Mahmoud Ibrahim

Mahmoud Ibrahim Zakzaky (H)

MAHMOUD IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyid Mahmoud shi ne É—a na Shida a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a makarantarsu É—alibai suna kiransa “Gentle Man”, a gida kuma jama’a suna masa laÆ™abi da “Shehu” saboda natsuwarsa da sauÆ™in kansa da riÆ™o da addini. An haifi Sayyid Mahmud ne ranar 20 ga watan March na shekarar 1995. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kafin ya yi Shahada yana aji uku a jami’ar “Al-Mustapha International University” da ke birnin Beirut na Æ™asar Lebanon.

Sayyid Mahmud ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan July na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 19 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Ƙudus ta nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Zariya.

Sayyid Mahmud mutum ne Æ™wararre a fagen ilimin kwanfuta da sadarwar zamani, haziÆ™i ne mai tawali’u da tsananin riÆ™o da addini, ya fi sha’awar karatun addini fiye da na zamani. An shaide shi da sauÆ™in kai da kyawun hali da kyawawan É—abi’u da yawan ibada. An yi hasashen da ya rayu, da shi zai gaji Shaikh Zakzaky (H) a fagen ilimin addini mai zurfi.

Post a Comment

0 Comments