BABI NA BIYU
BAIWA DA DABI’UN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)
HAZAƘARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tun tasowarsa a yarinta fasihi ne haziÆ™i, Allah ya wadata shi da hazaÆ™a da fasaha, domin duk a cikin ‘ya’yan mahaifinsu ya fi su hazaÆ™a. Malam Badamasi YaÆ™ubu shi ne Æ™anin da ke bin Shaikh Zakzaky, ya faÉ—i a wata hirarsa da ‘yan jarida cewa; “Malam ya taso da son karatu, kuma lalle kam duk a cikin ‘ya’yan mahaifinmu ba haziÆ™i kamarsa, domin zan iya tunawa, yana da yayye kamar guda biyu maza, akwai Malam AbdulÆ™adir YaÆ™ubu, akwai Malam Sani YaÆ™ubu, lalle akan gaya musu karatu su manta, mahaifinmu yakan koyar da su karatu su manta, shi Malam bai kai inda suke ba, amma idan sun manta (karatun) shi suke tambaya ya tuna musu… kuma ya iya karatun boko ba tare da ya yi firamare ba, sannan kuma duk wani littafi da ake yi a (karatun) zaure, lallai Malam ya yi shi” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 63).
Wani lokaci mun kai wa Shaikh Zakzaky (H) ziyara, yana mana hira cikin raha, sai magana ta biyo ta kan yaranta, sai yake cewa: “Lallai ni ina tuna abubuwan da na yi lokacin ina É—an shekara huÉ—u zuwa biyar da haihuwa, nakan tuna abubuwa da dama”. A raina sai na ce “Ku kenan masu ‘Extra Ordinary’ ƘwaÆ™walwa, amma mu kam ai sai a hankali!.
A wani jawabi Sayyid Badamasi YaÆ™ub ya faÉ—i cewa; “Wani lokaci in ana hirar yarinta, Malam (H) yakan ce mun a lokacin da aka haifeka kaza da kaza ya faru, wato, yana bada labarin wasu abubuwan da suka faru a lokacin da aka haife ni, wanda ya gani da idonsa, alhali tsakani na da shi shekara uku ne kacal”.
Tabbataccen abu ne cewa, kaifin Æ™waÆ™walwa da hazaÆ™ar Shaikh Zakzaky (H) ba su misaltuwa, domin a wani jawabi da ya yi wa Æ™ananan yara a taron IVC na shekarar 2013 a Darur-Rahma, ya faÉ—a musu cewa; “Lokacin da ina yaro É—an shekaru goma sha, Æ™waÆ™walwa ta kamar mayen Æ™arfe take game da É—aukar karatu. Na yi Æ™idaya a Kano a 1973 a (Æ™aramar hukumar) Fagge ta kudu, ta kai ma da a ce wani abu zai samu takardun (su É“ace), to, duk mutanen unguwar zan iya rubuta su da sunayensu da shekarunsu!” (Al-Mizan, bugu na 1093, shafi na 18).
Ba shakka wannan bayani zai haska mana waye Shaikh Ibraheem Zakzaky a ƙwaƙwalwa da fasaha da hazaƙa da zalaƙa, domin duk wanda zai iya haddace sunayen ɗaruruwan mutanen unguwa, da yawan shekarun kowannensu, da lambar gidajensu, da kalar addininsu a lokaci guda, to ba shakka zalaƙa da fasaha da hazaƙarsa ta kai maƙura!
Haka nan, sakamakon da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu a kammala digiri É—insa a shekarar 1979, har zuwa wannan shekara ta 2016 ba a samu É—alibin da ya samu irin wannan sakamako a darasin “Economics” a jami’ar Ahmadu Bello ba. MagayaÆ™in Zazzau Alhaji Abubakar Jibrin ya ce; “Muna da labarin cewa a jami’a sakamakon digiri É—insa ya yi kyau sosai! Domin ya samu “1st –Class” (daraja ta É—aya) ne akan sanin tattalin arziÆ™i (Economics), wanda kusan shi ne mutum na Æ™arshe da ya taÉ“a samun irin wannan takardar digiri É—in. Domin an ce tun daga kansa ba a Æ™ara samun É—alibin da ya samu sakamako irin nasa ba har zuwa yau (2016) a wannan jami’a (ta Ahmadu Bello da ke Zariya)”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 82).
HazaÆ™ar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) baiwa ce daga Allah, amma wannan baiwar tasa ta É—anfaru da naci na son sanin komai a haÆ™iÆ™arsa. Madaucin Zazzau Alhaji Ahmad Shehu, wanda tare suka yi yarinta da Shaikh Zakzaky (H) yana cewa; “Malam Ibraheem a cikinmu ya banbanta a tsakaninmu, tunda shi ya taso ne da neman ilimi da kuma neman sanin tarihin kowane abu da sanin asalinsa!... Malam shi mai son yin nazari ne akan kowane abu, don duk abin da bai san shi ba, in dai yana da alheri, za ka ga ya nemi iliminsa, sannan ya yi nazari akansa” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 80).
