TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM ALIYU BN MUSA (AS)
SUNA DA NASABARSA (AS):
Sunansa shi ne Aliyu
bn Musa bn Ja’afar bn Muhammad bn Aliyu bn Husain bn Ali bn Abi Talib (AS).
MAHAIFIYARSA (AS):
Wata kuyanga ce da ake kiranta Najma
, wasu kuma suna kiranta da wani sunan.
ALKUNYARSA (AS):
Abul Hasan, Abu Ali da sauransu.
LAƘABINSA (AS):
Al-Ridha, Al-Sabir, Al-Radhi, Al-Wafi, Al-Fadhil da sauransu.
An haife shi ne a ranar 11 ga watan Zil’Ƙa’ada shekara ta 148 bayan hijira, akwai kuma wasu maganganu na daban kan lokacin haihuwar nasa (AS).
WAJEN HAIHUWARSA (AS):
Birnin Madina.
- Kuyangar da ake kiranta da
Sukaina al-Marsiyya
, wasu kuma suna kiranta daAl-Khaizaran
. - Umm Habib bint Ma’amun.
- Imam Muhammad al-Jawad (AS).
- Al-Ƙani'i
- Ja’afar.
- Ibrahim.
- Al-Hasan.
RUBUTUN HATIMINSA (AS):Ma Sha’Allah La Ƙuwata illa billah
.
SHEKARUNSA (AS):
Shekaru 55.
SHEKARUN IMAMANCINSA (AS):
Shekaru 20, wasu kuma suna ganin saɓanin hakan.
- Harun al-Rashid.
- Al-Amin.
- Al-Ma’amun.
LOKACIN SHAHADARSA (AS):
Ƙarshen watan Safar, shekara ta 203, wasu kuma suna ganin saɓanin hakan.
WAJEN SHAHADARSA (AS):
Tus, a Khorasan - Iran.
DALILIN SHAHADARSA (AS):
Ya yi shahada ne sakamakon guban da aka sanya masa lokacin mulkin halifan Abbasiyawa Ma’amun.
ƘABARINSA (AS):
Khorasan (Masshad) – Iran.
0 Comments