TAƘAITACCEN TARIHIN IMAM HASAN BN ALI (AS)
SUNA DA NASABARSA (AS):
Sunansa shi ne Hasan
bn Ali bn Abi Talib bn Abdul Mutallib (AS).
MAHAIFIYARSA (AS):
Fatima al-Zahra (SA) ‘yar Manzon Allah (SAWA).
ALKUNYARSA (AS):
Abu Muhammad.
LAƘABINSA (AS):
Al-Takiy, Al-Zakiy, Al-Sibt, Al-Tayyid, Al-Sayyid, Al-Wali da sauransu.
An haifi Imam Hasan
(AS) ne a ranar 15 ga watan Ramalana shekara ta uku bayan hijira, wannan shi ne abin da yafi shahara, wasu kuma sun ce a shekara ta biyu hijiriyya.
WAJEN HAIHUWARSA (AS):
Birnin Madina.
YAKUKUWANSA (AS):
Imam Hasan
(AS) yayi yaƙi lokacin yaƙuƙuwan kame Afirka da garuruwan Farisawa tsakanin shekaru na 25 zuwa 30 hijiriyya, sannan kuma ya yi yaƙi tare da mahaifinsa Ali (AS) a dukkan yaƙuƙuwan da ya yi, su ne kuwa:
- Yakin Jamal.
- Yakin Siffin.
- Yakin Nahrawan.
- Ummu Bashir bint Abi Mas’ud Al-Khazrajiyya.
- Khaula bint Manzur Al-Fazzariyya.
- Ummu Ishak bint Talha al-Tamimi.
- Ju’ada bint Al-Ash’ath.
- Zaid bn Hasan.
- Al-Hasan bn Hasan.
- Amru.
- Al-Kasim.
- Abdullah.
- Abdurrahman.
- Husain bn Hasan.
- Talha.
- Ummul Hasan.
- Ummul Husain.
- Fatima bint Umm Ishak.
- Umm Abdullah.
- Fatima bint Hasan.
- Ummu Salama bint Hasan.
- Rukayya bint Hasan da sauransu.
RUBUTUN HATIMINSA (AS):Al-Izzat lillahi wahdahu
, wasu kuma sun ce wani abu ne na daban.
SHEKARUNSA (AS):
Shekaru 47.
SHEKARUN IMAMANCINSA (AS):
Shekaru 10.
SARAKUNAN ZAMANINSA (AS):
Mu’awiyya bn Abi Sufyan.
LOKACIN SHAHADARSA (AS):
7 ga watan Safar shekara ta 49 hijiriyya, wasu kuma sun ce: 28 ga Safar shekara ta 50 hijiriyya.
WAJEN SHAHADARSA (AS):
Birnin Madina.
DALILIN SHAHADARSA (AS):
Ya yi shahada ne sakamakon gubar da matarsa Ju’adata bint Al-Ash’ath ta sanya masa cikin abin sha bisa umarnin Mu’awiyya bn Abi Sufyan.
0 Comments