Imam Muhammad Al-Jawad (A.S)

Imam Muhammad Al-Jawad (AS)

TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM MUHAMMAD BN ALIYU (AS)

SUNA DA NASABARSA (AS):
Sunansa shi ne Muhammad bn Aliyu bn Musa bn Ja’afar bn Muhammad bn Aliyu bn Husain bn Ali bn Abi Talib (AS).

MAHAIFIYARSA (AS):
Wata kuyanga ce mai suna Sukaina Al-Marsiyya, wasu kuma suna kiranta: Al-Khaizaran da sauransu.

ALKUNYARSA (AS):
Abu Ali, Abu Ja’afar, har ila yau kuma ana kiransa (AS) da: Abu Ja’afar al-Thani don bambanta shi da Imam BaÆ™ir (AS).

LAƘABINSA (AS):
Al-Jawad, Al-Taƙi, Al-Zakiy, Al-Ƙaniy, Al-Murtadha, Al-Muntajab da sauransu.

TARIHIN HAIHUWARSA (AS):

An haife shi ne a ranar 10 ga watan Rajab shekara ta 195 bayan hijira, wasu kuma suna ganin saɓanin hakan.

WAJEN HAIHUWARSA (AS):
Birnin Madina.

MATANSA (AS):
  1. Kuyangar da ake kiranta Sumanah.
  2. Ummul Fadhl bint Ma’amun.
‘YA’YANSA (AS):
  1. Imam Al-Hadi (AS).
  2. Musa.
  3. Fatima.
  4. Umamah.
RUBUTUN HATIMINSA (AS):
Ni’imal Ƙadir Allah.

SHEKARUNSA (AS):
Shekaru 25.

SHEKARUN IMAMANCINSA (AS):
Shekaru 17.

SARAKUNAN ZAMANINSA (AS):
  1. Al-Ma’amun.
  2. Mu’atasim.

LOKACIN SHAHADARSA (AS):
Ƙarshen Zil Ƙa’ada shekara ta 220 hijiriyya.

WAJEN SHAHADARSA (AS):
Birnin Bagadaza.

DALILIN SHAHADARSA (AS):
Ya yi shahada ne sakamakon guban da aka sanya masa lokacin mulkin halifan Abbasiyyawa Al-Mu’utasim.

ƘABARINSA (AS):
Maƙabartar Ƙuraishawa da ke garin Kazimiyya kusa da kakansa Imam Kazim (AS).

Post a Comment

0 Comments