Babi Na Shida

Babi Na Shida

BABI NA SHIDA


NASARORI DA ƊAUKAKAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

KEƁANTATTUN NASARORINSA:
Baki bai isa ya iya faɗin dukkanin nasarorin da jagoran Harka Islamiyyah a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu a rayuwarsa ba, haka nan, alƙalami ba zai taɓa iya rubuta waɗannan nasarori ba, domin sun fi ƙarfin iyakancewa balle kewayewa da sani, amma tunda tsokaci muke yi akan komai na rayuwar jagoran, wannan ma bari mu yi tsokaci kaɗan akai.

  1. NASARA TA ƊAYA: Nasara ta farko da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu a rayuwarsa ita ce Shiriya! Babu shakka Allah Ta’ala ya so shi ya zaɓe shi ya kuma fifita shi da shiriya a birbishin sauran malamai. A duk tarihin Shaikh Zakzaky (H) bai taɓa yin riƙo da tafarkin ɓata ba, ya fito ne daga tsatso mai daraja, gida na malamta, zuriyya ma’abuciyar addini, da kuma tarbiyya ta gari. Duk wata nasara da ɗan adam ke samu a rayuwa a bayan shiriyar Ubangiji take.

  2. NASARA TA BIYU: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi nasarar canza rayuwar ɗimbin mutane daga ɓata zuwa shiriya, daga kuskure zuwa ga daidai, ya ‘yanto tunanin mutane daga ɗimuwa zuwa tunani mai kyau, ya raya zukatan da suka mutu, ya farfaɗo da waɗanda suka suma.
  3. Ta sanadin Da’awarsa da dama daga masu aƙidar kwaminisanci sun canza zuwa aƙidun Musulunci, masu kwana barci sun koyi raya dare da Tahajjud, masu yini cin abinci sun koyi azumomin nafilfili, masu mugayen ɗabi’u sun canza zuwa kyawawa, masu rowa sun koyi kyauta, masu son kai sun koyi Iythari, mata masu tabarruji sun koyi suturtuwa da Hijabi, mazajen da ke wulaƙanta mata sun koyi mutuntasu, matsorata sun zama jarumai, jahilan addini sun zama malamai, ‘yan Malikiyya sun zama ‘yan Ja’afariyyah, nasarar Shaikh Zakzaky (H) wajan sauya al’umma ba ta ƙidayuwa!

  4. NASARA TA UKU: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi nasarar canza Miliyoyin mutane daga aƙidar Sunnanci zuwa na Shi’anci, wanda tarihi bai taɓa ganin irinsa ba. Domin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne kawai mutum ɗaya tilo da aka yi ƙiyasin ya yi nasarar canza sama da mutum miliyan Ashirin da Biyar (zuwa yanzu a nahiyar Afirka) daga aƙidar Ahlis-Sunnah zuwa tafarkin Ahlul-Bait (AS). Wannan irin nasara tarihin ɗan adam bai taɓa ganin irinta ba tun bayan bayyanar Shi’anci a bayan ƙasa.

Batun nasarorin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya cimma a rayuwarsa abu ne da bai da iyaka, dan haka za mu taƙaitu da wannan a matsayin misali.

NASARORINSA GA AL’UMMAH:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya cimma ɗimbin nasarori ta fuskoki da dama na kawo sauyi a al’ummar da yake rayuwa a cikinta, mafi yawan nasarorin Shaikh Zakzaky (H) nasarori ne na baɗini, nasarori ne na raya zukata da canza tunane-tunanen al’umma da wasu I’itiƙadodinsu iri-iri zuwa sahihan tunanuka ta fuskar addini.

Amma tattare da haka, akwai ɗimbin nasarori na kawo sauyi a zahirin rayuwar al’umma da ido zai iya shaidawa ta fuskar addini, al’ada da “Social Issues”, wanda Shaikh ɗin ya samar ga al’ummar da yake rayuwa a cikinta, ga wasu kaɗan daga ciki.

SANYA HIJABI: Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ce ta zo da sanya Hijabi ga mata musulmi a Nijeriya, domin kafin Da’awarsa, ba wanda ya san mata da sanya Hijabi a Nijeriya. Tun bayan Jihadin Shehu Ɗan Fodiye (RA) mata suka watsar da sanya Hijabi. Duk wanda ya wanzu kafin bayyanar Shaikh Zakzaky (H) shaida ne cewa bai ga sanya Hijabi a gidansu ba. Mata sun fara suturtuwa da kammalallen Hijabi ne sakamakon Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

MATA A ADDINI: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara shigo da mata fagen addini a wannan nahiya. A baya a wannan al’umma tamu ba a san yin hidimar addini da mata ba, abin da kawai aka sani shi ne fitar tsofaffin mata tuguf-tuguf zuwa masallacin juma’a da na Idi. Amma sakamakon Da’awar Shaikh Zakzaky (H) yanzu duk wata hidima ta addini da mata ake yi, kama daga wa’azozi, tarukan ƙarawa juna ilimi, muzaharori, I’itikafi da duk wata hidima ta addini. Sannan Da’awarsa ce ta fara ba matan aure ‘yancin ci gaba da karatun addini daga gidajen aurensu, shi ya fara samar da makarantar mata kafin Wahabiyanci ya mamaye fagen daga baya.

MUZAHARA: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya koyawa al’ummar musulmin wannan nahiya yin Muzahara ta fuskar addini. A baya ba a san yin Muzahara don nuna farin ciki, ko tallata wani abu na addini, ko dan nuna rashin yarda da rashin amincewa kan wani abu da ya shafi cutar da Musulmi ko Musulunci ba. Shaikh Zakzaky (H) ne ya fara yin Muzahara da sunan addini a tarihin Nijeriya, yanzu ta kai ga kusan duk ƙungiyoyin addini suna yin Muzahara ko gangami dan nuna farin ciki (kamar Muzaharar Maulidi), ko dan nuna rashin amincewa da tozarta addini, ko dan bayyana wata manufa tasu.

I’ITIKAFI: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara yin I’itikafi a Masallaci a watan Ramadan a tarihin Nijeriya. Tun Shaikh yana matashi yake shiga I’itikafi shi kaɗai a masallaci. Kafin ya aikata I’itikafi a aikce ba a san I’itikafi a zahiri ba, an dai san bayanin I’itikafi a babuka na littattafan Fiƙihu. Dan haka, duk wanda yake I’itikafi a Nijeriya ya kwaikwaya ne daga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa. Wannan wani abu ne sallamamme da ba wanda ya jahilce shi sai mai ƙarancin masaniya da rashin lura da al’amura.

KARE ANNABI (S): Kafin bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), al’ummar wannan nahiya ba ta san hanyar da ya kamata a bi wajan kare martabar Manzon Allah (S) ba. Ko da wani ya ci zarafin Annabi (S) musulmi sukan ji takaici ne kawai a ransu, amma ba sa iya yin wani kataɓus na nuna rashin amincewa da hakan. Hatta a farkon lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara kare martabar Annabi (S) ta hanyar nuna rashin amincewa da zagi ko cin zarafinsa, sai da ya fuskanci tsattsauran martani daga waɗanda ake kallonsu a matsayin malamai da jagororin addini.

A nahiyar Afirka ta yamma baki ɗaya, Shaikh Zakzaky (H) ne ya koya wa musulmi yadda ake kare martabar Annabi (S) ta hanyar mayar da martani, rubuce-rubuce, da Muzaharorin Allah wadai na nuna rashin amincewa. Ta haka musulmin wannan nahiya suka koyi kare martabar Annabi (S) da martabar addini idan an taɓa shi.

