Babi Na Bakwai

Babi Na Bakwai

BABI NA BAKWAI


BUSHARORIN BAYYANAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

BUSHARA A TARIHIN ÆŠAN ADAM:
Tarihi ya nuna cewa kafin a haifi duk wani mutum na musamman, mai baiwa ta musaman, wanda zai yi wani aiki na musamman a duniya, ko zai wanzu ya shahara, to, akan samu wasu bayin Allah masu hangen nesa da za su yi busharar bayyanarsa, kamar dai yadda aka samu wasu bayin Allah da ke busharar bayyanar Annabawa (AS), da yadda aka samu waliyan da suka yi busharar bayyanar Mujaddadi Shehu Usman É—an Fodiye (RA), kuma aka samu zantuka masu busharar bayyanar Imam Khumain (QS). To, haka nan shi ma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) an samu bayin Allah da suka yi busharori na bayyanarsa da girman sha’aninsa.

Bushara ta farko da ake alaƙanta ta game da bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ita ce wacce ta zo daga Imam Muhammad Baƙir (AS) wacce Imam Jalaluddin Suyuɗy ya ruwaito a cikin littafinsa, wacce kuma wani manazarci ya yi fashin baƙi akanta ya nuna dacewarta da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Bushara ta biyu ita ce Busharar Imam Ja’afar AssadiÆ™ (AS), wacce ta zo cikin hadisinsa mai tsawo, inda ya bayyana mataimakan Imam Mahdi (AF) guda 313, ya ambaci sunaye da wasu daga cikin siffofinsu, daga cikin sunayen akwai Ibraheem Al-Magriby, wanda ake kyautata zaton Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne.

Bushara ta uku wacce waliyin Allah kuma Mujaddadin addini Shaikh Usman bin Fodiye ya yi, wacce a ciki ya bayyana siffofin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekarar haihuwarsa. Shaikh Usman bin Fodiye ya yi wannan bushara ne a wata waÆ™a tasa mai Baiti Ashirin, wacce ya yi ta da harshen Fulatanci, waÆ™ar tana cikin littafin “Bushral-Ahbab” na Shaikh Usman bin Fodiye, wanda littafi ne da aka tattara waÆ™oÆ™in da ya yi ga waliyyan Allah na zamaninsa da wanda za su zo nan gaba.

Wani malami mai suna Shaikh Bayero ibn Muhammadu Sambo Kulwa ya fassara waÆ™oÆ™in littafin “Bushral-Ahbab” daga Fulatanci zuwa Larabci, bayan ya yi naÆ™alinsu daga littafin mahaifinsa Malam Muhammadu Sambo Kulwa (wanda ya rasu a shekara ta 1248 bayan Hijira) mai suna “Kanzul-Aulaad”, shi kuma mahaifin nasa almajirin Shaikh Usman bin Fodiye ne kai tsaye.

Bushara ta huÉ—u ita ce Busharar da waliyiya Nana Asma’u bint Usman bin Fodiye ta yi akan bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Nana Asma’u ta yi busharar bayyanar Shaikh Ibraheem ne a wata waÆ™arta mai Baitoci 40 cikin harshen Fulatanci, kuma an kawo wannan Bushara a cikin kundin waÆ™oÆ™in ta da wasu Turawan Ingila suka tattara wuri É—aya aka maishe su littafi mai suna; “The Collected Works of Nana Asma’u” na Jean Boyd da B.B Mark, wanda kanfanin wallafa na Sam Bookman Publishers da ke birnin Ibadan a Nijeriya suka wallafa a shekarar 1999.

Sannan akwai busharar da wani babban malamin É—ariÆ™a a Zariya ya taÉ“a yi, wanda bawan Allah ne sufi taÆ™iyyi, kafin rasuwarsa ya taÉ“a bayyana cewa “Wasu matasa daga Jami’ar Ahmadu Bello ne za su yi tajdidin addini a wannan Æ™asa”. Wanda a fili Æ™arara za a iya É—anfara wannan bushara ga Shaikh Zakzaky (H) da almajiransa, domin tushen da’awarsa ya samo asali ne daga wannan Jami’a. Bari mu kawo uku daga cikin waÉ—annan Busharori biyar da muka ambata, tare da yin taÆ™aitaccen sharhi a kansu.

