranar da Shaikh Zakzaky (H) ke ayyana siyada ko shariftakarsa a wajan wani taron Maulidin Sayyida Zahra (SA) da ‘yan uwa mata suka shirya a Fudiyya Islamic Center (FIC Zaria), ya karanto ruwaya da ke cewa; “Allah ya la’ani wanda yake shi tsatson Annabi (S) ne amma ya É“oye nasabarsa, sannan ya tsinewa wanda ya nasabta kansa ga tsatsontaka da Manzon Allah (S) alhali Æ™arya yake yi”. A fakaice, Shaikh (H) ya nuna cewa lalura ce ta sa zai ayyana Shariftakarsa ba don alfahari ko neman É—aukaka ba.

Tattare da haka, Shaikh (H) ya nuna cewa ba zai sa baÆ™in Rawani ba, saboda a al’adar mutanenmu (Hausawa), baÆ™in Rawani bai da kima, domin bayin Sarakunan gargajiya ne ke sanya shi, dan haka mu anan ba zai dace jikan Annabi (S) ya sanya baÆ™in Rawani ba, maimakon haka, sai Shaikh (H) ya ce zai riÆ™a anfani ne da “Koren Ƙyalle” na ratawa a wuya, wanda zai zama shi ne alami na Siyadar jikokin Manzon Allah (S) a wannan Æ™asa tamu.

Wannan shelanta Shariftaka ta Shaikh Zakzaky (H) ta É“uɓɓugo da abubuwa da dama na raya al’amarin nasaba ga Manzon Allah (S), da bada kima ta musamman ga jikokin Annabi (S) a wannan al’umma tamu.

ISTIBSARINSA:
Duk da cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tsatson Manzon Allah (S) ne, to amma yanayi na Biy’a (Inviroment) ya sa an haife shi a cikin Sunni, kuma hatta karatuttukan addini da ya taso da su na Mazhabar Malikiyya ne ta Ahlis-Sunnah.

Babu tabbataccen batu game da takameme lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi riƙo da Mazhabar Ahlul-Bait (AS), to Amma ta bayyana ga mutane cewa Shaikh yana bin tafarkin Ahlul-Bait (AS) ne a shekarar 1980, a lokacin yana da shekaru 27 da haihuwa. Almajiransa (wanda kusan baki ɗayansu Ahlis-Sunnah ne) sun soma gunaguni game da yadda suka ga Shaikh ɗin ya soma yin wasu abubuwa sabbi da ba su sani ba a cikin Alwala da Sallarsa a wancan lokacin.

Shaikh Zakzaky (H) da kansa ya taÉ“a bada labarin wannan rashin fahimta da sashen almajiransa suka nuna a wancan lokaci, wanda hakan ke tabbatar da cewa ya fara fitowa fili yana aikata koyarwar Ja’afariyya a ibadarsa ne tun a 1980, ya ce; “Na san tun 1980 lokacin da aka yi ”Funtua Declaration” akwai waÉ—anda suka zo suka same ni, cewa sun ga na yi Alwala amma na shafa Æ™afa ne, sai na Æ™yale, sai wani ya ce musu; ai shi Shi’a ne, shi ya sa yake shafa a Æ™afa, amma ni ban ce musu komai ba, (sai) wani ya ce ya ga ina Ƙunuti ina É—aga hannu, shi ma na Æ™yale ban ce masa komai ba, wani kuma ya ce ya ji ni ina Tasbihi a Ruku’u a bayyane, shi ma sai na Æ™yale, duk dai na Æ™i in amsa masu.

“Wani lokaci kuma mun tafi Sakkwato a dai cikin shekarar 1980, sai nai Sallar Azuhur da La’asar, sai na karanta “Bismillahir-Rahmanir-Raheem” a bayyane, wani sai ya tambaye ni, ya ji a cikin Sallah na yi Bisimilla a bayyane, sai na ce masa e, Manzon Allah (S) ya kasance yana yin haka, saboda su mutane akan wannan, sai su yi faÉ—a, ko kuma su ce addininka daban ne, saboda haka ni ban so tun farko mu fitinar da mutane (ba)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 154).