HAƊIN KAI: Kusan kowa shaida ne cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi ta fafutukar wayar da kan al’ummar Nijeriya wajan ganin sun fahimci juna tare da sanin tushen matsalarsu maimakon gaba da faɗace-faɗace da juna. Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta fara yaɗuwa ne a daidai lokacin da Wahabiyanci ke ganiyar mamaya da yaɗa munanan aƙidunsa na kafirta musulmi da dasa gaba da ƙiyayya a junansu.

Shaikh Zakzaky (H) ya yi ta fafutukar kawar da gaba a tsakanin musulmi da kuma hana faɗace-faɗacen ƙabilanci da na addini da ya addabi al’ummarmu. Bayan tsawon shekaru ne Shaikh (H) ya yi nasarar daƙile habaƙar gaba tsakanin Izala da Ɗarika, da kuma kashe-kashen ƙabilanci tsakanin Musulmi da Kirista. Ta kai ga Shaikh (H) ya samar da “Makon Haɗin kan Musulmi” wanda ake haɗa malaman musulunci na ƙungiyoyi daban-daban su yi jawabai. Da kuma bikin “Sallah Feast” wanda ake haɗa shugabannin Kirista da na musulmi waje ɗaya su tattauna don samun kusanci da fahimtar juna. Ta haka Shaikh (H) ya yi nasarar kashe kaifin hargitsin Ƙabilanci da na Addini da Siyasa da ma rage gaba a tsakanin al’umma.

DOGARO DA KAI: Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta koyawa ƙungiyoyin addini dogaro da kai wajan ƙoƙarin samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukansu da kansu. Domin a baya ƙungiyoyin addini sun dogara ne kacokam ga tallafin gwamnati da gudunmawar gwamnatoci da ƙungiyoyi na ƙasashen waje wajan tafiyar da al’amuransu, sam ba su iya yin abu da kansu ba, komai yi musu ake yi, a gina musu Masallaci, a saya musu motocin zuwa wa’azi, a ba su kuɗin gudanar da taruka da sauransu. Malamai sun zama Banbaɗawa yaran masu mulki, suna jurewa kowane wulaƙanci daga mahukunta don su ci gaba da samun abin da za su rayu da shi.

Sai Shaikh Zakzaky (H) ya zo da Da’awar da ba ruwanta da kwabon wani, ba ta buƙatar tallafin gwamnatin ƙasa balle na ƙasashen waje, ba ta buƙatar gudunmawar masu kuɗi balle na ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Da’awa ce da ta dogara kacokaf da gudunmawar membobinta kaɗai, duk abin da za a yi za a haɗa taro sisi ne daga membobi a yi shi, ba a neman gudunmawar gwamnati ko ta ƙasashen waje. Wannan ne kuma sirrin da ya ba Da’awar Shaikh Zakzaky cikakken ‘yanci, ba wani mai ikon juya Harka Islamiyya daga waje ko daga cikin gida, domin bai da tasirin da zai iya sawa a yi wani abin da yake so, ko ya hana yin abin da ba ya so.

RAYA MASALLACI: A bisa al’adar al’ummar wannan nahiya, masallaci wurin yin Sallah ne kawai, ba a komai a cikinsa sai Sallah. Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara raya masallaci ta hanyar yin ayyukan addini a cikinsa, a lokacin da yake ɗalibta a Jami’ar Ahmadu Bello ya maido da dukkan tarukan ƙungiyar MSS zuwa masallaci.

A wani jawabinsa yana cewa;- “Ni na tabbatar ba mun gani a aikace a wajan wani bane, mun karanta ne a littafi muka ga cewa a lokacin Annabi (S) masallacin Annabi nan ne cibiyar addini, a nan ne Annabi (S) yake koyarwa, a nan ne yake wa’azi, a nan yake alƙalanci, a nan yake sasanta tsakanin mutane, a nan yake karɓar baƙi daga ƙasashe daban-daban. Wato masallaci a lokacinsa cikakkiyar cibiya ce ta dukkan ayyukan addini, a nan ake yin taro a yi Mashawara a tattauna shawarwari, haka nan ma tattauna dabarun yaƙi da komi da komi duk a masallacin Annabi (S) ake yi a wancan lokacin.

“To, sai muka ce ai a karatu muna karantawa (cewa) komai a zamanin Annabi a masallaci ake yi, amma mu ba mu yin komai a masallaci (sai Sallah). Sai muka ce to harkokin da muke yi na addini mu koma da shi Masallaci. To, sai muka ƙira lacca irin wanda za a gayyato Malami a ba shi wani Maudhu’i ya yi magana akai, sai muka yi a masallaci, to (ai kuwa) sai muka sha surutu, wai yin lacca a masallaci ba a ‘Assambily Hall’ ba! (Saboda su mutane ba su saba da ganin haka ba a wancan lokacin)”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 71-72).

Hatta wa’azin da yanzu ake yi a kusan dukkan masallatai ranar Juma’a kafin zuwan liman, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara assasa shi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kafinsa ba a san da wannan ba, wanda a yau za mu ga cewa masallatai da dama har da na Wahabiyawa suna yi. Amma yanzu saboda yadda abin ya zamo jiki sai a ɗauka tun asali ma haka abin yake, alhali a 70s ne Shaikh Zakzaky ya sunnanta hakan.

RAYA SUNAYE: A bisa al’adar al’ummar wannan nahiya (duk da kasancewarsu musulmi), amma ba su cika ƙiran mutane da cikakkun sunayensu na addini ko na yanka ba, sun fi ƙiransu da sunaye na al’ada. Za ka ji suna ƙiran Ibrahim (Iro), Idris (Idi), Usman (Manu), Abdullahi (Audu), Abubakar (Garba), Dawud (Dauda), Adamu (Ado), Salihu (Salele), Mahmud (Mudi), Muhammad (Mamman), Zakariyya (Ya’u), Sulaiman (Sule) da sauransu.

Haka abin yake ga mata, Ruƙayya (Rakiya), Bilkisu (Balki), Maimunatu (Munari), A’ishatu (A’i), Khadija (Dije), Zainab (Abu), Maryam (Mairo), Hajara (Hajjo), Fatimah (Fatsuma), Lauratu (Laure) da dai sauransu. Haka nan sunan mutum na al’ada yakan shafe asalin sunansa na yanka daga samuwa, sai ka ji sunan mutum Sallau, Mati, Lado, Tanimu, Gambo, Barau, Gagare, Rabe, Makau, Kwasau, Datti, Ɗandunawa da sauransu. In kuma mata ne ka ji Kyallu, Kande, ko ka ji mutane ɗauke da sunayen ranakun da aka haife su irinsu Ɗan Liti, Ɗan Jummai, Asabe, Ladi, Talatu, Larai, da sauransu, ko ka ji mutane ɗauke da sunan lissafi da dai makamantansu.

Amma albarkacin wayewar addini musamman ƙarƙashin tasirin Da’awar Shaikh Zakzaky (H), yanzu duk waɗannan abubuwa suna kwaranyewa sannu a hankali, galibi yanzu ana kiran yara ne da sunayensu na addini ba na al’ada ba. Sannan ana sa wa yara sunaye da inkiya masu daɗi da ma’ana, musamman yadda Shaikh ɗin ya koyawa al’umma sa sunayen jikokin Annabi (S) da ‘ya’yayensu, kuma abun ya ratsa gidan kowa har da Wahabiyawa. Yanzu maimakon sunayen su Mati da Lado, za ka riƙa jin sunaye ne daɗaɗa, irinsu Al’ameen, Haneef, Munzir, Ma’aruf, Faisal, Sadiƙ, Arafat, Zahra, Yaseera, Afrah, Humaira, Sajida, Muslimah, Suhaila, Zeenat da sauransu.

