HAMMAD IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Hammad shi ne É—a na Bakwai a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 10 ga watan Disamba na shekarar 1997. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kuma ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa.
Ya yi shahada ne ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da ranar uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 18 kacal.
Kafin shahadarsa shi ne kwamandan rundunar Æ™ananan yara masu tasowa da ake kira “Kasshafa”. Ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya. HaziÆ™i ne mai kaifin Æ™waÆ™walwa da basira. An shaide shi da yawan ibada, iya mu’amala, da kula da Æ™ananan yara.
0 Comments