Ahmad Ibrahim

Ahmad Ibrahim Zakzaky (H)

AHMAD IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Ahmad shi ne É—a na uku a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 15 ga watan Oktoba na shekarar 1990. Ya yi karatun Firamare da Sakandare a Nijeriya, daga nan ya tafi jami’ar Kimiyya da Fasaha ta “Dhenyang University of Technology” da ke birnin Zhenyang a Æ™asar Chaina, inda yake karanta darasin fasahar sarrafa sinadarai, wato “Chemical Engineering”, yana shekarar Æ™arshe ta kammala karatu a Jami’ar ya yi Shahada.

Sayyid Ahmad ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan Yuli na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra. Ya rayu a duniya ne tsawon shekaru 23 kacal, kuma ya yi shahada sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Ƙudus ta nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Zariya.

Sayyid Ahmad ne kwamanda na Mu’assasar Abul-Fadal Abbas. HaziÆ™i ne mai kaifin Æ™waÆ™walwa da basira, yana kama da mahaifinsa sosai a yanayin halitta da hazaÆ™ar Æ™waÆ™walwa, da yanayin É—abi’u. Mutum ne mai tsananin son Æ™ananan yara, an shaide shi da jarunta, yawan ibada, da hidima ga addini.

Post a Comment

0 Comments