YAƊA MANUFA: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara koyawa musulmin wannan nahiya yadda za su dogara da kansu wajan bayyana ra’ayoyi da manufofi da aƙidunsu da kansu ga al’umma ta kafofin yaɗa labarai da na sadarwa, ba wai su shantake ta hanyar dogaro da kafafen yaɗa labarai na gwamnati da masu zaman kansu su tallata su ba, domin kayan aro ba ya rufe katara, kuma maƙiyinka ba zai ma kyakkyawan wakilci ba. Shaikh (H) ya nunawa ƙungiyoyin musulmi muhimmancin samar da kafar sadarwa ne ta hanyar samar da jaridar ALMIZAN da Mujallar GWAGWARMAYA, waɗanda ke bayyana saƙon Da’awarsa da manufarta, don al’umma su san manufar Da’awarsa daga bakinsa ba daga bakin wasunsa ba, daga baya an ƙara samar da jaridar “POINTER EXPRESS” da Mujallar “MUJAHIDAH”.

Sakamakon wannan darasi da Shaikh Zakzaky (H) ya nuna, sai ga ƙungiyoyin addini su ma sun shiga koyi da shi, Wahabiyawa suka samar da jaridar “AS-SUNNAH” da Mujallar “SAUTUS-SUNNAH”. ‘Yan Tijjaniyya suka samar da Mujallar “AL-KIBLAH”. ‘Yan Ƙadiriyya suka samar da Mujallar “SAUTUL-WAHDA”. ‘Yan Jama’atut-Tajdeedul-Islam suka samar da Jaridar “ATTAJDEED”. ‘Yan Salafiyya suka samar da jaridar “ATTATBEEƘ”. ‘Yan Shi’a Taƙleedi suka samar da Mujallar “AL-MAUZOON”. ‘Yan Shi’a ‘Commercial’ suka samar da jaridar “AHLUL-BAITI” da dai sauransu. Wannan yana nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ya cimma nasarar dasa ingantattun tunanuka a cikin al’umma.

RAYA SUNNONI: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi tasiri sosai cikin al’umma a fagage da dama, musamman a fagen raya wasu sunnonin da aka yi watsi da su, misali; Shi ya raya al’amarin sanya Zobe, wanda bayan Istibsari ta kai ga maza suna sanya zobba masu alfarma. Shi ya raya taron addini da ake ƙira “Goron Sallah”, duk wata ƙungiyar addini da take taro da sunan ‘Goron Sallah’ ta kwaikwaya ne daga gare shi. Shi ya raya yin Tafsiri ba tare da Alaramma mai jan baƙi ba, kafinsa ba a san yin hakan a matsayin Sunnah ba. Shi ya raya ziyarar malamai mabanbanta ra’ayi ga junansu, kafinsa ba a san malamai da ziyarar juna in ba ‘yan ƙungiya ɗaya ba. Shi ya raya batun Shariftaka, har ta kai ga yanzu al’amarin Shariftaka ya zama muhimmin al’amari a cikin al’ummarmu.

Shi ya raya Maulidin Annabi (S) ta hanyar ƙirƙiro yin Muzahara a ranar, wanda yanzu ya zama bikin addinin da ya fi kowanne armashi a Nijeriya. Shi ya raya mutunta Rawani, domin a baya kowa ma yana naɗa Rawani in ya ga dama, amma yanzu an barwa malamai yin Rawani saboda mutuntawa. Kuma ga shi yanzu yana raya maƙarbartu da ƙaburburan mamata, ta hanyar gyara su da ƙawata su da yi musu ado da kwalliya da fulawowi, ta yadda maƙabartun sun soma zama wurin ziyara mai ban sha’awa, maimako yadda a da suka zamo dazuka na ban tsoron Fatalwa, da ramukan Macizai, Ɓeraye, Buragu da ƙwari.

Wannan sauyi da Shaikh Zakzaki (H) ke ta samarwa a cikin al’umma, yana ƙara tabbatar da baiwar da Allah yai masa ta musamman. A taƙaice, waɗannan abubuwa suna daga cikin fitattun nasarorin da Shaikh Zakzaky (H) ya samar a cikin al’umma, madalla da wannan Jagora!

MATSAYINSA A DUNIYAR SHI’ANCI:
Babu tantama ko ja-in-ja game da matsayin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a duniyar Shi’anci, domin memba ne a Majalisar Ahlul-Bait ta duniya, wato (Ahlul-Bait World Assambly). Memba a Majalisar Taƙreeb na Mazhabobin Musulunci, wato (The World Forum for Proximity of Islamic Thoutht). Memba a majalisar haɗin kan Shi’a ta duniya, wato (World Federation Shi’a Khoja). Memba a majalisar goyon bayan Palasdinawa ta duniya, wacce Dr. Zahra Khumaini ke wa jagoranci. Memba a ƙungiyar taimakawa Intifadar Palasdinawa ta duniya, wato … Memba a ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta musulunci ta duniya, wato (International Islamic Human Right) mai hedikwata a birnin London, sannan shi wakili ne a wasu majalisu da ƙungiyoyi da dama na duniya.

Kamar yadda ba buƙatar tsawaita bayani game da karɓuwarsa da martabawar da duniyar Shi’anci ke masa, domin waɗannan wasu abubuwa ne da ke bayyane a fili ƙarara, musamman ga wanda ke bibiyar kafafen sadarwa na zamani.

Misali; A duk lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fita zuwa wata ƙasar waje, musamman Iran, Iraƙi, Lebanon da ƙasashen Turai, Asiya, ko Afirka, za ka ga irin tarba ta girmamawa, da liyafofin karramawa, da gayyace-gayyacen jawabi, da neman ganawa a keɓe, da sauran abubuwa na gayar karamci da ake masa, wannan kawai ya isa ya tabbatar da abin da muke faɗa.

Wata babbar shaidar da ta bayyana matsayin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a duniyar Shi’anci shi ne waƙi’ar Muzaharar Ƙudus da ta auku a birnin Zariya a shekarar 2014, inda sojojin gwamnatin Nijeriya suka kashe almajiransa guda 33 a lokacin wannan Muzahara, ciki har da ‘ya’yansa guda uku.

Yadda duniyar Shi’a ta tankawa wannan ta’addanci da aka yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya nuna ko waye Shaikh ɗin a duniyar ta Shi’anci, domin kusan ba wani babban Marja’i a duniya da bai yi Allah wadai, tare da rubutowa Shaikh Zakzaky (H) wasiƙar jaje da ta’aziyya ba. Maraji’ai da manyan malaman Shi’a daga kowane sashe na duniya sun rubuto wasiƙun jaje da ta’aziyya ga Shaikh, wasu ma sun tado jakadu ne musamman daga ƙasashensu, inda suka zo takanas ta Kano don jajantawa Shaikh Zakzaky (H), ciki kuwa har da Marja’il A’ala Ayatullah Sayyid Ali Hussain Khamna’i (DZ), wanda ya tado wakili na musamman Ayatullah Muhammad Hassan Akhtari don jajantawa.

Abu na biyu da ya ja hankali ga matsayin Shaikh Zakzaky (H) a duniyar Shi’anci shi ne, yadda manyan Maraji’ai sanannu a duniya suka riƙa kiran Shaikh Zakzaky (H) da sunaye na daraja da girman matsayi ta fuskar ilimi, malanta, jihadi da jagoranci, kamar kiransa da Al-Mujaheed, ko Al-Muslih, ko Ayatullah, ko Allamah da sauransu.

