TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM JA'AFAR BN MUHAMMAD (AS)
SUNA DA NASABARSA (AS):
Sunansa shi ne Ja’afar
bn Muhammad bn Aliyu bn Husain bn Ali bn Abi Talib (AS).
MAHAIFIYARSA (AS):
Ita ce Ummu Farwah
bint Al-Ƙasim bn Muhammad bn Abi Bakr.
ALKUNYARSA (AS):
Abu Abdillah da Abu Isma’il.
LAƘABINSA (AS):
Al-SadiÆ™, Al-Sabir, Al-Fadhil, Al-Tahir, Al-Kamil, Al-Munji da sauransu.
An haife shi ne a ranar 17 ga watan Rabi’ul Awwal shekara ta 83 bayan hijira, wasu kuma suna ganin saÉ“anin hakan.
WAJEN HAIHUWARSA (AS):
Birnin Madina.
MATANSA (AS):Fatima
bint Husain bin Ali bn Husain (AS), sauran matayensa (AS) kuyangi ne.
- Imam Musa (AS).
- Isma’il.
- Abdullah.
- IshaÆ™.
- Muhammad.
- Abbas.
- Ali.
- Ummu Farwah.
- Asma’
- Fatima.
RUBUTUN HATIMINSA (AS):Allahu Waliyi wa Ismati min khalƙihi
, wasu kuma sun ce wani abu ne na daban.
SHEKARUNSA (AS):
Shekaru 65.
SHEKARUN IMAMANCINSA (AS):
Shekaru 34.
Umayyawa daga cikinsu su ne:
- Hisham bn Abdul Malik.
- Ibrahim bn Walid.
- Marwan al-Himar.
- Abul Abbas Al-Saffah.
- Abu Ja’afar Al-Mansur al-DawaniÆ™i.
LOKACIN SHAHADARSA (AS):
25 ga watan Shawwal shekara ta 148 hijiriyya, wasu kuma suna ganin sabanin haka.
WAJEN SHAHADARSA (AS):
Birnin Madina.
DALILIN SHAHADARSA (AS):
Ya yi shahada ne sakamakon guban da aka sanya masa cikin abinci a lokacin mulkin Mansur al-Dawaniƙi, halifan Abbasiyawa.
0 Comments