Sayyida Fatima (S.A)

Sayyida Fatima (SA)

TAƘAITACCEN TARIHIN SAYYIDA FATIMA BINT MUHAMMAD (SA)

SUNA DA NASABARTA (SA):
Sunanta shi ne Fatima bint Muhammad (SAWA) bn Abdullah bn Abdul Mutallib.

MAHAIFIYARTA (SA):
Khadijah bint Khuwailid (SA).

ALKUNYARTA (SA):
Ummu Abiha, Ummul Hasanain, Ummul Raihanatain, Ummul A’imma da sauransu.

LAƘABINTA (SA):
Al-Zahra, Al-Batul, Al-Sadiƙa, Al-Mubaraka, Al-Tahira, Al-Zakiyya, Al-Radhiyya, Al-Mardhiyya, Al-Muhaddatha da sauransu.

TARIHIN HAIHUWARTA (SA):

An haife ta ne a ranar 20 ga watan Jumada Sani, shekara ta biyar da aiko Ma’aiki (SAWA), hakan shi ne abin da ya fi shahara tsakanin Shi'a, wasu kuma suna ganin akasin hakan.

WAJEN HAIHUWARTA (SA):
Garin Makka.

MIJINTA (SA):
Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib (AS).

‘YA’YANTA (SA):
  1. Imam Hasan bn Ali (AS).
  2. Imam Husain bn Ali (AS).
  3. Al-Muhsin (AS), wanda ta yi barinsa.
  4. Zainab Al-Kubra (AS).
  5. Zainab al-Sughra (AS).

RUBUTUN HATIMINTA (SA):
Aminal mutawakkilun.

HADIMARTA (SA):
Fiddha (RA).

SHEKARUNTA A DUNIYA (SA):
Shekaru 18, bisa ga abin da ya fi shahara, wasu kuma suna ganin saɓanin hakan.

LOKACIN SHAHADARTA (SA):
Ta yi shahada ne a ranar 3 ga Jimada Sani, shekara ta 11 bayan hijira, wata ruwayar kuma ta ce 13 ga Jimada Awwal, wasu kuma suna ganin akasin hakan.

DALILIN SHAHADARTA (SA):
Sakamakon matse ta da Umar bn Al-Khattab ya yi tsakanin ƙofa, wanda ya yi sanadiyyar karyewar haƙarƙarinta da kuma nutsewar ƙusa cikin ƙirji, sannan kuma ta yi ɓarin ɗan da take ɗauke da shi wato Muhsin.

ƘABARINTA (SA):
A birinin Madina, sai dai har ya zuwa yanzu ba a tantance inda ƙabarin nata yake ba, saboda wasiyyar da ta yi wa Amirul Muminina (AS) gabannin wafatinta cewa ya bisne ta cikin dare sannan kuma ya ɓoye ƙabarin nata.

Post a Comment

0 Comments