Daga cikin wasiƙun da Maraji’ai da manyan malaman Shi’a suka kira Shaikh Zakzaky (H) da “Samahatul ALLAMAH Al-Mujaheed Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)” mafiya jan hankali sune na Hujjah Muhsinul Araky, shugaban majalisar haɗin kan Musulmi ta duniya, wato “Majma’ul Aalamy Littaƙribi Bainal Mazahibil Islamiyyah”.

Sai wasiƙar Sayyid Aliy Ƙadhiy Askar, Amirul Hajji na ƙasar Iran, kuma Wakilin Sayyid Ƙa’id kan al’amuran Hajji. Sai wasiƙar Ayatullahil Uzmah Alawy Karkany, fitaccen Marja’i a duniya. Sai wasiƙar Jami’ar Al-Mustapha ta duniya, wato “Jami’atul Mustapha Al-Aalamiyyah, Lebanon” da sauransu, (duba kwafin wasiƙun a shafin Harka Islamiyya na Intanet, ko ka duba Al-Mizan bugu na 1142 shafi na 7, da bugu na 1144 shafi na 5).

Nasabta Kalmar “Allamah” da fitattun Maraji’an duniya da suka cika sharuɗɗan Ijtihadi suka yi ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta nuna daraja da girman da yake da shi ne a da’irar Shi’anci na duniya, kuma ya nuna mustawar ilimin Mujaddadin wannan ƙarnin!

Amma abin da ya fi nuna girman daraja da zurfin matsayin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a duniyar ɗan adam baki ɗaya, da duniyar musulmi ta wata fuska, da kuma duniyar Shi’a a fuska ta musamman, shi ne, faruwar waƙi’ar ta’addancin sojojin Nijeriya na abkawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa a farkon watan Maulidi na shekarar 1437, wanda ya yi daidai da 12-12-2015.

A wannan waƙi’ar, wacce aka kashe ɗaruruwan almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ciki har da ƙarin ‘ya’yansa guda uku, aka harbi matarsa Malama Zeenatuddeen a wurare da dama na jikinta, sannan shi kansa Shaikh ɗin aka yi masa ruwan harsashi da nufin kashe shi, amma Allah ya ƙi ɗaukar ransa, daga ƙarshe suka kama shi suka tsare. Wannan abu da aka yi wa Shaikh Zakzaky (H) ya girgiza duniya, wanda nan da nan duniya ta yi Allah wadai da abin da sojojin Nijeriya suka yi, ƙasashe da dama sun yi tir da Allah wadai, wasu a gwamnatance kai tsaye, wasu ta hannun jakadun Nijeriya da ke ƙasashensu.

Ta ɓangare guda kuma, al’ummomin ƙasashen duniya daban-daban ne suka fito kan tituna don yin tir da Allah wadai, tare da nuna rashin amincewarsu ga abin da aka yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da kuma kira ga gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta sakin shi. An yi zanga-zanga da muzaharori da gangamin ɗimbin mutane a ƙasashe kusan 80 na duniya, ciki har da Iran, Iraƙi, Lebanon, Indiya, Amurka, Ingila, Denmark, Norway, Afirka ta kudu, Malesiya, Ghana, Phakistan, Mali, Philipines, Kashmir, Moroko, Dubai, Nijar, Yamen, Kamaru, Bahrain, da sauransu. Wannan martani na bai ɗaya da duniya ta mayar dangane da kama Shaikh Zakzaky (H), ya ƙara nunawa duniyar girman matsayin Shaikh ɗin da gayar tasirinsa a duniyar Shi’anci baki ɗaya.

A jawabi na musamman da shugaban Shi’a na duniya Ayatullah Sayyid Ƙa’id Aliyul Khamna’iy (DZ) ya yi wa manyan malaman Shi’a a ganawar musamman da ya yi da su a falonsa cikin watan Janairun 2016, ya nuna cewa wajibi ne duniya ta yi tir da abin da ya faru ga Shaikh Zakzaky (H). Ya ce; “Me ya sa al’ummar musulmi su ka yi shiru akan abin da ya faru ga wannan Shehin Malami, Mumini, mai kawo Gyara, mai son Zaman Lafiya, mai haɗa kan (musulmi) Shi’a da Sunnah waje guda! An kashe aƙalla kusan mutum dubu da ke tare da shi, sannan ‘ya’yansa sun yi Shahada!” (Sayyid Ƙa’id ya yi wannan jawabi ne ranar 24 ga watan Janairu na shekarar 2016).

KARRAMAWA (AWARDS) DA AKA BA SHI:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin muhimman mutanen da aka yi ta karramawa da muhimman kyaututtuka a duniya, an ba shi kyauttuttukan karramawa masu yawa a ƙasashe da cibiyoyi daban-daban, kaɗan daga cikin muhimman karramawar da aka yi masa sune;

  1. NA ƊAYA: A watan Janairu na shekarar 1980 Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya amsa gayyatar halartar wani taro akan Musulunci a ƙasar Iran, bayan kammala taron an karrama Shaikh (H) da ganawa ta musamman da Imam Khumain (QS), wanda ke kwance a gadon asibiti yana jinya a lokacin. A ƙarshen ganawar, Imam Khumain (QS) ya ɗauki Alƙur’aninsa da yake karatu da shi ya ba Shaikh Zakzaky (H) a matsayin kyautarsa ta karramawa gare shi, inda ya umarce shi da cewa; ya je ya kira mutane zuwa ga aiki da Alƙur’ani.

  2. NA BIYU: Gwamnatin mulkin soja ta jahar Kaduna a Nijeriya cikin shekarar 1996 ta karrama Shaikh (H) da “Award” a matsayin mutum mafi tasiri da ya fi kowa son zaman lafiya a ƙasa. Gwamnan soja na wancan lokacin Kanar Lawal Ja’afaru Isah ne ya jagoranci karrama Shaikh (H) da wannan kyauta, kuma Shaikh Zakzaky ya kafa shaida da wannan “Award” ɗin a kotu a lokacin da ake shari’arsa a 1998.

  3. NA UKU: Ƙungiyar Hizbullah da ke ƙasar Lebanon ƙarƙashin jagorancin Sayyid Hassan Nasrullah, ta karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekararriyar Tutar Haramin Imam Hussain (AS).
  4. Wannan muhimmiyar karramawa ta baƙar Tutar da ke filfilawa akan Ƙabarin Sayyidish-Shuhada (AS) mai ɗauke da kalmar “Labbaika Yaa Hussain!” an yi ta ga Shaikh (H) ne a shekarar 2012.

  5. NA HUƊU: Haramin Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala a ƙasar Iraƙi, ya Karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekararriyar Tutar da ke filfilawa a saman Haramin garkuwan Imam Hussain (AS) wato Abul-Fadal Abbas (AS), wanda ake wa laƙabi da “Ƙamaru Bani Hashim”. An karrama Shaikh (H) da kyautar Tutar Hubbaren Abul-Fadal ne a shekarar 2013.

  6. NA BIYAR: Ƙungiyar tara gudunmawar jini ta ƙasa, wato “National Blood Transfussion Services” ta karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da “Award” na musamman don jinjina masa da godiya gare shi bisa umartar miliyoyin almajiransa da ya yi da taimakawa majinyata da gudunmawar jini a duk faɗin ƙasar, kuma wannan gudunmawar jini da ɗimbin almajiran Shaikh ke bayarwa ta dindindin ce a kowace Munasaba ta bikin haihuwa ko juyayin wafatin wani Ma’asumi (AS). An karrama Shaikh Zakzaky (H) da wannan kyauta ne a shekarar 2013.

