TAƘAITACCEN TARIHIN ANNABI MUHAMMAD BN ABDULLAH (SAWA)
SUNA DA NASABARSA (SAWA):
Sunansa Muhammad
bn Abdullahi bn Abdul Mutallib bn Hashim bn Abdu Manaf bn Kusay bn Kilab, nasabarsa tana komawa ne ga Annabi Ibrahim (AS).
MAHAIFIYARSA (SAWA):
Ita ce Amina
bint Wahab bn Abdu Manaf bn Zuhra bn Kilab.
ALKUNYARSA (SAWA):
Abul Ƙasim da Abu Ibrahim
LAƘABINSA (SAWA):
Daga cikin laƙubbansa akwai:
Al-Mustafa, sannan akwai wasu kuma da suka zo cikin AlÆ™ur’ani mai girma da suka haÉ—a da:
Khatam al-Nabiyin, Al-Ummi, Al-Muzammil, Al-Mudaththir, Al-Nadhir, Al-Mubin, Al-Karim, Al-Nur, Al-Ni’ima, Al-Rahma, Al-Abd, Al-Ra’uf, Al-Rahim, Al-Shahid, Al-Mubasshir, Al-Da’iy da sauransu.
An haifi Annabi Muhammad
(SAWA) ne a ranar 17 ga watan Rabi’ul Awwal a shekarar giwaye (571 miladiyya), wannan shi ne abin da yafi shahara tsakanin ‘yan Shi'a, wasu kuma sun ce a ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal a shekarar giwayen.
WAJEN DA AKA HAIFE SHI (SAWA):
Birnin Makka.
LOKACIN DA AKA AIKO SHI (SAWA):
An aiko Manzon Allah
(SAWA) a matsayin Manzo
ne a garin Makka a ranar 27 ga watan Rajab a lokacin yana É—an shekaru 40 a duniya.
KOYARWARSA (SAWA):
Manzon Allah
(SAWA) ya zo ne da saÆ™on daidaituwa tsakanin dukkanin halittu, ‘yan’uwantaka da kuma afuwa ta gaba É—aya ga duk wanda ya shiga Musulunci
, sannan kuma ya zo da cikakkiyar shari’a da dokoki na adalci. Ya karÉ“o wadannan hukumce-hukumce ne daga wajen Ubangiji
Madaukakin Sarki, don ya isar da su zuwa ga dukkanin al’umma.
MU'UJIZARSA (SAWA):
Mafi girman mu’ujizarsa shi ne AlÆ™ur’ani mai girma, amma sauran mu’ujizozin da ya nuna a lokacin isar da saÆ™on sa kuwa suna da yawa da ba za a isar Æ™irga su ba.
DA'AWARSA (SAWA):
Ya kirayi mutane zuwa ga kaÉ—aita Ubangiji
a garin Makka a É“oye na tsawon shekaru uku, sannan a bayyane kuma na tsawon shekaru goma.
HIJIRARSA (SAWA):
Manzon Allah
(SAWA) ya yi hijira ne daga Makka zuwa Madina a farko-farkon watan Rabi’ul Awwal bayan shekaru 13 da aiko shi saboda tsananin cutarwar da mushirikai suka nuna masa da shi da sahabbansa.
YAƘUƘUWANSA (SAWA):
Bayan da Allah
Madaukakin Sarki Ya yi masa umarnin yaƙan kafirai da mushirikai da munafukai, Manzon Allah (SAWA) ya yaƙe su a lokuta daban-daban.
Fitattun yaƙin da ya yi sun haɗa da:
- Yaƙin Badar.
- Yaƙin Uhudu.
- Yaƙin Khandak ko kuma Ahzab.
- Yaƙin Khaibar.
- Yaƙin Hunain.
MATAYENSA (SAWA):
- Khadijah bint Khuwailid, ita ce matarsa ta farko (SAWA).
- Saudatu bint Zam’ah
- A’isha bint Abi bakr
- Ghaziyya bint Dudan (Umm Sharik)
- Hafsat bint Umar
- Ramla bint Abi Sufyan (Umm Habiba)
- Umm Salama bint Abi Umayyah
- Zainab bint Jahshin
- Zainab bint Khuzaimah
- Maimuna bint Al-Harith
- Juwairiya bint Al-Harith
- Safiyya bint Hayyi bn Akhtab.
- Abdullah.
- Al-Ƙasim.
- Ibrahim.
- Fatima al-Zahra (SA). Wasu sun ce akwai kuma:
- Zainab
- Ruƙayya
- Umm Kulthum.
- Al-Harith.
- Al-Zubair.
- Abu Talib.
- Hamza.
- Al-Ghaidak.
- Dharar al-Mukawwim.
- Abu Lahab.
- Al-Abbas.
Daga cikinsu akwai:
- Umaymah.
- Umm Hakimah.
- Barra.
- Atika.
- Safiyya.
- Arwah.
WASIYYANSA (SAWA):
Su ne Imamai Ma’asumai goma sha biyu (AS), su ne:
- Amirul Muminina Ali bn Abi Talib (AS).
- Al-Hasan bn Ali (AS).
- Al-Husain bn Ali (AS).
- Aliyu bn Husain (AS).
- Muhammad bn Ali (AS).
- Ja’afar bn Muhammad (AS).
- Musa bn Ja’afar (AS).
- Aliyu bn Musa (AS).
- Muhammad bn Ali (AS).
- Aliyu bn Muhammad (AS).
- Al-Hasan bn Ali (AS).
- Muhammad bn Hasan Al-Mahdi al-Muntazar (Allah Ya gaggauta bayyanarsa).
- Hussan bn Thabit.
- Abdullah bn Rawaha.
- Ka’ab bn Malik.
- Bilal al-Habashi.
- Ibn Umm Maktum.
- Sa’ad Al-Kard.
RUBUTUN HATIMINSA (SAWA):
Muhammad Rasulullah
.
SHEKARUNSA (SAWA):
Shekaru 63.
LOKACIN ANNABCINSA (SAWA):
Shekaru 23.
LOKACIN RASUWARSA (SAWA):
Manzon Allah
(SAWA) ya rasu ne a ranar 28 ga watan Safar, shekara ta 11 bayan hijira.
WAJEN RASUWARSA (SAWA):
Birnin Madina.
ƘABARINSA (SAWA):
Masallacinsa da ke birnin Madina.
0 Comments