BUSHARAR IMAM BAƘIR (AS):
Malam IshaÆ™ Muhammad ÆŠan’adany (malami, manazarci mazaunin birnin Zariya), ya fitar da wani nazarinsa akan ruwayar Imam BaÆ™ir (AS) da Imam Jalaluddin SuyuÉ—y ya ruwaito a fitaccen littafinsa mai suna “ALHAAWY LIL-FATAAWA” juz’i na uku shafi na 99, inda ya ce lallai wannan ruwaya tana Busharar bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne, ga abin da ya rubuta.

Imam SuyuÉ—y ya ruwaito hadisi a littafinsa mai suna “Al-Haawy Lil-Fataawa” cikin zantukan jikan Manzon Allah (S) Imam BaÆ™ir (AS), ya ce; daga Abiy-Ƙubail (daga Imam BaÆ™ir (AS)) ya ce; “Wani jagora zai kasance a AFIRKA, (zai yi jagoranci) na shekaru sha biyu, kuma a bayansa Fitina za ta kasance. Sa’annan wani namiji wankan TarwaÉ—a (launi tsakanin fari da baÆ™i) zai mulketa ya cikata da adalci. Sannan ya tafi zuwa ga Mahdi (AF) ya miÆ™a masa biyayyarsa (Bai’a), kuma ya yi yaÆ™i a Æ™arÆ™ashinsa” (Al-Haawy Lil-Fataawa” Juz’i na 03 shafi na 98-99).

Abubuwan la’akari da lura a wannan ruwaya sune; Mutum biyun da aka yi Busharar zuwansu ‘yan Afirka ne. Na farkon zai yi Mulki na tsawon shekara sha biyu, sai Fitina ta biyo bayansa, sai wani namiji ya zo (a bayansa) ya tabbatar da adalci, kuma shi wannan mutumin zai riski Imam Mahdy (AF) ya miÆ™a masa Bai’a, sa’annan zai yi yaÆ™i a Æ™arÆ™ashinsa.

To, a bisa nazari, za mu ga cewa wannan ruwaya ta Imam BaÆ™ir (AS) kamar tana magana ne akan Shaikh Usman Bin Fodiye (RA) da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin na farko; Shehu Usman bin Fodiye da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) duk ‘yan Afirka ne.

Na Biyu: Shehu Usman da almajiransa sun fara samun Nasara a jihadinsu ne a shekarar 1805 Miladiyya, wanda kafin nan Shehu da almajiransa sun ci karo da wahalhalu sosai, kama daga tsananin yunwa da rashin wurin zama, wanda saboda tsananin yunwa har ta kai ga hijira ta gagari wasu saboda hatta dabbobinsu ba za su iya wannan tafiyar ba, sai da wani Buzu ya taimaka da raƙuminsa wajan kwasarsu zuwa garin Gwandu, inda Shehu da almajiransa suka tare don yin Noma da Kiwo.

Shehu Usman ya samu cikakkiyar nasarar kafa Gwamnati da ikon gudanarwa ne a shekarar 1805, sannan ya yi wafati ne a shekarar 1817. Kenan, in mun lissafa daga 1805 zuwa 1817 za mu samu shekaru 12 ne daidai.

Na uku: Bayan wafatin Shehu ɗan Fodiye fitina ta biyo baya tun daga kan wanda zai gaje shi (kamar yadda tarihi ya tabbatar), wanda hakan ya kawo rarrabuwar kai a almajiran Shehu, har ya yi sanadin raunanar Musulmi, a ƙarshe (babbar fitina, wato) Bature ya zo ya ci su da yaƙi ya rusa ɗan sauran abin da ya ragen.

Na huÉ—u: Bayan tsawon lokaci, sai ga wani namiji a wannan nahiya ta Afirka ya tashi yana Da’awa da fafutukar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma, Æ™iransa ya ratsa Æ™asashe da dama na nahiyar Afirka, wannan kuwa shi ne Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), wanda kuma shi mai cikakkiyar É—a’a ne ga Imam Mahdi (AF), kuma akan biyayya ga Imam É—in yake gina almajiransa.

