Imam Husain (A.S)

Imam Husain (AS)

TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM HUSAIN BN ALI (AS)

SUNA DA NASABARSA (AS):
Sunansa shi ne Al-Husain bn Ali bn Abi Talib bn Abdul Mutallib (AS).

MAHAIFIYARSA (AS):
Ita ce Fatima al-Zahra ‘yar Manzon Allah (SAWA).

ALKUNYARSA (AS):
Abu Abdillah.

LAƘABINSA (AS):
Al-Rashid, Al-Sibt, Al-Tayyid, Al-Sayyid, Al-Zakiy, Al-Mubarak, Al-Tabi’ limardhatillah, Al-Dalil ala Zatillah, Sayyid Shabab Ahl al-Janna, Sayyid al-Shuhada’, Abul A’imma da sauransu.

TARIHIN HAIHUWARSA (AS):

An haifi Imam Husain (AS) ne a ranar 3 ga watan Sha’aban shekara ta 4 bayan hijira, wasu kuma sun ce 5 ga Sha’aban É—in, wasu kuma suna ganin saÉ“anin hakan.

WAJEN HAIHUWARSA (AS):
Birnin Madina.

YAƘUƘUWANSA (AS):
Ya kasance tare da mahaifinsa Ali (AS) a yaƙuƙuwan Jamal, Siffin da Nahrawan.
Sannan kuma ya kasance babban kwamandan dakarun imani wajen fuskantar dakarun kafirci a Karbala.

MATANSA (AS):
  1. Shah Zanan bint Kisra.
  2. Laili bint Murra Al-Thakafiyya.
  3. Umm Ja’afar Al-Kadha’iyya.
  4. Al-Rubab bint Imra’il Kais.
  5. Ummu Ishak bint Talha al-Tamimi.
‘YA’YANSA (AS):
  • Aliyu al-Akbar.
  • Aliyu al-Asghar.
  • Ja’afar.
  • Abdullah al-Radhi.
  • Sakina.
  • Fatima.

RUBUTUN HATIMINSA (AS):
Likulli Ajalin Kitab, wasu kuma sun ce wani abu ne na daban.

SHEKARUNSA (AS):
Shekaru 57.

SHEKARUN IMAMANCINSA (AS):
Shekaru 11.

SARAKUNAN ZAMANINSA (AS):
  1. Mu’awiyya bn Abi Sufyan.
  2. Yazid bn Mu’awiyya.

LOKACIN SHAHADARSA (AS):
10 ga watan Muharram shekara ta 61 hijiriyya.

WAJEN SHAHADARSA (AS):
Karbala mai tsarki.

DALILIN SHAHADARSA (AS):
Ya yi shahada ne yana mai kare addinin kakansa Ma’aiki (SAWA) a Karbala.

ƘABARINSA (AS):
Karbala mai tsarki.

Post a Comment

0 Comments