  7. NA SHIDA: Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya wato “Chirisian Association of Nigeria” (CAN) ɓangaren matasa, a shekarar 2014 ta Karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da “Award” na gwarzon Malami mai ƙaunar al’umma da samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin ma’abuta banbancin addini.

  8. NA BAKWAI: Ƙungiyar kula da iyayen gwarazan Shahidai ta Duniya mai hedikwata a ƙasar Iran, ta karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da kyauta ta “Uban Gwarazan Shahidai”. An shirya babban taro ne a Iran, inda aka gayyaci iyaye da dangin gwarazan Shahidai daga ƙasashe daban-daban na duniya aka karrrama su. Kuma Shaikh Zakzaky (H) ne ya zamo gwarzon uba a wannan taron, don shi ne ya rasa haziƙan ‘ya’yansa uku a rana guda. An karrama Shaikh (H) da wannan kyauta ne a shekarar 2014.

  9. NA TAKWAS: Haramin Imam Ridha (AS) da ke birnin Mashhad a ƙasar Iran ya karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da matsayin “Hadimin Imam Ridah (AS)”, inda aka ba shi “Award” haɗe da koriyar Tutar da ke filfilawa a saman ƙabarin Imam Ridha (AS), wanda aka tara manyan Maraji’ai don su shaida bikin wannan karramawa da aka yi ga Shaikh (H) a Hubbaren Imam Ridah (AS) a watan August na shekarar 2015.

  10. NA TARA: Haramin Sayyida Fatimah Ma’asuma (SA) da ke ƙasar Iran, ya karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekararriyar Tutar da aka lulluɓe Hubbaren na ƙanwar Imam Ridah (AS), a wani ƙwarya-ƙwaryan biki a babban ofishin Haramin da ke birnin Isfahan na ƙasar Iran cikin watan Zulhajji na shekarar 1436, wanda ya yi daidai da ƙarshen watan August 2015.

  11. NA GOMA: Haramin Sayyida Zainab (SA), da ke birnin Dimashƙa a ƙasar Siriya, ya karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da kyautar Tutar da ta shekara tana lulluɓe da ƙabarin Sayyida Zainab bint Amiril Muminin (SA), wanda aka shirya biki na musamman a ɗakin taro na Mahdiyyah da ke birnin Mashhad Iran don karrama Shaikh ɗin da wannan Tuta mai alfarma. An yi wannan karramawa ga Shaikh (H) ne ran 20 ga watan Janairu na shekarar 2016, lokacin yana tsare a hannun gwamnatin Nijeriya, wasu almajiransa ne suka wakilce shi a bikin.

  12. NA SHA DAYA: Ƙungiyar kula da al’adu ta ƙasar Iran mai suna “Iranian Cultural Caravan” wacce ke ƙarƙashin cibiyar “Under The Shade of The Sun”, wacce kuma kula da Haramin Imam Ridah (AS) ke ƙarƙashinsu, sun karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da kyautar Tutar da ke filfilawa a saman Hubbaren jikan Manzon Allah (S) kuma Khalifa na 8 a jerin Khalifofin Annabi (S) na Shari’a (wato Imam Aliyur-Ridah (AS)). An yi wannan karramawa ne ranar Juma’a 04 ga August 2016, kuma duk da cewa Shaikh Zakzaky (H) yana tsare a kurkuku a lokacin, amma an iya isar masa da tutar don Tabarruki.

  13. NA SHA BIYU: Gamayyar ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan na jihohin kudancin Nijeriya, wato “Southeast Based Coalition of Human Rights Organisations” (SBCHRO’s) a taƙaice, wacce ta ƙunshi ƙungiyoyi 12 na kare haƙƙin ɗan adam a Nijeriya, sun karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da “Prestigious Award” na “Prisoner-of-Conscience” wato (POS) a taƙaice. Sun yi wannan karramawa ne ranar 17 ga watan August na shekarar 2016 a birnin Ummuahia na jihar Abia.

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin Mr. Emeka Umeagbalasi ya ce; Mun karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky da wannan “Award” da ya ginu akan cika ƙa’idojin Majalisar ɗinkin duniya na wanzar da zaman lafiya da yaƙi da wariya ne, bisa irin al’ummar da ya samar mai tsananin hangen nesa da aiki da hankali, “Domin an tsare shi tsawon lokaci bayan an harbe shi da kashe masa ‘ya’yansa da ɗimbin mabiyansa, amma har zuwa yau ba a samu yamutsi ko hargitsi ko tashin hankali da sunansa ko na mabiyansa ba!” Sun karrama shi ne duk da cewa yana tsare a kurkuku a lokacin.

Waɗannan jerin “Awards” da karramawa guda 12 da muka ambata ba suke nan ba, an ba Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) “Awards” da dama a wurare da ƙasashe da dama, mun ambaci waɗannan ne a matsayin misali.

YABO DA JINJINA A GARE SHI:
Tirƙashi! Idan mutum yana so ya ɓaro aiki, to ya nemi sanin yawan yabon da mutane daban-daban suka yi ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin linzami ya fi ƙarfin bakin kaza. Za a iya wallafa manya-manyan littattafai akan yabo da kyawawan zantukan mutane akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), amma da yake komai muna taƙaitawa ne, bari mu bada ‘yan misalai na yabon ɓangarorin al’umma gare shi.

  1. YABON KIRISTOCI: Kiristocin Nijeriya na ɓangarori daban-daban sun sha yabawa Shaikh Zakzaky (H) a lokuta da dama, wannan yabo sukan yi shi a ƙungiyance da ɗaiɗaikunsu, sun sha kwatanta halayensa da na Annabi Isa (AS), sukan ce shi ne “Small Jesus” ko “The Saviour” ko “The Mesiah” da sauransu.
  2. Rebaran Musa D. Musal na cocin Angilika a Gombe, ya faɗi a wani jawabinsa cewa; “Ɗabi’un Shaikh Zakzaky irin na Annabawa ne. Kusan shekaru 20 ina tare da Shaikh, ina jin karatuttukansa, har ta kai ga na ɗauki Shaikh a matsayin jagorana! Akwai Shehunnai a ƙasar nan, amma Shaikh Zakzaky ya fita daban a cikinsu… dan haka addu’ata da zan yi ga Shaikh shi ne, Allah ya ƙarfafe shi, Allah ya sa shi ne wanda zai zama sanadin tsiranmu a wannan nahiya” (Rebaran Musa ya yi wannan jawabi ne a taron Mu’utamar na Matasa na ƙasa da aka yi a Bauchi, ranar 7-Zulƙa’ada-1436).

    Wani Fadan kirista, kuma shugaban ƙungiyar yaƙi da cin hanci ta “Anti Corruption Network” a Nijeriya, Mr. Ebenezer Onyetekan ya faɗi cewa; “Yadda na ga ɗabi’un Shaikh Zakzaky da halayensa, da kuma salon Da’awarsa, ko da Musulunci zan yi, to Shi’a zan yi!” (Ya faɗi wannan ne a taron tunawa da Shahidan Ƙudus karo na farko, ranar Lahadi 26 ga watan Yulin 2015, a Sheraton Hotel Abuja).

    Fasto Meter Peller na Cocin Anglican Abuja, ya faɗi a wata hirarsa da ‘yan jarida cewa; “Malam Zakzaky ba irin sauran malamai ba ne da za su ce abu su kuma kasa aikatawa, Malam yana faɗa ne da aikatawa, kuma muna gani a zahiri. Kuma lallai wannan mutumin ya kamata ya zama Uba ga kowa, kuma ya kamata ni in zama ɗa gare shi daga cikin ‘ya’yansa!” (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1256, shafi na 08).