Na biyar: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai da burin da ya wuce Allah ya sanya shi cikin mataimakan da za su yi yaƙi a ƙarƙashin Imam Mahdi (AF), ba ma shi ba, hatta almajiransa ba su da burin da ya wuce haka. Sannan wasu Busharori na Waliyan Allah sun nuna yana cikin mataimakan Imam Mahdi (AF) 313, kamar yadda ya zo a hadisin Imam Sadiƙ (AS) da zantukan su Shehu Ɗan Fodiyo (RA).

Kenan, in mun duba da kyau za mu ga wancan hadisi na Imam BaÆ™ir (AS) tamkar yana bushara ne na bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin kusan dukkanin abubuwan da hadisin ya ambata sun dace da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Allah ne masani ga haÆ™iÆ™anin al’amura. (IshaÆ™ ÆŠan’adani Al-Rafidhiy, rubutunsa a Wattsapp ranar 04/09/2016).

BUSHARAR IMAM SADIƘ (AS):
Bushara ta biyu wacce ake kyautata zaton Busharar bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ce, ita ce busharar bayyanar wani Ibraheem Al-Maghriby cikin jerin mataimakan Imam Mahdi (AF) da Khalifan Manzon Allah (S) na shida, wato Imam Ja’afar As-SadiÆ™ (AS) ya yi, marubucin littafin “Bayyanar Sharafuddin” ya yi bayani akan wannan Bushara kamar haka;-

“Akwai wata daÉ—aÉ—É—ar Bushara wadda Imam Ja’afar ibn Muhammad AssadiÆ™ (AS) - watau Imami na shida daga zuriyar gidan Manzo mai tsarki (SAWA) - ya yi kan zuwan Malam (H). Wannan busharar kuwa ya yi ta ne tun shekaru É—aruruwa da suka shuÉ—e kafin bayyanar Shehu ÆŠan Fodiyo (RA). Wannan busharar ta fito ne a cikin littafi mai suna “BUSHRAL ISLAM” wanda yake littafi ne da ya yi bayanai a kan bayin Allah waÉ—anda za su bayyana a duniya tun bayan wafatin Manzo mai tsarki (SAWA) har zuwa Æ™arshen duniya.

“Yadda lamarin ya kasance kuwa, wani ne ya zo wajen Imam SadiÆ™ (AS), yana neman sanin ilimi kan bayyanar Imam Mahdi (AS), sai Imam SadiÆ™ (AS) ya fayyace masa bayanai daki-daki har ya kai ga ambata masa sunayen mataimakan Imam Mahdi (AF) su 313, daga ciki ya ambaci sunan Ibraheem Al-Maghriby, watau Ibraheem na yammacin duniya, wanda kai tsaye za a iya cewa yana nufin Malam (Ibraheem Zakzaky) (H) kenan!” (Bayyanar Sharafuddin, Babi na 6, shafi na 40).

Marubucin bai tsawaita bayani akan wannan Bushara ba, sai dai nazari zai iya tabbatar da haka, domin ya zuwa yanzu ba wani Ibraheem da aka yi a Magrib (wato Afirka) da ya fi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) zama kusa da kasancewa cikin mataimakan Imam Mahdi (AF). Domin na farko dai yana riÆ™o ne da tafarkin Imam Mahdi (AF) wato Shi’a Imamiyyah, kuma ayyukan da yake aiwatarwa tamkar shinfiÉ—awa Imam Mahdi (AF) hanya ne, wato yana gwagwarmaya da zalunci da azzalumai, da kuma Æ™oÆ™arin wanzar da adalci a cikin al’umma. Kuma hatta Husainiyyarsa ma wacce ta fi kowace Hussainiyyah girma a nahiyar Afirka, sunan da ya sa mata shi ne “Hussainiyyah BaÆ™iyyatullah”, wato ‘Hussainiyyar Imam Mahdi’ wanda wannan babban alami ne na alaÆ™a da kusancinsa ga Imam Mahdi (AF).

