TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM MUSA BN JA'AFAR (AS)
SUNA DA NASABARSA (AS):
Sunansa shi ne Musa
bn Ja’afar bn Muhammad bn Aliyu bn Husain bn Ali bn Abi Talib (AS).
MAHAIFIYARSA (AS):
Ita ce Hamida
, wasu kuma suna kiranta da wani suna na daban.
ALKUNYARSA (AS):
Abul Hasan, Abu Ibrahim, Abu Ali, Abu Isma’il da sauransu.
LAƘABINSA (AS):
Al-Kazim, Abdus Salih, Al-Sabir, Al-Amin da sauransu.
An haife shi ne a ranar 7 ga watan Safar shekara ta 128 bayan hijira.
WAJEN HAIHUWARSA (AS):
Abwa, a birnin Madina.
MATANSA (AS):
Dukkansu kuyangi ne.
Yana da kusan ‘ya’yaye 37:
- Imam Ali Al-Ridha (AS).
- Ibrahim.
- Abbas.
- Al-Ƙasim.
- Isma’il.
- Ja’afar.
- Harun.
- Husain.
- Ahmad.
- Muhammad.
- Hamza.
- Abdullah.
- Ishak.
- Abdullah.
- Zaid.
- Hasan.
- Al-Fadhl.
- Sulaiman.
- Fatima al-Kubra.
- Fatima al-Sughra.
- Rukayya.
- Hakima.
- Ummu Abiha.
- Rukayya al-Sughra.
- Kulthum.
- Umm Ja’afar.
- Lubabah.
- Zainab.
- Khadijah.
- Ulayyah.
- Amina.
- Hasana.
- Bariha.
RUBUTUN HATIMINSA (AS):Hasiyallah
, wasu kuma sun ce wani abu ne na daban.
SHEKARUNSA (AS):
Shekaru 55.
SHEKARUN IMAMANCINSA (AS):
Shekaru 35.
- Abu Ja’afar Al-Mansur al-Dawaniki.
- Muhammad Al-Mahdi.
- Musa al-Hadi.
- Harun al-Rashid.
LOKACIN SHAHADARSA (AS):
25 ga Rajab, shekara ta 183, wasu kuma suna ganin saɓanin hakan.
WAJEN SHAHADARSA (AS):
Birnin Bagadaza.
DALILIN SHAHADARSA (AS):
Ya yi shahada ne sakamakon guban da aka sanya masa cikin abinci a lokacin mulkin Haruna Rashid, halifan Abbasiyawa.
ƘABARINSA (AS):
Maƙabartar Ƙuraish da ke Kazimiyya, arewacin birnin Bagadaza.
0 Comments