    Malam ya zama ‘Bridge Builder’ mai gina gadar fahimtar juna tsakanin kudu da arewa, da kuma tsakanin Kirista da Musulmi, Ibo da yawa sukan ce in dai za su yi Musulunci, to irin na Zakzaky za su yi, wani ma cewa ya yi “This man na freedom fighter” wato wannan mutumin mai ƙwatarwa raunana ‘yancinsu ne”. (Malam, Malam Ne, shafi na 18).

  3. YABON ƘADIRIYYA: Limamin Ƙadiriyya na Afirka, Shaikh Muhammad Nasiru Kabara (RA) tun yana da rai aka ruwaito cewa, wata rana da Shaikh Zakzaky (H) ya ziyarce shi, a jawabinsa ya ce; Duk ɗan Ƙadiriyar da ya soki Da’awar Shaikh Zakzaky ya ci amanar Ƙadiriyya!”. Sannan kusan baki ɗayan ‘yan gidan Ƙadiriyya ba wanda bai ya bi Shaikh Zakzaky (H) da yabo kyakkyawa ba a lokuta daban-daban.

  4. YABON TIJJANIYYA: Shaikh Murtadha Abul-Fathi, wanda ɗa ne ga babban jagoran Tijjaniyya a Nijeriya, kuma ɗaya daga cikin jigoginta na duniya, wato Shaikh Abul-Fathi Maiduguri, a jawabinsa na wani taron “Makon Haɗin Kan Musulmi” da aka yi a Zariya, ya ce, duk wata kamala (Qualities) na Annabawa (AS) to Shaikh Zakzaky (H) ya siffatu da su, “Da ba don na riga na yi wa Shaikh Ibraheem Inyas mubaya’a ba, to da na miƙa hannuna na mubaya’a ga Shaikh Zakzaky!”.

  5. YABON GWAMNATI: Abin mamaki game da Shaikh Zakzaky (H) shi ne, hatta gwamnatocin da suke adawa da shi, sun sha yabonsa a fili da ɓoye, misali; Gwamnatin jahar Kaduna ta taɓa ba shi takardar karramawa (Certificate) a matsayin gwarzon mutumin da ya fi kowa kawo zaman lafiya a ƙasa, wanda gwamnan jahar Kaduna na mulkin soja Laftanar Kanal Lawal Ja’afaru Isah ya ba shi a shekarar 1996 kafin Janar Abacha ya kama shi a wancan lokacin.
  6. Haka nan, wasu daga cikin manyan Sarakunan gargajiya mafiya daraja a Nijeriya, sun sha yabawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), misali, marigayi Sarkin Kano Dr. Alhaji Ado Bayero CFR, ya sha yabawa Shaikh Zakzaky, har ma ya taɓa fitowa fili ya yi kiran da a sake shi lokacin da gwamnatin Janar Abacha ta kama shi, kuma ya yi Allah wadai da gallazawar da ake masa.

    Haka nan Sarkin Zazzau Dr. Alhaji Shehu Idrees CFR, ya taɓa jinjinawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a wata hira da aka yi da shi lokacin da ya cika shekaru 30 akan gadon Sarauta, an tambaye shi ne me zai ce game da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)? Sai ya ce; “Malam Ibraheem Zakzaky yana cikin ‘ya’yanmu masana masu albarka, shi ɗan mu ne mai albarka!” (Al-Mizan, bugu na 657, shafi na 3, 10-Muharram-1426).

  7. YABON ALMAJIRANSA: Yabon almajiran Shaikh Zakzaky (H) gare shi abu ne da bai misaltuwa, wani almajirinsa a littafin da ya rubuta mai suna “Tarihin Harkar Musulunci” yana cewa; “Akwai sunnoni da yawa na Manzon Allah (S), Shukran Laa-fakhran, Sayyid Zakzaky (H) shi ne asasin raya su a wannan nahiya ta mu da muke ciki, wanda ba ‘yan uwa kawai ba, a’a hatta sauran jama’ar gari, da yawa sun kwaikwayi waɗannan sunnoni”.

RUBUCE-RUBUCE AKANSA:
Ta ɗaya janibin kuma, akwai littattafan da aka rubuta akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da rayuwarsa, wanda littattafai ne ƙanana, amma sun yi tsokaci akan wasu muhimman janibobi na rayuwarsa.

  1. NA ƊAYA: Littafi na farko game da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne; “Kitabul Bushra” wanda littafi ne da ya yi magana akan albishirin bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Waliyi kuma mujaddadi Shehu Usman Bin Fodiye ya yi tun fiye da shekaru 200 kafin haihuwarsa. An buga littafin ne a shekara ta 1416 Hijira, Edita Malam Ibrahim Musa ne ya wallafa littafin.

  2. NA BIYU: Littafin “Malam Zakzaky (H) Rayuwarsa da Karamominsa”, wanda shi kuma laccocin wasu malamai guda biyu ne akan rayuwar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) aka mayar da su littafi, ya ƙunshi tsokaci akan ɓangarori daban-daban na rayuwar Shaikh Zakzaky (H). An buga littafin ne a shekarar 1416 Hijira, malaman da suka gabatar da jawaban littafin su ne Shaikh Ya’aƙubu Yahya Katsina, da Malam Abubakar Abdullahi Sokoto.

  3. NA UKU: Littafin “Tauhidin Kalma Daga Rayuwar Mujaddadai”. Shi wannan littafin littafi ne na falsafa, wanda ya ƙunshi salo da kalmomi masu sarƙaƙiya, yana kwatanta dacewar salon rayuwar bayin Allah ne ma’abuta Tajdidin addini, inda ya kwatanta dacewar rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da sauran Mujaddadan addini da suka gabace shi. An wallafa littafin ne a shekarar 1997, marubucin littafin shi ne Malam Ibrahim Muhammad Potiskum.

  4. NA HUƊU: Shi ne littafin; “Yusufuz-Zaman”. Shi wannan littafin ya fito da darussa ne na dacewar rayuwar Shaikh Zakzaky (H) da ta Annabi Yusuf (AS), ta yadda ya gaji halayya da ɗabi’u da yanayin rayuwar Annabi Yusuf (AS) musamman ta fuskacin jarabawar garƙamewa a gidan kurkuku. An wallafa wannan littafi ne a shekarar 1998, marubucin littafin shi ne Malam Ibrahim Muhammad Potiskum.

  5. NA BIYAR: Shi ne littafin “Wakilin Manzon Allah (S) a Doron Ƙasa”. Shi wannan littafi an gina shi ne akan hujjoji na nassi da na hankali da na zahiri da ke nuna cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) magajin Manzon Allah (S) ne a wannan nahiya, domin ayyukansa da ɗabi’unsa da halayensa suna kama da na Manzon Allah (S). Littafin na ɗaya da na biyu ne, kuma an buga su ne a shekarar 1997 da 1998 Miladiyya, marubucin littafin shi ne Malam Ɗanjuma Katsina.

  6. NA SHIDA: Shi ne littafin “Bayyanar Sharafuddin”. Shi wannan littafi shi ne irinsa na farko a fagen hallale bayani akan rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) daki-daki. Littafin ya ƙunshi magana akan Shaikh Zakzaky (H) tun daga wasiyyoyin bayyanarsa, zuwa asalin zuriyya da nasabarsa, har zuwa yarinta, karatu, gwagwarmaya, kulen da ya fuskanta, da sauran ɓangarorin rayuwarsa. An buga littafin ne a shekarar 2001 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Malam Al-Ameen Isa Al-Sakkwaty.