A wani zama na Khass da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi da wakilan ‘yan uwa na manyan Da’irori a wancan lokaci, ya bayyana musu cewa; “Ana jira in ce ni Shi’a ne domin a tarwatse, to, ni Shi’a ne! Tun da can ni Shi’a nike akai, a Shi’ar ka sanni, in ba ka sanni a haka ba to ba ka da basira! Saboda haka a Shi’a nike, kuma Insha Allah a Shi’a zan mutu, kuma ina fata Allah ya tasheni da Shi’a a ranar Ƙiyama, ya kai ni mokomar Shi’a!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 155).

Kenan, a bisa wannan jawabi, duk wanda ya fahimci Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), to ya shigo ne ya samu Shaikh (H) a bisa aÆ™idar Shi’a da Wila’a ga Ahlul-Bait (AS) da kuma biyayya ga koyarwarsu, Amma saboda maslaha ta Biy’ar da yake rayuwa a ciki, da kuma tausayin kar mutane su fitinu su nesanci tafarkin tsiransu, ya sa Shaikh (H) bai bayyana wannan aÆ™ida da Mazhaba ta Ahlul-Bait (AS) a fili ba, ya bar abin ga kansa kawai, sai da yanayi ya kyautata sannan ya shelanta tare da ayyana tafarkin da yake riÆ™o da shi a fili, wanda sakamakon hakan ya sa miliyoyin almajiransa suka rungumi aÆ™idar ba tare da Æ™yama ba. Wannan ya sa Shaikh Zakzaky (H) ya zama mutumin da ya fi kowa nasarar canza akalar aÆ™idar miliyoyin mutane daga Sunnah zuwa Shi’a a tarihin Musulunci baki É—aya!

UWARGIDANSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana da mace É—aya, wannan kuwa ita ce Malama Zeenatuddin Ibraheem, ita ce mahaifiyar duk ‘ya’yansa, wato daga gareta zuriyarsa ta samu. An haifi Malama Zeenatuddeen ne ranar 14 ga watan Ogusta na shekarar 1961, a unguwar Sabon Gari da ke cikin garin Zariya. Sunan mahaifinta Malam Ibrahim, sunan mahaifiyarta Malama Maryam, su huÉ—u ne a wajan mahaifiyarsu kuma dukkaninsu mata, Nafisa Ibraheem, Maryam Ibraheem, Zeenatuddeen Ibraheem da Khadija Ibraheem.

Malama Zeenatu ta fara karatun firamare ne a wata firamare ta Mishon da ke Sabon Gari Zariya, daga baya ta koma Firamaren Jafaru, wato St, George Primary School Zaria, daga 1967 zuwa 1973. Daga nan ta tafi “Commercial College, Zaria” a shekarar 1977, ta kammala a 1979, sai ta tafi CAST Katsina, ta shekara biyu a can, daga nan sai ta shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1981 inda take karanta fannin aikin Banki, Amma ba ta samu damar Æ™arasawa ba sakamakon korarsu da makarantar ta yi saboda harkokin addini a sekarar 1982.

Daga nan Malama Zeenatu ta tafi karatu a wata “Hauza Ilmiyyah” da ke Æ™asar Iran, daga shekarar 1982 zuwa 1984. Malama Zeenatu baiwar Allah ce ma’abuciyar hidima ga addini da tsayuwa akan hadafi, mace ce haziÆ™a mai tsananin riÆ™o ga karantarwar addini da fikirar Harka Islamiyya. An shaideta da yawan ibada da kishin addini da tsananin tausayawa mata.

AURENSA:
Malama Zeenatuddeen Ibraheem ta fara sanin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne a shekarar 1977 lokacin da take karatu a makarantar kwalejin koyon sana’o’i, “Commercial Collage Zaria”, a lokacin Shaikh Zakzaky (H) yana É—alibta a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, kuma kasancewar yana É—aya daga cikin jagororin Æ™ungiyar É—alibai musulmi MSS (wato Officials), kuma yana É—aya daga cikin masu gabatar da jawabai da wa’azozi na Æ™ungiyar, a irin wannan jawabai da yake gabatarwa ne Malama Zeenatu ta san shi.