BUSHARAR SHEHU USMAN ÆŠAN FODIYE (RA):
Shaikh Usman bin Fodiye (RA) ya rubuta waƙa Baitoci goma da ke bayani akan wasu manyan waliyyan Allah da suka gabata da kuma waɗanda za su zo nan gaba, to a ciki sai ya ambaci wani waliyi Ibraheem da zai bayyana, wanda ya ce sunansa na baɗini shi ne Sharafuddeen, kuma za a haife shi ne a shekara ta 1370 bayan hijira.

Ga sashen Baitukan nasa:-
(Waliyai) masu zuwa a bayan waÉ—ancan sune; Ibraheem wanda shi ne Sharafuddin da kuma Jamalul-Badry Husamuddini.
Shi Husamun nan da aka ambata shi ne; Wanda aka ba cikamakon Waliyai Kamilai akan muƙaman addini.
A shekara ta 1370 bayan hijira zai bayyana, Wato shi Ibraheem mataimakin Imam Mahdin.

Shaikh Bayero Sambo Kulwa ya yi taÆ™aitaccen sharhi ga waÉ—annan Baituka guda uku, ya ce; “(Ibraheem É—in da zai bayyana), Sharafuddeen shi ne laÆ™abinsa wato sunansa na baÉ—ini, saboda addini zai É—aukaka a lokacinsa…”

“Shi kuma Husamuddin É—in nan da aka ambata, shi ne wanda aka ba muÆ™amin cikamakon waliyai kamilai akan muÆ™aman addini. An tambayi Shehu Usman dangane da wannan Husamuddin É—in, sai ya ce shi ne Imam Mahdi da ake jira… shi shugaban kowa ne a zamaninsa…”

“An tambayi Shehu Usmanu da ya yi Æ™arin bayani akan (abin da zai faru a shekara ta 1370) sai ya ce; “Wannan shekarar ita ce shekarar bayyanar Ibraheem, wanda shi ne mafi girman mataimakan Imam Mahdi da ake jira, amma Allah ne kaÉ—ai ya san lokacin jihadi da yaÆ™i na sojojinsa tare da kafirai, fajirai, fasiÆ™ai da ma’abuta munafunci” (Kitabul-Bushura, shafi na 04).

To, bayan Shehu Usman bin Fodiye ya kammala waƙar, sai aka tambaye shi ƙarin haske game da Ibraheem ɗin nan da ya ambata, shi ne sai ya ƙara rera wasu baitoci goma sabbi, inda ya hallale bayani daki-daki game da Ibraheem ɗin da siffofinsa, ya nuna cewa zai zo da albarkoki masu yawa. Ga yadda baitukan na Shaikh ɗan Fodiye (RA) suke bayan an tambaye shi ƙarin bayani game da Ibraheem Sharfaddeen;

Wani mutum zai bayyana a Æ™asar yamma, Yana kuma da jama’a masu taimakon Mahdi.
Wannan mutumin da zai fito daga yamma manisanciya, Da mabiyansa sune mutanen (Imam) Mahdi.
Duk lokacin da wannan mutumin ya bayyana, Ku da shugabanninku ba za a muku É—a’a ba sai dai ga Mahdi.
Cikin shekarar 1370 ne wannan mutumin zai bayyana, Shi ne kuma babban mataimaki (ga Imam) Mahdi.
Wannan mutumin yana da faffaÉ—an goshi tare da alama, Ka fahimci haka ya kai mai tambaya akan siffofin (mataimakin) Mahdi.
Shi wannan mutumin fatar jikinsa baƙa ce, Gemunsa da ƙirjinsa kuma mayalwata ne (Nasirul Mahdi).
Kuma yana da idanu kamar na Mussa (Mage).
Wannan mutumin zai yawaita ziyarar mafi alherin halitta (SAWA).
Laƙabinsa shi ne Sharafuddeeni, Ibraheem kuma shi ne sunan mataimakin (Imam) Mahdi.

