TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM ALIYU BN HUSAIN (AS)
SUNA DA NASABARSA (AS):
Sunansa shi ne Aliyu
bn Husain bn Ali bn Abi Talib (AS).
MAHAIFIYARSA (AS):
Ita ce Shah Zanan
, wasu kuma sun ce sunanta shi ne Shahrbanu
.
ALKUNYARSA (AS):
Abu Muhammad, Abul Hasan, Abul Ƙasim da sauransu.
LAƘABINSA (AS):
Zainul Abidin, Sayyid al-Abidin, Al-Sajjad, Zu al-Thafanat, Imam al-Muminin, Al-Zahid, al-Amin, Al-Mutahajjid, Al-Zakiy da sauransu.
An haife shi ne a ranar 5 ga watan Sha’aban shekara ta 38 bayan hijira, wasu kuma sun ce a ranar 15 ga Jimada Sani na wannan shekarar, wasu kuma suna ganin saÉ“anin hakan.
WAJEN HAIHUWARSA (AS):
Birnin Madina.
MATANSA (AS):
An ce ya auri mata bakwai: ta farkonsu ita ce Umm Abdullah
bint Hasan (AS).
- Imam Baƙir (AS).
- Hasan
- Husain
- Zaid.
- Husain al-Asghar.
- Abdurrahman.
- Sulaiman.
- Ali.
- Muhammad Al-Asghar.
- Khadijah.
- Fatima.
- Aliyah.
- Umm Kulthum da sauransu.
RUBUTUN HATIMINSA (AS):Wa Ma Taufiki illa billah
, wasu kuma sun ce wani abu ne na daban.
SHEKARUNSA (AS):
Shekaru 57.
SHEKARUN IMAMANCINSA (AS):
Shekaru 35.
- Yazid bn Mu’awiyya.
- Mu’awiyya bn Yazid.
- Marwan bn Hakam.
- Abdul Malik bn Marwan.
- Al-Walid bn Abdul Malik.
LOKACIN SHAHADARSA (AS):
Akwai saɓani dangane da lokacin shahadarsa (AS), wasu sun ce ranar 12 ga watan Muharram, wasu kuma sun ce 18 ga Muharram ɗin, wasu kuma suka ce 25 gare shi shekara ta 94 ko 95 hijiriyya.
WAJEN SHAHADARSA (AS):
Birnin Madina.
DALILIN SHAHADARSA (AS):
Ya yi shahada ne sakamakon guban da aka sanya masa cikin abinci a lokacin mulkin Walid bn Abdul Malik, halifan Umayyawa.
0 Comments