  7. NA BAKWAI: Shi ne littafin “Malam Malam Ne”. Wannan littafi ya ƙunshi muhimman bayanai game da wasu ɓabgarori na rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da baiwar da Allah Ta’ala ya yi masa a ɓangare daban-daban. Asalin littafin rubuce-rubuce ne da mawallafin ya yi a jaridar ALMIZAN, shi ne aka tattara su wuri guda aka maishe su littafi. An buga littafin ne a shekarar 2007 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Marigayi Malam Haruna Shelleng.

  8. NA TAKWAS: Shi ne littafin “Shekaru 60 Masu Albarka”. Shi wannan littafin ya ƙunshi hirarraki ne da mutane daban-daban akan rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tun daga yarintarsa har zuwa cikarsa shekaru 60 a duniya. An yi hira da iyalansa, da ‘ya’yansa, da abokansa, da danginsa na jini, da almajiransa, da sauran jama’ar da suka san shi, kuma a ƙarshen littafin an kawo wasu rubuce-rubuce akansa. An wallafa littafin ne bayan bukin cikar Shaikh ɗin shekaru 60 da haihuwa a shekarar 1433, wanda ya yi daidai da farkon shekarar 2012 Miladiyya. Mawallafin littafin shi ne Edita Malam Ibrahim Musa.

  9. NA TARA: Shi ne littafin “Mujaddadin Wannan Ƙarnin”. Shi wannan littafi ne da ya ƙunshi bayanai akan rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da hujjoji akan zamowarsa Mujaddadin addini a wannan nahiya. Marubucin ya kawo hujjoji na naƙali da na hankali da ke tabbatar da cewa Shaikh Zakzaky (H) Mujaddadin addini ne. An buga littafin ne a shekarar 2013 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Muhammad Nasir Miji Gombe.

  10. NA GOMA: Shi ne littafin “Sallah Mafificiyar Ibada”. Shi wannan littafi ya ɗauki janibi ɗaya ne kacal, wato sallolin Shaikh Zakzaky (H) ya yi bayani akai, cike yake da hotunan Sallolin Shaikh Zakzaky (H) tun daga na Yaumiyya har zuwa Idi da sallar Jana’iza. An kawo dukkanin karance-karance, da addu’o’i, da Azkar, da Alƙunut ɗin da Shaikh Zakzaky (H) ke yi ne a cikin sallolinsa, da surar yadda yake wasu ayyukansa na Sallah a cikin hotuna masu kala. An wallafa littafin ne a shekarar 2014. Marubucin littafin shi ne Abdullahi A. Hamza.

  11. NA SHA DAYA: Shi ne littafin “Tarihin Sayyid Ibraheem Yaƙub Al-Zakzaky da Harkar Musulunci”. Wannan littafi shi ne irinsa na farko a bisa salo da usulubinsa, domin littafin ya ƙunshi ɓangare biyu ne, ɓangaren tarihin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da kuma ɓangaren tarihin Da’awarsa ta Harka Islamiyyah. A irin wannan usulubi, za a iya cewa shi ne littafin tarihin Harka Islamiyyah na farko. An wallafa littafin ne a shekarar 2015 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Malam Muhammad Sulaiman Kaduna.

  12. NA SHA BIYU: Shi ne littafin “Shaikh Zakzaky Ikon Allah!” wato wannan littafin da ke hannun mai karatu, shi ya ƙunshi tsokaci ne akan ɓangarori da dama na rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da tarihinsa ataƙaice. An kammala rubuta littafin ne a shekarar 2017 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Adamun Adamawa.

A taƙaice, waɗannan sune littattafan da aka rubuta kacokam akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da abubuwan da suka shafe shi, amma akwai littattafai da dama da suka ambaci wani sashe na rayuwarsa a wasu babukansu. Sannan wannan littatafan da aka rubuta da Hausa ne kawai, banda na Larabci, Turanci, Projects, Mujallau da sauransu.

WAƘOƘIN DA AKA YI AKANSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin mutane ƙalilan da tarihi zai ayyana cewa an yi ɗimbin waƙoƙin yabo a kansu, domin zuwa yanzu abu ne mai matuƙar wahala a iya ƙiyasi ko kirdadon adadin waƙoƙin yabon da aka yi a kansa. Tun a ƙarshen shekarun 70s waƙoƙi akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Da’awarsa suka soma karaɗe sassa da lungunan Nijeriya da ƙasashe maƙwabta, kuma har ya zuwa yanzu sai abin da ya ƙaru.

An yi waƙoƙi marassa ƙirguwa akan Shaikh Zakzaky (H) da Da’awarsa, hasali ma akwai ƙungiyar mawaƙa na Harka Islamiyya mai suna “Ittihadus-Shu’ara Lil Harkatil Islamiyyah”, wanda suke taimakawa da fasaharsu wajan wayar da kan jama’a game da manufar Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Babu shakka mawaƙa da daman gaske sun yi waƙoƙi da yawa akan Shaksiyyar Shaikh Zakzaky (H), wanda zai yi wuya a iya ƙididdige su, to amma mawaƙan da suka fi kowa yin fice akan yi wa Shaikh Zakzaky (H) waƙoƙi sune Alhaji Mustapha Gadon Ƙaya, da Malam Ammar Muhammad Ɗan Tinka.

Shi Alhaji Mustapha Gadon Ƙaya ya yi waƙoƙin yabon Shaikh Zakzaky (H) da dama, daga cikin wanda suka yi fice akwai; “Yaa Sharafaddeeni Maraba”. Da “Imamul Bara’ati Labbaika!”. Sai “Ya Malam Zakzaky, Ibraheemu Baban Nusaiba Tsayayye”. Sai “Ibraheem Zakzaky, Labbaika ya Zakzaky”. Sai “Ya Zakzaky ƙara yin Juriya Jagoran Addini Babba”. Sai “Akan Zakzaky Mu Ba Mu Shakkar Uban Kowa!”. Sai “Ya Allah Kare Al-Zakzaky Ƙara Mana Yin Biyayya”. Sai “Ya Hasken Allah Imamu Zakzaky Mai Alfarmaa”. Sai “Al-Zakzaky Kogin Baiwa, Sirri na Allah sai Kallo!”. Sai kuma “Sannu-sannu Dattijo, Wila’armu na gurin Allah, Bai’armu na a hannunka”. Sai kuma “Babu inda ba Allah, in akwai ku kai Malam” da dai sauransu.

Shi ma Malam Ammar Ɗan Tinka Zariya, ya yi waƙoƙin yabo da jinjina ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da dama, daga cikin fitattun waƙoƙinsa akwai; “Yaa Mujaddadi”. Da “Labbaika Zakzakiy Shehu!”. Da “Gaskiya Malam Malam ne”. Da “Haske ya Bayyana Al-Zakzaky Muna nan Bayanka”. Da “Zakzaky Taka da Laafiya!”. Da kuma “Zakzaky Aarifum-Billahi” da dai sauransu.

A gefe guda, akwai wasu fitattun mawaƙa da suka yi waƙoƙi na yabon Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da suka yi tashe a cikin al’umma, daga ciki akwai; Alhaji Mustapha Limanci da waƙarsa ta “Gaisuwa nake Jagorana Shehu Ibraheem Zakzaky. Sani Aliyu Katsina da waƙarsa ta “Lallai-lallai Mun yi Nasara, Malam Zakzaky shi Muka Riƙe!”. Bello Shehu Mafara da waƙarsa ta “Zakzaky Malamin Ulama’u”. Nura Shahidi da waƙarsa ta “Barka da Fitowa Maulana Al-Zakzaky mai Gulbin Baiwa”. Shaheed Shafi’u Kazaure da waƙarsa ta “Ni na maka Bai’a Baban su Nusaiba Zakzaky mai Haiba”. Abdullahi Andu da waƙarsa ta “Imam Khumaini da Malam Zakzaky Mun Faɗi Ɗa da Uba ne”. Marigayi Malam Rabi’u Tudun Iya da waƙarsa ta “Labbaika Shehu Imam Zakzaky”.

