Imam Muhammad Al-Bakir (A.S)

Imam Muhammad Al-Bakir (AS)

TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM MUHAMMAD BN ALIYU (AS)

SUNA DA NASABARSA (AS):
Sunansa shi ne Muhammad bn Aliyu bn Husain bn Ali bn Abi Talib (AS).

MAHAIFIYARSA (AS):
Ita ce Fatima bint Imam Hasan (AS).

ALKUNYARSA (AS):
Abu Ja’afar da sauransu.

LAƘABINSA (AS):
Al-Baƙir, Baƙir al-Ilm, AlShakir, Al-Hadi da sauransu.

TARIHIN HAIHUWARSA (AS):

An haife shi ne a ranar 1 ga watan Rajab shekara ta 57 bayan hijira, wasu kuma sun ce a ranar 3 ga watan Safari na wannan shekarar, wasu kuma suna ganin saɓanin hakan.

WAJEN HAIHUWARSA (AS):
Birnin Madina.

MATANSA (AS):
  1. Umm Farwah bint al-Ƙasim.
  2. Umm Hakim bint Usayyid al-Thakafiyya.
  3. da 4 Kuyangi ne.
‘YA’YANSA (AS):
  • Imam SadiÆ™ (AS).
  • Abdullah.
  • Ibrahim.
  • Abdullah.
  • Aliyu.
  • Zainab.
  • Umm Salama.

RUBUTUN HATIMINSA (AS):
Al-Izzatu lillahi, wasu kuma sun ce wani abu ne na daban.

SHEKARUNSA (AS):
Shekaru 57.

SHEKARUN IMAMANCINSA (AS):
Shekaru 19.

SARAKUNAN ZAMANINSA (AS):
  1. Al-Walid bn Abdul Malik.
  2. Sulaiman bn Abdul Malik.
  3. Umar bn Abdul’Aziz.
  4. Yazid bn Abdul Malik.
  5. Hisham bn Abdul Malik.

LOKACIN SHAHADARSA (AS):
7 ga watan Zil Hajj shekara ta 114 hijiriyya.

WAJEN SHAHADARSA (AS):
Birnin Madina.

DALILIN SHAHADARSA (AS):
Ya yi shahada ne sakamakon guban da Ibrahim bn Walid bn Yazid ya sanya masa cikin abinci a lokacin mulkin Hisham bn Abdul Malik, halifan Umayyawa.

ƘABARINSA (AS):
MaÆ™abartar Baki’a da ke birnin Madina.

Post a Comment

0 Comments