ALI HAIDAR IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Aliy-Haidar shi ne É—a na Takwas a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ranar 15 ga watan Satumba na shekarar 1999. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kuma ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa.
Sayyid Ali yana cikin waÉ—anda waÆ™i’ar Ƙudus ta 2014 ta rutsa da su, tare aka kama shi da ‘yan uwansa guda biyu aka tafi da su barikin soji aka yi ta azabtar da su, shi ne kaÉ—ai ya kuÉ“uta da ransa a cikinsu bayan an yi masa harbi da dama tare da dagargaza Æ™afarsa ta hagu, wanda ya jaza dole sai da aka fita da shi waje aka yi masa aiki.
Sayyid Aliy-Haidar ya yi shahada ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da Litinin uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437 Hijira. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 16 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya. Sayyid Aliy-Haidar haziÆ™i ne mai kaifin Æ™waÆ™walwa da basira. An shaide shi da yawan ibada, son karatu, son wasannin motsa jiki, da sauÆ™in kai a mu’amala.
0 Comments