Amma Shaikh Zakzaky (H) bai san Malama Zeenatu ba sai a shekarar 1979, lokacin da aka je taron “Islamic Vocation Course” (IVC) na Æ™ungiyar MSS a Legos, a nan ne ya fara ganinta, saboda ta zo taron ne daga Zariya, amma ba wata mu’amala da ta shiga tsakaninsu a lokacin. Mu’amala ta fara shiga tsakaninsu ne a birnin Bauchi a wannan shekarar ta 1979, lokacin da aka zo wani taron IVC na musamman, Malama Zeenat ita ce kaÉ—ai mace da ta zo wannan taro daga wata jaha, kasancewar daga taron IVC na Legos aka wuce Bauchi kai tsaye, kuma É—alibai da yawa ba su san da wannan shiri na wucewa Bauchi daga Lagos ba.

Dan haka da Malama Zeenat ta wuce Bauchi daga Legos sai kuÉ—in mota da na guzurinta ya Æ™are a Bauchi, da aka kammala taron, sai ta nemi ganin Shaikh Zakzaky a keÉ“e a matsayinsa na É—an garinsu (Zariya), ta koka masa Æ™arewar kuÉ—inta, ta nemi ya bata aron kuÉ—in mota, in sun koma Zariya za ta biya shi, sai Shaikh ya bata kuÉ—in da zai wadaceta komawa Zariya da cin abinci da sauran buÆ™atu. Bayan sun koma Zariya da ta samu kuÉ—in ta mayar masa sai ya Æ™i karÉ“a, ya ce tun asali kyauta ya bata ba bashi ba, wannan ce mu’amala ta farko da ta shiga tsakaninsu.

Kasancewar Malama Zeenat haziÆ™a ce mai basira da Æ™umaji, sai aka riÆ™a gayyatarta taron keÉ“antattun membobin MSS na musamman waÉ—anda Shaikh Zakzaky (H) yake karatun gina fikira (Ideology) da tarbiyyar addini da su. Wannan ganawa ta keÉ“antattu da ake kira EED ana yin ta ne a duk taron IVC da aka je, kuma Shaikh Zakzaky ya fara gayyatar Malama Zeenatu zuwa wannan taro na EED ne a IVC na Wudil cikin shekarar 1979, sai kuma na Funtuwa (wanda Shaikh É—in ya shelanta Bara’arsa ga tsarin kafirci) duk dai a shekarar 1979/1980.

Bayan tafiya ta yi nisa ne, Shaikh Zakzaky ya bayyanawa Malama Zeenatu cewa yana sonta da aure, wannan ya faru ne a shekarar 1980, to amma sai Malamar ta nuna cewa ba ta fara tunanin yin aure yanzu ba tukunna, sai Malam ya haƙura da batun. Amma bayan wani lokaci mai tsawo, sai ta yi ta ganin isharori ta hanyar mafarki na dacewar aurenta da shi, wannan ya sa ta canza shawara, ta niƙi gari ita da babbar ƙawarta a lokacin (Fatimah Yunus), suka je har Kurkukun Enugu (inda Shaikh ɗin ke tsare a lokacin) a 1981, ta nemi afuwarsa kuma ta nuna amincewarta ga aurensa.

An ɗaura auren Shaikh Zakzaky (H) da Malama Zeenatu ne a watan July na shekarar 1984, wanda ya yi daidai da watan Shauwal 1404 hijira, bayan dawowarta daga karatu na tsawon shekaru biyu a ƙasar Iran.

ZURIYARSA:
Allah Ta’ala ya yi baiwa ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta hanyar azurta shi da zuriya mai albarka, domin ya haifi ‘ya’ya har guda tara (9), bakwai daga ciki maza ne, yayin da biyu kuma mata ne. Sai dai azzaluman hukumomin Nijeriya ba su bar mafi yawan ‘ya’yan nasa sun yi rayuwa mai tsawo a duniya ba, domin sun kashe shida daga cikin ‘ya’yansa maza guda bakwai a cikin shekara É—aya, kenan, a cikin ‘ya’yansa guda 9, yanzu 3 suka rage, mata biyu da namiji É—aya.