WaÉ—annan Baitoci na Shehu Usman bin Fodiye (RA) sun hallale bayani akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), tare da tabbatar da cewa lallai shi ake nufi a wannan Bushara, domin ba wani Ibraheem da ya tattara waÉ—annan siffofi in ba shi ba.

DACEWAR SHAIKH ZAKZAKY (H) DA BAITOCIN ÆŠAN FODIYE:
Manazarta sun yi nazarin waÉ—annan Baituka na Shehu Usman bin Fodiye (RA), inda suka yi sharhohi masu faÉ—i ta fuskoki da dama. Marubucin littafin “Kitabul-Bushura” da mawallafin “Bayyanar Sharafuddin” da marubucin littafin “Mujaddadin Wannan Ƙarnin” duk sun yi dogayen bayanai da suke tabbatar da cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne kawai ya cika waÉ—annan siffofi da Shehu Usman É—an Fodiye ya zayyana.

  1. NA FARKO: Shehu ya ce za a haifi Ibraheem mataimakin Imam Mahdi (AF) ne a Æ™asar yamma manesanciya. To, idan mutum ya duba hadisan da suka yi maganar bayyanar Imam Mahdi (AF), zai ga cewa duk sun tabbatar da cewa Imam Mahdi (AF) zai bayyana ne a Makka, kuma mataimakansa guda 313 za su je can ne su yi masa Mubaya’a.
  2. To, in aka yi dubi ga Makka a matsayin wurin da Imam Mahdi (AF) zai bayyana, kenan za a iya cewa Æ™asar da mataimakinsa zai fito wato Nijeriya “Ƙasar Yamma Manesanciya”, domin in dai za a auno Nijeriya daga Saudiyya, za a iya Æ™iranta Æ™asar yamma mai nisa.

  3. NA BIYU: An ce Ibraheem É—in zai bayyana a shekarar 1370 bayan Hijira, sai ga shi an haifi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1372 bayan Hijira. Wannan ya dace sosai da zancen Shaikh É—an Fodiye, domin in za a fassara abin da Shehu ya faÉ—i daga Fulatanci ko daga Larabci zuwa Turanci, to cewa za a yi; “Za a haifi Ibraheem Sharafuddeen ne a shekarun saba’inoni wato (Seventes) bayan Hijira” wanda hakan yana nufin ba lallai ne sai an haife shi a 1970 daidai ba, a ko da yaushe aka haife shi daga 1970 zuwa 1979 duk a 70s aka haife shi.
  4. Sannan kuma, in ma mun tafi akan cewa yana nufin za a haife shi ne a 1370 daidai, to dole mu yi la’akari da cewa Shehu Usman bin Fodiye waliyyi ne ba Annabi ba, Ma’asumi ne kawai in ya faÉ—i magana take tabbata cif da cif, su waliyai ana iya samun abin ya gaza da kaÉ—an ko ya Æ™etare da kaÉ—an.

  5. NA UKU: An faÉ—i siffofinsa kamar cewa shi baÆ™in fata ne, kuma mai faÉ—in goshi, mai alama a fuska, mai mayalwacin gemu, mai faÉ—in Æ™irji, kuma mai manyan idanu farare kamar na Mage. WaÉ—annan siffofi suna iya É—aukar ma’anoni biyu, na zahiri da na baÉ—ini, kuma duk biyun sun dace da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Misali; Duk mutumin da ya san Shaikh Zakzaky (H), ko ya ga hotonsa, to zai ga cewa a zahirin halittarsa baƙin fata ne, kuma yana da faffaɗan goshi, kuma yana da alamar Sujjada a fuskarsa, kuma yana da mayalwacin gemu, kuma yana da faɗin ƙirji, kuma yana da manyan idanu farare, da dai sauransu.

