TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM MUHAMMAD BN HASAN (ATF)
SUNA DA NASABARSA (ATF):
Sunansa shi ne Muhammad
bn Hasan bn Aliyu bn Muhammad bn Aliyu bn Musa bn Ja’afar bn Muhammad bn Aliyu bn Husain bn Ali bn Abi Talib (AS).
MAHAIFIYARSA (ATF):
Wata kuyanga ce da ake kira Narjees
, wasu kuma suna kiranta da wani sunan.
ALKUNYARSA (ATF):
Abul Ƙasim.
LAƘABINSA (ATF):
Al-Mahdi, Al-Muntazar, Sahib al-Zaman, Al-Hujja, Al-Ƙa’im, Wali al-Asr, Al-Sahib da sauransu.
An haife shi ne a ranar 15 ga watan Sha’aban shekara ta 255 bayan hijira, lokacin halifan Abbasiyawa Al-Mu’utamad.
WAJEN HAIHUWARSA (ATF):Samarra
’.
SHEKARUNSA (ATF):
Har ya zuwa yanzu yana raye sai dai ya faku daga idanu, zai bayyana a ƙarshen zamani da izinin Allah
, muna roƙonsa Madaukakin Sarki da Ya gaggauta bayyanarsa (AS) don ya cika duniya da adalci bayan ta cika da zalunci.
SHEKARUN IMAMANCINSA (ATF):
Lokacin imamancinsa na da tsawo saboda har ya zuwa yanzu yana raye.
Yana da zaɓaɓɓun jakadu guda huɗu da mutane suke karɓa hukumce-hukumce daga wajensu a lokacin ƙaramar fakuwarsa (AS), su ne:
- Usman bn Sa’id.
- Muhammad bn Usman.
- Husain bn Ruh.
- Aliyu bn Muhammad al-Samri.
Yana da fakuwa kala biyu:
- Ta Farko: Ƙaramar Fakuwa: tsawon shi ne shekaru 69, ta fara ne a shekara ta 260 hijiriyya har zuwa shekara ta 329 hijiriyya.
- Ta Biyu: Babbar Fakuwa: ta fara ne a shekara ta 329 hijiriyya bayan rasuwar jakadansa na ƙarshe.
Ba za mu iya bayyana su duka a nan ba, sai dai za mu taƙaita da ambaton huɗu daga cikinsu:
- Bayyanar Al-Sufyani.
- Kashe al-Hasani.
- Karɓa baƙar tura daga Khorasan.
- Bayyanar Al-Yamani.
0 Comments