  1. MUHAMMAD IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Muhammad shi ne babban É—a wato É—a na farko a wurin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne a shekarar 1985 (a lokacin mahaifinsa yana tsare a kurkuku sakamakon kamun da shugaban Æ™asa na lokacin Janar Buhari ya yi masa). Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya da Æ™asar Ingila, kuma ya je Æ™asar Iran inda ya karanta darasin “Fasahar Gine-gine” da ake kira “Architecture” a babbar Jimi’ar Tehran (wato University of Tehran) da ke birnin Tehran.
  2. Sayyid Muhammad Æ™wararre ne a yaren Turanci, Farisanci da Hausa. Mutum ne mai tsananin shiru da kawaici da rashin son hayaniya, yana da É—abi’ar kauda kai ga abin da bai shafe shi ba, yana da kaifin basira da hangen nesa, kuma mutum ne mai taka tsantsan akan al’umuran rayuwa. Ya yi aure a watan Mayu na shekarar 2016, a lokacin mahaifinsa yana tsare a kurkuku sakamakon kamun da shugaban Æ™asa Muhammadu Buhari ya sake yi masa a 2015.

  3. NUSAIBA IBRAHEEM ZAKZAKY: An haifi Sayyida Nusaiba ne a ranar 21 ga watan Afirilu na shekarar 1987 bayan fitowar Shaikh Zakzaky daga gidan kurkuku, ita ce ‘ya mace ta farko ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), kuma ta biyu a jerin ‘ya’yansa. Ta yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, ta fara karatun Jami’a a Æ™asar Malesiya, daga nan ta wuce Jami’ar Æ™asa da Æ™asa da ke birnin Dubai na haÉ—aÉ—É—iyar daular Larabawa (United Arab Emerate). Sayyida Nusaiba haziÆ™a ce mai basira da hangen nesa, an shaide ta da yawan haÆ™uri da kawaici.

  4. AHMAD IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Ahmad shi ne É—a na uku a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 15 ga watan Oktoba na shekarar 1990. Ya yi karatun Firamare da Sakandare a Nijeriya, daga nan ya tafi jami’ar Kimiyya da fasaha ta “Dhenyang University of Technology” da ke birnin Zhenyang a Æ™asar Chaina, inda yake karanta darasin fasahar sarrafa sinadarai, wato “Chemical Engineering”, yana shekarar Æ™arshe ta kammala karatu a Jami’ar ya yi Shahada.
  5. Sayyid Ahmad ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan Yuli na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra. Ya rayu a duniya ne tsawon shekaru 23 kacal, kuma ya yi shahada sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Ƙudus ta nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Zariya.

    Sayyid Ahmad ne kwamanda na Mu’assasar Abul-Fadal Abbas. HaziÆ™i ne mai kaifin Æ™waÆ™walwa da basira, yana kama da mahaifinsa sosai a yanayin halitta da hazaÆ™ar Æ™waÆ™walwa, da yanayin É—abi’u. Mutum ne mai tsananin son Æ™ananan yara, an shaide shi da jarunta, yawan ibada, da hidima ga addini.

  6. HAMEED IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Hameed shi ne É—a na huÉ—u a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 17 ga watan Janairu na shekarar 1992, ya yi karatun Firamare da Sakandare a Nijeriya, daga nan ya tafi Jami’ar “Zain University of Technology” da ke birnin Xain a Æ™asar Chaina, inda yake karanta darasin Æ™era jirgin sama wato “Aeronautical Engineering”, yana shekarar Æ™arshe ta kammala jami’ar ya yi Shahada.
  7. Sayyid Hameed ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan Yuli na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra, ya rayu a duniya tsawon shekaru 22 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Ƙudus ta nuna goyon baya ga FalasÉ—inawa a birnin Zariya.

