MUHAMMAD IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Muhammad shi ne babban É—a wato É—a na farko a wurin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne a shekarar 1985 (a lokacin mahaifinsa yana tsare a kurkuku sakamakon kamun da shugaban Æ™asa na lokacin Janar Buhari ya yi masa). Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya da Æ™asar Ingila, kuma ya je Æ™asar Iran inda ya karanta darasin “Fasahar Gine-gine” da ake kira “Architecture” a babbar Jimi’ar Tehran (wato University of Tehran) da ke birnin Tehran.
Sayyid Muhammad Æ™wararre ne a yaren Turanci, Farisanci da Hausa. Mutum ne mai tsananin shiru da kawaici da rashin son hayaniya, yana da É—abi’ar kauda kai ga abin da bai shafe shi ba, yana da kaifin basira da hangen nesa, kuma mutum ne mai taka tsantsan akan al’umuran rayuwa. Ya yi aure a watan Mayu na shekarar 2016, a lokacin mahaifinsa yana tsare a kurkuku sakamakon kamun da shugaban Æ™asa Muhammadu Buhari ya sake yi masa a 2015.
0 Comments