Kamar Yadda Al'umma Suka Sani A Duk Shekara A Farkon R/Auwal Ƴan uwa Musulmi Al'majiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) Sukan Gabatar Da Biki Na Daura Tutar Mauludi A Ƙubbar Hussainiyya BuÆ™iyyatulah Dake Zaria, Don Nuna Farin Ciki Da Zuwan Watan Mauludin Annabi (SAWA), A Shekara 2015/1436 Kamar Ko Wace Shekara, Ƴan uwa Sun Shirya Tsaf Domin Gabatar Da Wannnan Baban Biki Kamar Yadda Aka Saba, Sai Dai Kuma Wannan Shekara Ta Zo Da Sabon Al’amari, Wanda Bai Taba Faruwa A Shekarun Da Suka Gabata Ba.
A Ranar Asabar 12/12/2015, Kwatsam Sai Ga Rundunar Sojojin Nigeria Sun Zo Dai-dai Ƙofar Husainiyya Suna Raba Duty, A Tsakaninsu, A Kusa Da Muhallin Na Husainiyya, Ba Tare Da Sanin Abinda Ya Kawo Suba.
Fara Taruwar Ƴan uwa Ke Da Wuya, Wadanda Suka Zo Domin Gabatar Da Bikin Sanya Tuta Kawai Sai Sojoji Suka Dirar Musu Da Harbi Da Bindiga, Ba Tare Da Laifin Ƙomi Ba, Al’amarin Da Ya Janyo Rasa Rayukan Ƴan uwa Gami Da Jikkata Da Dama Daga Cikinsu Wanda Ya Hada Maza Da Mata Manya Da Yara.
Hakan Bai Wadace Su Ba, Sai Suka Juya Da Akalar Maitarsu Zuwa Gidan Sheikh Zakzaky (H), Dake Gyallesu A Daren Ranar. Suka Je Suka Shekar Da Jinin Al’umma, Bisa Zalunci, Ba Tare Da Hujjar Komi Ba. Suka Ta Kashe Ƴan uwa Musulmi Tun Daga Wannan Rana Ta Asabar Har Zuwa Ranar Litini Suka Kashe Al’umar Musulmi, Almajiran Sheikh ÆŠin. Daga Bisani Suka Shiga Har Cikin Gidan Sheikh Zakzaky (H) Suka Kashe Ƴar uwarsa Ta Hanyar Ƙonata Da Wuta Akan Idanunsa. Sannan Suka Kashe Uku Daga Cikin ƳaÆ´ansa Duk A Gaban Idanunsa (Aliyu Haidar, Hammad, Humaid) Baya Ga Haka Suka Dirar Masa Da Harbi Da Bindiga Shi Da Mai É—akinsa Malama Zeenatu Suka Yi Ruwan Harshashi Akan Su, Sai Da Tunaninsu Ya Ba Su Cewa Sun Kashesu. Sannan Suka Fitar Dasu Cikin Jini Suka Cinnawa Gidan Wuta Da Duk Abinda Ke Ciki. Suka Tafi Dasu Suka Yasar Dasu Bayan Dan Gajaren Lokaci ALLAH (T) Ya Nufi Bayinsa Da Rayuwa Bayan Kashesu Da Aka Yi.
Sannan Suka Tsare Su Tsawon Kwanaki Fiye Da Ɗari Tara 900 Zuwa Yanzu Ba Tare Dasun Aikata Laifin Komai Ba, Duk Da Umarnin Da Babban Kotun Ƙasa Ta Bayar Na Sakin Shehin Malamin Gami Da Biyansa Diyya Da Gina Masa Muhalli A Duk Inda Yakeso A Faɗin Arewacin Ƙasar. Amma Duk Da Hakan Baisa Gwamnati Ta Bi Umarnin Kotu Ta Saki Malamin Ba, Inda Taka Ci Gaba Da Tsareshi Har Zuwa Yanzu, Bisa Zalunci, Duk Da Kuwa Fafutukar Da Almajiran Malamin Suke Yi Na Ganin Gwamnati Ta Sake Shi Ba Tare Da Wani Sharaɗi Ba.
Daga Cikin Ta’addancin Da Aka Yi Wa Sayyid Zakzaky (H) Da Almajiransa Akwai Kashe Almajiransa, Fiye Da Dubu (+1,000). Ciki Harda ƳaÆ´ansa Guda Uku. Sannan Aka Ƙona Wasu Da Rayukansu, Wasu Kuma Aka Dunga Yi Musu Azaba Har Zuwa Rasuwarsu, Gami Da Yi Wa Mata FyaÉ—e, Da Keta Alfarmarsu, Sannan Aka Bizne Mutane Fiye Da 347 A Rami ÆŠaya, Ba Tare Da Yi Musu Sallah Ko Sittirah Ba (Kamar Yadda Addini Musulunci Ya Tanada). Daga Bisani Suka Kama Da Yawa Daga Ciki Wanda Har Zuwa Yanzu Wasu Ba A San Halin Da Suke Ciki Ba.
Daga Baya Suka Rusa Gidan Sheikh Zakzaky (H) Dake Gyallesu Da Hussainiya Bakiyatullah Da Fudiyya Islamic Centre Dake Ɗanmagaji Zaria Tare Da Maƙabartar Shahidai Dake Dambo, Da Kuma Ƙabarin Mahaifiyarsa Dake Unguwan Jushi Zaria, Da Sauran Wurare.
0 Comments