    Sayyid Hameed haziÆ™i ne É—an baiwa irin wanÉ—anda ake kira “Genius”. Kafin rasuwarsa an tabbatar da cewa zai iya Æ™era jirgin sama saboda hazaÆ™a. Mutum ne mai tsananin natsuwa da kawaici, ya fi sha’awar rayuwar shiru da kaÉ—aici, yana da Æ™arancin magana, kuma ba ya son hayaniya.

  8. SUHAILA IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyida Suhaila ita ce ‘ya ta Biyar a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), amma ta biyu a ‘ya’ya mata. An haifi Sayyida Suhaila ne ranar 8 ga watan Agusta na shekarar 1993. Ta yi karatun Firamare da Sakandare a Nijeriya, ta fara karatu a Jami’ar “Usman ÆŠan Fodiyo” da ke birnin Sakkwato a Nijeriya, amma daga baya sai ta tafi wata Jami’ar Æ™asa da Æ™asa “International University” da ke Æ™asar Malesiya, inda ta karanta darasin “Halayyar ÆŠan Adam” wato “Sociology”. Sayyida Suhaila haziÆ™a ce mai fasahar magana, an shaideta da kawaici, Æ™wazo, da himma a fagen addini.

  9. MAHMOUD IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Mahmoud shi ne É—a na Shida a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a makarantarsu É—alibai suna kiransa “Gentle Man”, a gida kuma jama’a suna masa laÆ™abi da “Shehu” saboda natsuwarsa da sauÆ™in kansa da riÆ™o da addini. An haifi Sayyid Mahmud ne ranar 20 ga watan March na shekarar 1995. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kafin ya yi Shahada yana aji uku a jami’ar “Al-Mustapha International University” da ke birnin Beirut na Æ™asar Lebanon.
  10. Sayyid Mahmud ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan July na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 19 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Ƙudus ta nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Zariya.

    Sayyid Mahmud mutum ne Æ™wararre a fagen ilimin kwanfuta da sadarwar zamani, haziÆ™i ne mai tawali’u da tsananin riÆ™o da addini, ya fi sha’awar karatun addini fiye da na zamani. An shaide shi da sauÆ™in kai da kyawun hali da kyawawan É—abi’u da yawan ibada. An yi hasashen da ya rayu, da shi zai gaji Shaikh Zakzaky (H) a fagen ilimin addini mai zurfi.

  11. HAMMAD IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Hammad shi ne É—a na Bakwai a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 10 ga watan Disamba na shekarar 1997. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kuma ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa.
  12. Ya yi shahada ne ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da ranar uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 18 kacal.

    Kafin shahadarsa shi ne kwamandan rundunar Æ™ananan yara masu tasowa da ake kira “Kasshafa”. Ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya. HaziÆ™i ne mai kaifin Æ™waÆ™walwa da basira. An shaide shi da yawan ibada, iya mu’amala, da kula da Æ™ananan yara.

  13. ALI HAIDAR IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Aliy-Haidar shi ne É—a na Takwas a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ranar 15 ga watan Satumba na shekarar 1999. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kuma ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa.
  14. Sayyid Ali yana cikin waÉ—anda waÆ™i’ar Ƙudus ta 2014 ta rutsa da su, tare aka kama shi da ‘yan uwansa guda biyu aka tafi da su barikin soji aka yi ta azabtar da su, shi ne kaÉ—ai ya kuÉ“uta da ransa a cikinsu bayan an yi masa harbi da dama tare da dagargaza Æ™afarsa ta hagu, wanda ya jaza dole sai da aka fita da shi waje aka yi masa aiki.

    Sayyid Aliy-Haidar ya yi shahada ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da Litinin uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437 Hijira. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 16 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya. Sayyid Aliy-Haidar haziÆ™i ne mai kaifin Æ™waÆ™walwa da basira. An shaide shi da yawan ibada, son karatu, son wasannin motsa jiki, da sauÆ™in kai a mu’amala.

