HUMAID IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Humaid shi ne É—a na Tara kuma É—an auta a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ranar 22 ga watan Yuni na shekarar 2001, kuma ya yi shahada ne ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da Litinin uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437 Hijira. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 14 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya.
Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, sannan ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa. Haziƙi ne mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira, an shaide shi da jarunta da rashin tsoro, ga sakin fuska da girmama na gaba.
0 Comments