Sai Gambo Ɗankaka da waƙarsa ta “Mu dai Al-Zakzaky Muna Son ka Ƙwarai-ƙwarai”. Shareef Uzairu Badamasi da waƙarsa ta “Kada Mage ba Yanka ba, Yaa Shehu Ibraheem Labbaika Zakzaky Mazajen Fama!”. Abdullahi Ɗan Lushi da waƙarsa ta “Yaa Shehu Zakzaky”. Sa’idu Saƙafa Potiskum, da waƙarsa ta “Malamina da na yi wa Mubaya’a Jagorana, Zakzaky na!”. Sani Ɗan Auta da waƙarsa ta “Zakzaky Kainuwa Dashen Allah, mun ji mun Gani”. Musa Ƙasida Gombe da waƙarsa ta Fulatanci “Shehu Zakzaky Modibbo, Wala bamaɗa Nder Moɗiɓɓe”, da dai sauran ɗimbin mawaƙan da ba za su ƙirgu ba.

Wani tabbataccen abu da nazari ya nuna shi ne, duk waƙoƙin da ake yi akan Shaksiyyar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba ƙaramin farin jini da tashe suke yi ba, wataƙil wannan yana da alaƙa da ɗanfaruwar zukatan al’umma ga Shaikh Zakzaky (H) ɗin ne.

KYAWAWAN MAFARKAI AKANSA:
Babu shakka kowane bawan Allah akan samu wasu alamomin da za su zamo shaida akan Khususiyya da darajarsa, ta irin wannan salo ne aka samu isharori da dama game da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) musamman ta hanyar mafarkai, kasancewar mafarki wata hanya ce daga cikin ingantattun hanyoyin Bushara, kenan hakan zai zama abin la’akari ga ma’abuta hankali.

Mafarke-mafarke da ke ishara ga darajojin Shaikh Ibraheem Zakzaky ba su da iyaka, domin jama’a da dama sun sha yin ayyuka “A’amal”, ko su yi wasu addu’o’i na neman ganin Manzon Allah (S) a mafarki, amma maimakon haka sai su yi mafarki da Shaikh Zakzaky a madadinsa, wanda hakan ke nuna wata alaƙa mai ƙarfi da ke tsakanin Shaikh da Manzon Allah (S).

Haka nan, jama’a da dama sun yi mafarke-mafarke da Manzon Allah (S) ko wani Imami daga cikin Ma’asumai (AS), ya umarce su da riƙo da yin biyayya ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), wannan ya sha faruwa hatta ga waɗanda ke ƙiyayya ga Shaikh Zakzaky (H) kamar Wahabiyawa da wasu mabiya ɗariƙun Sufaye. Misali;

A shekarar 1995, wani Bawahabiye a birnin Bauchi ya yi Mafarki da Imam Mahdi (AF), ya ce masa; “In na bayyana kana cikin wanɗanda zan yaƙa!”, sai Bahwahabiyen ya fashe da kuka yana roƙon Imam ya yafe masa laifinsa kuma ya faɗa masa mafita. Sai Imamul-Asr (AF) ya ce masa; “In kana son tsira daga wannan, to ka yi mubaya’a ga mai Da’awar nan na Zariya Malam Ibraheem Zakzaky!”, Da sassafe Bawahabiyen ya yo sammako zuwa cibiyar ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky (H) ta Bauchi, ya faɗi mafarkin da ya yi, kuma ya nemi a miƙa bai’arsa ga Jagora (H).

Sannan a wajajen shekarar 2000, wani ɗan Ahlis-Sunnah a Sakkwato ya yi mafarki game da Shaikh Zakzaky (H), wanda ta sanadinsa ya zama almajirin Shaikh Zakzaky (H). An buga labarin mafarkin nasa a jaridar Al-Mizan. Ya ce;- “Na yi mafarkin an gina wani sabon masallacin juma’a babba a garinmu, sai na ji ana sanarwa cewa za a yi gagarumin taro na bikin buɗe masallacin, kuma babban bako mai buɗe masallacin, wanda kuma zai jagoranci sallar farko a masallacin shi ne Shaikh Ibraheem Zakzaky!

“Sai abin ya bani mamaki, a raina na ce; Zakzaky shugaban ‘yan Shi’a ne zai buɗe mana masallacin garinmu, alhali mu Ahlis-Sunnah ne? Na yi ta tambayar kaina, me ya sa aka gayyato shi? Me ya sa ‘yan kwamitin masallacin ba su ga dacewar gayyatar kowa ba sai shi? Me ya haɗa mu da ɗan Shi’a? A haka dai na haƙura, na yi wanka na sa farar jallabiya, na tafi wajan bikin buɗe masallacin.

“To, inda ake taron buɗe masallacin ƙaton wuri ne kewaye da wata doguwar katanga, ta ƙofa ɗaya ake shiga wurin, gun ya cika maƙil da jama’a, sai aka yi shela cewa kowa ya daidaita sahu za a yi Sallah, na ga Shaikh Zakzaky (H) ya wuce gaba zai ja sallah, sai na riyawa zuciyata cewa; Ni ba zan bi shi Sallah ba!

“Sai na kama hanya zan fita, ina zuwa ƙofa, da na hangi waje, sai na ga mugayen namun daji ne ta ko’ina! Duk wata muguwar dabba akwaita a wurin, Kura, Zaki, Damisa, Gwanki, Dorina, Aladu da sauransu, ga su nan ba iyaka! Suna ta hargowa, suna jiran in fito su cinye ni! Nan take sai na juya da hanzari na koma na shiga sahu na bi Shaikh Zakzaky (H) Sallah! Kawai sai na farka daga barcina.

“Daga nan na sallamawa Shaikh Zakzaky (H), na ce wannan ishara ce ake yi min ta yin biyayya gare shi. Alhamdulillah, yanzu ina cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H). Allah ka tabbatar da mu a bayansa har abada! Dan darajar Manzon Allah (S) da iyalansa tsarkaka!”.

Haka nan, wani mabiyin ɗariƙar Sufanci, ya yi mafarki da Manzon Allah (S), inda ya nuna masa cewa abin da Shaikh Zakzaky ke tafiya akai shi ne shiriya, kuma ya umarce shi da biyayya gare shi muddin yana son tsira cikin sauƙi a gobe ƙiyama. Haka ma wani babban malami daga ƙasar Senegal, mai suna Shaikh Sayyid Haidar Muhammad Shamsuddeen ya yi mafarki har sau uku da Sayyida Fatimah Az-zahra (SA) tana ce masa ya je birnin Zariya a Nijeriya ya yi mubaya’a ga ɗanta Shaikh Ibraheem Zakzaky, a karo na ukun har gargaɗi ta yi masa. Shi ne a shekarar 2014 ya niƙo gari daga Senegal ya zo Nijeriya ya miƙawa Shaikh Zakzaky (H) mubaya’arsa don yin biyayya ga umarnin ‘yar Manzon Allah (S).

Ire-iren waɗannan mafarkai akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba su da iyaka, mun kawo waɗannan ne kawai a matsayin misali, kuma duk da cewa ba kowane mafarki ne hujja ba, to amma ire-iren waɗannan mafarkai bushara ce ingantacciya.

Post a Comment

0 Comments