  15. HUMAID IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Humaid shi ne É—a na Tara kuma É—an auta a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ranar 22 ga watan Yuni na shekarar 2001, kuma ya yi shahada ne ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da Litinin uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437 Hijira. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 14 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya.

Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, sannan ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa. Haziƙi ne mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira, an shaide shi da jarunta da rashin tsoro, ga sakin fuska da girmama na gaba.

A taÆ™aice, wannan ne tsokaci akan rayuwar ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) guda tara, wanda shida daga ciki suka yi shahada, uku ne kacal ke raye, É—aya namiji biyu mata. Muna roÆ™on Allah ya wanzar da zuriyar Shaikh Zakzaky ta cikinsu, Ilahiy Ameen.

FARA DA'AWARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara wa’azi a bainar jama’a ne a wani babban taro da aka yi a makarantar “Provincial Arabic School” da ke unguwar Kwarbai a cikin birnin Zariya. Wannan taro an yi shi ne a watan Afrilu na shekarar 1972 don kafa Æ™ungiyar samarin Musulmi, kuma ya haÉ—a manyan mutane ciki har da sarakunan gargajiya. Wannan shi ne wa’azi na farko da Shaikh Zakzaky ya fara yi a bainar jama’a, a lokacin yana da shekaru 19 kacal a duniya.

To, amma Da’awa ta fikirar Harka Islamiyyah, wato kiran mutane zuwa ga bin koyarwar addini da Æ™auracewa tsarin jahiliyya, ya fara shi ne a shekarar 1977, wato tun bai fi shekara É—aya a Jami’ar ABU ba, sai dai a lokacin yana Da’awa ta sirri ne ba tare da shelanta manufarsa a fili ba (Da’awa Sirriyya). Ya shafe shekaru uku a wannan mataki na Da’awa ta sirri (1977-1979), sa’annan daga baya ya shelanta manufar Da’awarsa a fili a farkon shekarar 1980 a Funtuwa.

Shaikh Zakzaky (H) ya shelanta Da’awarsa da manufarta a fili ne cikin watan Jimada-Ula na shekarar 1400 Hijira, wanda ya yi daidai da watan Yuli na shekarar 1980. Ya shelanta wannan Da’awa ne a wani babban taro na Æ™ungiyar É—alibai musulmi ta Æ™asa “Muslim Students Society” (MSS) a garin Funtua. A jawabin ya shelanta miÆ™a wila’arsa ga Allah da Manzo (S), tare da Bara’a ga duk tsarin da ya saÉ“awa nasu, ya kuma shelanta Æ™yamarsa ga zalunci da azzalumai. Wannan bayyana Da’awa da ya yi ita ake kira “Shelar Funtuwa” wato “Funtua Declaration” a turance.

Bayan shelanta Da’awarsa a taron É—alibai na Funtuwa, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi wa’azinsa na farko ga al’umma ne a wani gangamin wa’azi da aka yi a masallacin Kwarbai dake Zariya a cikin watan Rajab na shekarar 1400 Hijira (1980), wanda shi ne wa’azi na farko É—auke da fikirar Harka Islamiyya da Sheikh Zakzaky (H) ya gabatar wa mutanen gari.

Bayan shelanta wannan Æ™ira nasa ya fuskanci tsangwama mai tarin yawa ta fuskoki da É“angarori da dama, kama daga azabtarwa daga É“angaren hukuma, da kuma matsin lamba daga dangi da makusantansa. A wani jawabinsa yana cewa; “Wani ma ya ce min “ba za ka koma Jami’a ka yi karatu ba!” (sai) na ce masa; to ai wannan aikin da kake so na yi akwai masu yi, amma wannan (Da’awa) da nake yi ba mai yi! Saboda haka gara wannan shi ma a tsaya a yi shi” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 18).

DALILIN FARA DA'AWARSA:
Kowa zai so sanin yaya aka yi Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) ya fara wannan Da’awa tasa, wato meye dalili, ko ya aka yi tunanin fara yin Da’awar ya zo masa?

