TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM HASAN BN ALIYU (AS)
SUNA DA NASABARSA (AS):
Sunansa shi ne Hasan
bn Aliyu bn Muhammad bn Aliyu bn Musa bn Ja’afar bn Muhammad bn Aliyu bn Husain bn Ali bn Abi Talib (AS).
MAHAIFIYARSA (AS):
Wata kuyanga ce mai suna Sausan
, wasu kuma suna kiranta da wani sunan.
ALKUNYARSA (AS):
Abu Muhammad.
LAƘABINSA (AS):
Al-Askari, Al-Siraj, Al-Khalis, Al-Samit, Al-Taƙiy da sauransu.
An haife shi ne a ranar 8 ga watan Rabi’ul Awwal shekara ta 232 bayan hijira, wasu kuma suna ganin saÉ“anin hakan.
WAJEN HAIHUWARSA (AS):
Birnin Madina.
MATANSA (AS):
Kuyanga ce da ake kiranta Narjees
.
‘YA’YANSA (AS):
ÆŠansa guda ne shi ne kuwa Imam al-Hujja Al-Muntazar, Allah
Ya gaggauta bayyanarsa.
RUBUTUN HATIMINSA (AS):Subhana man lahu maƙalidis samawat wal ardh
.
SHEKARUNSA (AS):
Shekaru 28.
SHEKARUN IMAMANCINSA (AS):
Shekaru 6.
- Al-Mutawakkil.
- Al-Muntasir.
- Al-Musta’in.
- Al-Mu’utaz.
- Al-Muhtadi.
- Al-Mu’utamad.
LOKACIN SHAHADARSA (AS):
8 ga watan Rabi’ul Awwal, shekara ta 260 hijiriyya, wasu kuma suna ganin saÉ“anin hakan.
WAJEN SHAHADARSA (AS):
Samarra’.
DALILIN SHAHADARSA (AS):
Ya yi shahada ne sakamakon guban da aka sanya masa lokacin mulkin halifan Abbasiyyawa Al-Mu’utamad.
ƘABARINSA (AS):
A gidansa (AS) da ke garin Samarra’ na Æ™asar IraÆ™i.
0 Comments