TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM ALI BN ABI TALIB (AS)
SUNA DA NASABARSA (AS):
Sunansa shi ne Aliyu
bn Abi Talib bn Abdul Mutallib bn Hashim bn Abdu Manaf.
MAHAIFIYARSA (AS):Fatima
bint Asad bn Hashim bn Abdu Manaf.
ALKUNYARSA (AS):
Abul Hasan, Abul Husain, Abul Sibtain, Abul Raihanatain, Abu Turab da sauransu.
LAƘABINSA (AS):
Amirul Muminin, Sayyid al-Muslimin, Imam al-MuttaÆ™in, Ƙa’id al-Gurral Muhajjalin, Sayyid al-Awsiya’, Sayyid Al-Arab, Al-Murtadha, Ya’asub Al-Din, Haidar, Al-Anza’ Al-Batin, Asadullah da sauransu.
An haife shi ne a ranar 13 ga watan Rajab, shekaru talatin bayan shekarun giwaye, wato bayan shekaru talatin kenan da haihuwar Ma’aiki (SAWA).
WAJEN HAIHUWARSA (AS):
Garin Makka, a cikin É—akin Ka’aba.
YAƘUƘUWANSA (AS):Amirul Muminina
(AS) ya kasance tare da Ma’aiki (SAWA) a yaÆ™uÆ™uwan da ya yi da kafirai in banda yaÆ™in Tabuka lokacin da Manzo (SAWA) ya buÆ™ace shi da ya zauna a Madina don kula da al’amurra.
Yaƙuƙuwan da ya yi da kansa kuwa lokacin halifancinsa (AS) su ne:
- Yaƙin Jamal.
- Yaƙin Siffin.
- Yaƙin Nahrawan.
- Fatima al-Zahra (SA) ‘yar Ma’aiki Muhammad (SAWA).
- Umamah bint Abi Al-Aas.
- Ummul Banin.
- Laili bint Mas’ud.
- Asma’ bint Umais.
- Al-Sahba’ bint Rubai’ah (Umm Habib).
- Khaula bint Ja’afar.
- Umm Sa’ad bint Urwah.
- Mukhba’ah bint Imra’il Kais.
Akwai saÉ“ani tsakanin malaman tarihi kan adadin ‘ya’yansa (AS), sai dai ruwayoyi sun tsaya ne tsakanin 25 da 33. Ga fitattu daga cikinsu:
- Imam Hasan (AS).
- Imam Husain (AS).
- Zainab al-Kubra (SA).
- Zainab al-Sughra.
- Abbas (Abul Fadhl) (AS)
- Muhammad al-Awsat.
- Ja’afar.
- Abdullah.
- Usman.
- Muhammad bn Al-Hanafiyya.
- Yahya.
- Umm Hani.
- Maimuna.
- Jumanah (Umm Ja’afar).
- Nafisa.
RUBUTUN HATIMINSA (AS):Al-Mulk lillah al-Wahid al-Kahhar
, wasu kuma sun ce sabanin hakan.
SHEKARUNSA A DUNIYA (AS):
Shekaru 63 a duniya.
SHEKARUN IMAMANCINSA (AS):
Shekaru 30.
LOKACIN SHAHADARSA (AS):
Imam Ali
(AS) ya yi shahada ne a ranar 21 ga watan Ramalana shekara ta 40 hijiriyya.
DALILIN SHAHADARSA (AS):
Saran da la’anannen Allah Ibn Muljam al-Muradi ya yi masa a kansa da takobi mai guba a lokacin da yake salla a masallacin Kufa.
ƘABARINSA (AS):
Birnin Najaf mai tsarki, a yankin Al-Gari.
0 Comments