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sha amsa wannan tambaya ga ‘yan jaridu, yakan ce, shi a farko bai taÉ“a tunanin zai zama mai Da’awa ko ya zama malamin addini ba, tunaninsa shi ne in ya gama karatunsa na boko zai zama ma’aikacin gwamnati ne ko malamin jami’a, domin rayuwar ma’aikatan gwamnati da ta malaman jami’a tana burge shi, rayuwa ce ta natsuwa wacce ba hayaniya a cikinta, kuma shi yana sha’awar rayuwa ta kaÉ—aici da natsuwa, ba ya son a san shi ko ya zama wani fitaccen mutum, domin ba ya son hayaniya da É—awainiyoyi da yawa.

To, ya aka yi tunanin Shaikh Zakzaky (H) ya canza daga zama ma’aikacin gwamnati ya koma malamin addini mai Da’awa da gwagwarmaya? Shaikh Zakzaky ya amsa tambayar kamar haka; “Ina iya cewa (zama mai Da’awa da na yi) Æ™addara ce ta Ubangiji da kuma ayyukan waÉ—anda suke ganin za su ga bayana, su lalata ni, su hana ni magana….. Domin lokacin da na shiga jami’a, akwai Æ™alubale da yawa da suke fuskantar Musulunci, akwai masu aÆ™idar gurguzu a wancan lokacin, (yanzu babu su ya’alla a harabobin jami’a ne ko a ko’ina), a wancan lokacin suna caccakar duk wani abu da ya shafi Musulunci da shi kansa addini gaba É—aya.

“To, sakamakon na taso da ilimin addinin musulunci, na san suna sukar Musulunci ne kan abin da bai da laifi, suna da aÆ™idar cewa addini kamar Æ™waya ce mai bugarwa ga mutane, kuma da shi ake fakewa ana zaluntar jama’a, suna kawo misali da sarakunan da suke da mata barkatai da saÉ—akoki, kamar wannan kawai Musulunci ya Æ™unsa, sai muka ga bai kamata mu yi shiru kan irin wannan zarge-zarge ba, dan haka muka fara kare addini, ta haka wannan Da’awa ta fara, wato kare addini, kuma a lokaci guda da koyar da mutane haÆ™iÆ™anin manufofin addinin.

“(Domin) mun gano akwai ‘ya’yan musulmi da ba su san mene ne addinin Musulunci ba, wanda masu wannan farfaganda za su iya yaudararsu da waÉ—annan aÆ™idu, hasali ma da dama ko mafi rinjayen (masu aÆ™idar Gurguzun) ‘ya’yan musulmi ne suka dawo suna zargin Musulunci da zaluntar É—an adam, alhali a É—aukacin tarihin É—an adam ba wata aÆ™ida ko tunanin da ya tseratar da É—an adam kamar Musulunci.

“Wani É“angare da suka fi kwarmato akai shi ne batun mata, sun zargi Musulunci da tauye mata, amma bisa É—an ilimin da muke da shi, mun san wannan ba gaskiya bane, duk da cewa abin da waÉ—ansu musulmi suke yi ga mata za a ga kamar haka (musulunci yake), amma wannan ba yana nufin Musulunci ne ya koyar da hakan ba. To, zan iya cewa da haka muka fara (wannan Da’awa) a jami’a, kuma ga alama (abin da muke yin ba ya yi musu daÉ—i), ba su son wannan ci gaba da aka samu, don haka suka fara musguna mana tun muna É—alibta, ta kai ga an kama mu an tsare…

“Kuma ina iya cewa wannan (Da’awa É—in) Æ™addara ce daga Allah, idan muka karanta tarihin Annabi Musa (AS), za mu ga yana Æ™oÆ™arin kare É—an Æ™abilarsa ne (ta kai ga) ya banke ma’aikacin tsaro na Fir’auna ya mutu. Wannan ya tilastawa Annabi Musa (AS) yin hijira, kuma akan hanyarsa ta dawowa ne Allah ya yi masa wahayi da Annabta, wannan Æ™addara ce ta Ubangiji cewa hakan zai faru. A nawa gefen ma ina iya cewa Æ™addara ce ta Ubangiji cewa hakan za ta faru, amma ban taÉ“a tunanin faruwar hakan ba, ban taÉ“a tunanin zan zama malamin addinin Musulunci ba, abin da kawai na yi tsammani shi ne ko dai in zama ma’aikacin gwamnati, ko malamin jami’a, sai na tsinci kaina a abin da nake kai a yanzu”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 02 zuwa 03).