Amma a fassara ta baɗini, ba zahirin halitta Shehu Usman bin Fodiye ke nufi da waɗancan siffofin ba, aron kalma ne ya yi a matsayin lamiri. Kenan, da ya ce mai faɗin goshi, yana nufin mai yawan Sujjada na bautar Allah ne. Da ya ce mai alama a fuska, yana nufin mai Haiba ne da kwarjini da hasken fuska. Da ya ce mai yalwar gemu, yana nufin dattijo ne a maganarsa, (wato duk abin da ya faɗa gaskiya ne kuma zai tabbata). Da ya ce mai faɗin ƙirji, yana nufin mai tarin masaniya da zurfin ilimi na fannoni daban-daban ne. Da ya ce mai manyan idanuwa, yana nufin mai ganin shiriya ne a haƙiƙarta, da kuma ɗora mutane akan tafarkin shiriya madaidaici. Duk waɗannan siffofi kuwa sun dace ƙwarai da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ka yi nazari ka gani!

BUSHARAR NANA ASMA’U ‘YAR ÆŠAN FODIYE (R):
Waliyiya Nana Asma’u bint Usman bin Fodiye (R) wacce ta rayu tsakanin 1793 zuwa 1864, ta jaddada Busharar bayyanar mujaddadi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ita kam ma bayan ta ambaci sunan waliyi Ibraheem, da shekarar haihuwarsa, da dangantakarsa da Imam Mahdi (AF), sai ta Æ™arfafa zance akan yadda wa’azinsa zai sha banban da na sauran malamai, da kuma uwa-uba nau’in sabon ilimin da zai bayyanar a cikin al’ummarsa, wanda wannan ke nuna ilimin tafarkin Ahlul-Bait (AS) ne, wanda Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke yaÉ—awa yanzu haka a wannan nahiya.

Ga nassin Busharar Nana Asma’u a waÆ™enta mai Baiti 40, amma mun naÆ™alto daga Baiti na 17 ne zuwa na 30 kamar yadda mawallafin littafin “Bayyanar Sharafuddeen” ya yi, wanda sune ke Æ™unshe da batutuwa akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H);

A cikin shekarar Hijira ta 1400 (1979) ne, Wani Mujaddadin Musulunci zai bayyana.
Usman (ÆŠan Fodiye) ya faÉ—i zuwansa, A lokacin da yake maganar Mahdi.
Zukatan da suka haskaka za su fahimci wannan, WaÉ—anda kuwa ke a cikin duhu ba sa fahimta.
Ana jiran lokutan (bayyanarsa) tun, Shekaru É—ari uku da suka shuÉ—e.
Haƙiƙa an haife shi a shekarar hijirar, Annabi ta 1370 zai bayyana.
Yana da matsayi mai girma, Don haka dole ne a girmama shi.
Littattafansa sune hujjarsa, In kana musu to ka karanta su (ka jiya).
Ganinsa kawai zai iya bayyanar maka, Da ko shi wanene (idan har ka kula).
Kowa (ya kamata) ya so shi, Ya kuma kula da amfanonin da zai zo da su.
Ba ko shakku cewa akwai alamomi, Musulmi ku kula kuma ku fahimta.
Ka da ku kula da ‘yan Æ™ananan abubuwa, Ku kula da hankali kuma ku karanta littattafansa.
Ka da ku ce, “Mu ba mu gaji wannan ba”, Sannan kuma mu (sam) ba mu fahimce shi ba.
Duk yadda lamari ya kasance ku karanta littattafan, Kuma ku sanya zukatanku a cikin aminci.
Ya Allah Ta’ala ka tsare mu daga jahilci, Ka kuma kare mu daga wahalhalun (Duniya).

(The Collected Works of Nana Asma’u. Na Jean Boyd B.B Mark, naÆ™ali daga; “Bayyanar Sharafuddin”, shafi na 48, bisa tasarrufi da tsari).

NAZARIN BUSHARAR NANA ASMA’U (RA):
Idan muka nazarci waÉ—annan Baituka da kyau, za mu ga akwai Æ™wararan shaidu na zahiri da ke tabbatar da cewa Nana Asma’u (RA) ta Æ™ara bayyana wasu siffofi ne na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a wannan Bushara tata, kuma ta fito da abin a fili Æ™arara ta yadda ba za a iya kore dacewar waÉ—annan siffofi ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba.

