Imam Aliyu Al-Hadi (A.S)

Imam Aliyu Al-Hadi (AS)

TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM ALIYU BN MUHAMMAD (AS)

SUNA DA NASABARSA (AS):
Sunansa shi ne Aliyu bn Muhammad bn Aliyu bn Musa bn Ja’afar bn Muhammad bn Aliyu bn Husain bn Ali bn Abi Talib (AS).

MAHAIFIYARSA (AS):
Wata kuyanga ce mai suna Sumana, wasu kuma suna kiranta da wani sunan.

ALKUNYARSA (AS):
Abul Hasan da Abul Hasan al-Thalith.

LAƘABINSA (AS):
Al-Hadi, Al-Mutawakkil, Al-Fattah, Al-Naƙiy, Al-Murtadha, Al-Najib, Al-Alim da sauransu.

TARIHIN HAIHUWARSA (AS):

An haife shi ne a ranar 15 ga watan Zil Hajj shekara ta 212 bayan hijira, wasu kuma suna ganin saɓanin hakan.

WAJEN HAIHUWARSA (AS):
Ƙauyen Sarya da ke kimanin mil uku daga birnin Madina.

MATANSA (AS):
Kuyanga ce da ake kiranta Sausan, wasu kuma suna kiranta da wani sunan.

‘YA’YANSA (AS):
  1. Imam Hasan al-Askari (AS).
  2. Al-Husain.
  3. Muhammad.
  4. Ja’afar.

RUBUTUN HATIMINSA (AS):
Hifzul Uhudi min AkhlaÆ™ al-Ma’abud.

SHEKARUNSA (AS):
Shekaru 42.

SHEKARUN IMAMANCINSA (AS):
Shekaru 33.

SARAKUNAN ZAMANINSA (AS):
  1. Al-Mu’utasim.
  2. Al-WasiÆ™.
  3. Al-Mutawakkil.

LOKACIN SHAHADARSA (AS):
3 ga watan Rajab, shekara ta 254 hijiriyya.

WAJEN SHAHADARSA (AS):
Samarra’.

DALILIN SHAHADARSA (AS):
Ya yi shahada ne sakamakon guban da aka sanya masa lokacin mulkin halifan Abbasiyyawa Al-Mutawakkil.

KABARINSA (AS):
Samarra’ da ke kasar IraÆ™i.

Post a Comment

0 Comments