Bayan Shaikh Zakzaky (H) ya soma gwagwarmaya da masu aÆ™idar Gurguzu da ke sukar fikirar addini, tare da tuhumar musulunci da kushe shi kan abubuwa da dama, wanda kuma cikin Æ™anÆ™anin lokaci suna ta gurÉ“ata aÆ™idun ‘ya’yan musulmi ta hanyar falsafa da hikimomi irin nasu, sai ya zamo in Shaikh Zakzaky (H) ya É—auki AlÆ™ur’ani yana karantawa sai ya ji kamar da shi ake magana, kamar Allah Ta’ala yana umartarsa ne da ya tashi ya kare addini ta hanyar karantar da mutane haÆ™iÆ™anin addini da nuna musu hanyar shiriya.

A wata hira da “Mujallar Gwagwarmaya Shaikh Zakzaky (H) yana cewa; “A lokacin in na karanci AlÆ™ur’ani sai in riÆ™a fahimtarsa ta wata mahanga da ada can ni ban gane ba. Ba zan manta ba, a lokacin har nakan riÆ™a kallon aya sai ina ganin kamar a lokacin aka sauÆ™ar da ita… wato sai Allah sanya mini fahimta, in na karanta (aya) sai in ga kamar ana magana da ni ne!” (Mujallar Gwagwarmaya, fitowa ta 3, shafi na 09).

Kenan, idan mun lura da waÉ—annan bayanai, za mu ga cewa abubuwa biyu ne suka zamo asasin wannan Da’awa ta Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), Æ™oÆ™arin kare addinin Musulunci da fikirarsa, don ceto al’ummar musulmi daga gurÉ“acewar aÆ™ida, da kuma Æ™addarawar Allah Ta’ala wacce ya riga ya zartar, wannan su ne tushe ko mu ce asalin abin da ya sa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara wannan Æ™ira na Harka Islamiyyah a Nijeriya.

MANUFAR DA'AWARSA:
Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wani yunÆ™uri ne na sauÆ™e haƙƙin Allah Ta’ala, ta hanyar biyayya ga umarninsa da hanuwa ga hane-hanensa, da kuma Æ™oÆ™arin kawo gyara a cikin al’umma don a gudu tare a tsira tare a gobe Æ™iyama.

Al’umma ta yi nisa cikin É—imuwa da rashin sanin haƙƙoÆ™in Allah a kanta, an ajiye umarnin Allah a gefe ana ta rayuwa cikin son zuciya da makanta, wannan ya jaza É—imbin matsaloli a tafarkin rayuwar al’umma, kama daga munanan É—abi’u da halaye, Æ™eta da fin Æ™arfi, zalunci da danniya, jahilci da makanta, rashin sanin addini da rashin sanin alÆ™ibla, da kuma uwa uba fuskantar mummunar makoma a gobe Æ™iyama.

Wannan ya sa Shaikh Zakzaky (H) ya tashi don kiran mutane zuwa ga addini wanda a cikinsa ne kawai mafitarsu ta ke, a cikinsa ne kawai al’umma za su samu duk abin da suke nema na kwanciyar hankali, yalwar arziÆ™i, tarbiyya da kuma kyakkyawar makoma a gobe Æ™iyama. Dan haka manufar Da’awar Shaikh Zakzaky (H) ita ce É—ora mutane akan koyarwar addinin musulunci da kyautata hali da É—abi’unsu.

A jumlace kuma a dunÆ™ule, manufar Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne kawo gyara don kyautata rayuwar al’umma, da kuma neman uzuri da tsira gaba ga Allah a ranar alÆ™iyama.

Post a Comment

0 Comments