Misali, bayan ta faÉ—i shekarar da za a haifi Mujaddadin a 1370, tare da tabbatar da cewa zai jaddada addinin Musulunci, da kuma cewa zukatan da Allah ya nufa da haske za su fahimci Da’awar wannan mujaddadi da aka shafe kusan shekaru 300 ana jiran bayyanarsa. Sai ta faÉ—i wasu sabbin abubuwa guda biyu wanda Shehu Usman bai faÉ—e su a tasa Busharar ba.

Abubuwan kuwa su ne; Bayyanar Mujaddadin a shekarar hijira ta 1400 wacce ta yi daidai da shekarar 1979 Miladiyya, sai kuma yawan littattafan Mujaddadin, da kuma sabon ilimin da zai zo da shi, wanda ta ce lallai mutanen zamaninsa su karanta littattafan, kuma kada su ce wa sabon ilimin da ya kawo “Mu ba mu gaji wannan ba”. Sannan ta Æ™arÆ™are da cewa, lallai mutane su yi anfani da hankali wajan nazarin rayuwa da ayyukan wannan Mujaddadi idan ya bayyana, kar su riÆ™a la’akari da ‘yan Æ™ananan abubuwa.

WaÉ—annan muhimman abubuwa guda biyu ba wani Malami a Afirka da ya siffatu da su sama da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin a shekarar 1979 ne Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana, wato a shekarar ne ya shelanta Da’awarsa a wani babban taron Æ™ungiyar É—alibai musulmi da ya gudana a garin Funtuwa, kuma a shekarar ne duniya ta fara jin É—uriyarsa da sunansa a karon farko, sakamakon rikicin “K-GUYS” da ya faru a Jami’ar Ahmadu Bello da ke birnin Zariya, lokacin da Shaikh É—in ya jagoranci matasa musulmi suka wargaza taron Æ™ungiyar mashaya giyar kwakwa da suka saba yi duk shekara. A lokacin manyan jaridu (ciki har da na Æ™asashen waje) da sauran kafafen yaÉ—a labarai duk sun yaÉ—a wannan abu da ya faru, tare da ambatar sunan Shaikh Zakzaky (H) a matsayin wanda ya jagoranci abin.

Sannan da Nana Asma’u ta ce zai kasance mai yawan littattafai, wanda take cewa ya kamata mutane su karanta su, wannan zai iya É—aukar ma’anar yawan wa’azozi, da laccoci, da huÉ—ubobi, da Muhadharorin da Shaikh Zakzaky (H) ke ta yi ne, wanda yanzu kusan shekaru 40 kenan yana yi, amma da yawan mutane ba su ma sauraron jawaban, balle su ji me yake faÉ—a, balle su fahimce shi. Na’am, idan ma tana nufin littattafai ne na zahiri, to akwai É—imbin littattafan Shaikh Zakzaky (H) akan batutuwa daba-daban, wanda laccoci da muhadharorinsa ne aka maishe su zuwa littafi.

Abu na uku shi ne nau’in sabon ilimin da zai bayyanarwa musulmi a zamaninsa, wanda Nana Asma’u take gargaÉ—in cewa kar mutane su ce su ba su gaji irin wannan ilimin a wajan iyayensu ba. Wannan a zahiri yana nufin ilimin tafarkin Ahlul-Bait (AS) ne, wanda ake Æ™ira Shi’a, domin shi ne nau’in sabon ilimin da Shaikh (H) ya bayyana a wannan nahiya, wanda kuma sashen musulmi ke faÉ—a da shi bisa hujjar cewa su ba su yarda da shi ba don ba akansa suka tarar da iyayensu ba.

Kenan, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne mujaddadin da Shehu Usman bin Fodiye da ‘yarsa Nana Asma’u suka yi Busharar bayyanarsa, domin shi ne kaÉ—ai ya cika sharuÉ—É—a da siffofin da waÉ—annan waliyyan Allah suka zayyana a Busharorinsu, amma idan wani na da ja, sai ya kawo nasa gwanin a É—ora shi akan waÉ—ancan sikelin a gani!

Post a Comment

0 Comments