Hamid Ibrahim

Hameed Ibrahim Zakzaky (H)

HAMEED IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Hameed shi ne É—a na huÉ—u a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 17 ga watan Janairu na shekarar 1992, ya yi karatun Firamare da Sakandare a Nijeriya, daga nan ya tafi Jami’ar “Zain University of Technology” da ke birnin Xain a Æ™asar Chaina, inda yake karanta darasin Æ™era jirgin sama wato “Aeronautical Engineering”, yana shekarar Æ™arshe ta kammala jami’ar ya yi Shahada.

Sayyid Hameed ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan Yuli na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra, ya rayu a duniya tsawon shekaru 22 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Ƙudus ta nuna goyon baya ga FalasÉ—inawa a birnin Zariya.

Sayyid Hameed haziÆ™i ne É—an baiwa irin wanÉ—anda ake kira “Genius”. Kafin rasuwarsa an tabbatar da cewa zai iya Æ™era jirgin sama saboda hazaÆ™a. Mutum ne mai tsananin natsuwa da kawaici, ya fi sha’awar rayuwar shiru da kaÉ—aici, yana da Æ™arancin magana, kuma ba ya son hayaniya.

Post a Comment

0 Comments