Malam AbdulÆ™adir YaÆ™ubu, wanda shi ne babban wa ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cewa; “Muna masu alfahari da wannan Æ™ane namu, ya kasance wanda ya fara haddace AlÆ™ur’ani a zuri’armu tun bayan kakanmu Malam Aliyu, shi ya cikata addu’a da babban burin da kakanmu ya mutu da shi”. (Mujallar Gwagwarmaya, fitowa ta 3, shafi na 24).
Wani abu da zai Æ™ara nuna hazaÆ™ar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne yadda ya iya haddace AlÆ™ur’ani da Æ™ira’o’i biyu, wato bayan ya haddace AlÆ™ur’ani da Æ™ira’ar ‘Hafs’, sai kuma ya sake dawowa ya haddace shi da Æ™ira’ar ‘Warshu’. Wannan ba Æ™aramar baiwa bace, marubucin littafin ‘Malam, Malam ne’ yana cewa; “Malam hafizi ne na AlÆ™ur’ani, kuma Alaramma ne, don kuwa da hannunsa ya rubuta AlÆ™ur’ani a lokacin da ya zauna a kurkukun Fatakwal na farko daga 1986 zuwa 89”. (Malam, Malam Ne, shafi na 11).
Da marubucin littafin “Mujaddadin Wannan Ƙarnin” ke magana game da hazaÆ™ar Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Malam (H) bai taÉ“a shiga aji ya koyi “Computer” ba, amma ya san “Computer” fiye da wanda ya shekara biyar yana karanta ta. Kuma duk wani fanni na ilimin zamani in Malam (H) yana magana akai sai ka rantse da Allah a kansa ne ya yi digiri, saboda kawai yadda ya san fannin!” (Mujaddadin Wannan Ƙarnin, shafi na 49).
FIKIRARSA:
Marubucin littafin “Tarihin Harkar Musulunci” yana cewa; “Duk wanda ka gani, to zantukansa da ayyukansa da kuma É—abi’unsa sakamakon fikirarsa ne, wato tunaninsa. Ashe kenan fikira sahihiya kuma salimiya, wadda ta yi daidai da koyarwar addinin musulunci tana da gayar muhimmanci ga mutum, tunda zantukansa da ayyukansa sakamakonta ne”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 25).
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wani bawa ne da Allah ya keÉ“e shi da wata irin baiwa ta sahihiyar fikira ta musamman, duk wanda ya nazarci rayuwar Shaikh Zakzaky (H) zai tabbatar da cewa bawa ne da Allah ya azurta shi da salimiyar fikira da ingantaccen tunani, domin ba ya tufÆ™a da warwara a cikin zantuka da ayyukansa, kullum akan tafarki É—aya yake tafiya. Sau da yawa wasu abubuwa kan bijiro bagatatan ba zato ba tsammani, jama’a su ruÉ—e kowa yana neman mafita, amma shi sam baya ruÉ—ewa, duk abin da ya bijiro, to Shaikh yana da ingantaccen tunani akansa, kuma yana da Æ™waƙƙwarar mafita a game da shi.
A shekarar 1990 lokacin yaÆ™in Tekun Fasha tsakanin IraÆ™i da Amurka, kan al’ummar Nijeriya ya rabu gida biyu, suna ganin yaÆ™i ne tsakanin Musulunci da kafirci, dan haka suka saÉ“a kan waye mai gaskiya tsakanin shugaban Amurka Gorge Bush da kuma shugaban IraÆ™i Saddam Hussain. Wannan ya jawo É“araka a tsakanin musulmi ya su-ya su, wanda har ya kai Æ™ungiyar Izala ta rabu kashi biyu, masu goyon bayan Amurka, da kuma masu goyon bayan Saddam Hussain.
Adaidai lokacin da ake wannan ruÉ—ani, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fito fili ya yi wa al’ummar musulmi bayani cewa wannan yaÆ™i bai da wata alaÆ™a da Musulunci, kawai saÉ“ani ne aka samu tsakanin karen farauta da ubangidansa, faÉ—a ne na kare muradi da kuma Æ™oÆ™arin cimma wani muradin, ba faÉ—a ne tsakanin musulunci da kafirci ba. Wannan abu ya jawowa Shaikh Zakzaky (H) hujumi daga malamai, amma daga Æ™arshe bayan kammala yaÆ™in sai jama’a suka gano lallai matsayar da Shaikh Zakzaky ya É—auka ita ce gaskiya!
Haka nan a shekara 1999, bayan kafa mulkin farar hula a Nijeriya, gwamnonin wasu jihohi na Nijeriya Æ™arÆ™ashin jagorancin gwamnan Zamfara Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura, sun Æ™irÆ™iro batun Shari’a, inda suka ce za su riÆ™a hukunci da AlÆ™ur’ani maimakon hukunci da Kwansitushin a jihohinsu. Wannan ya ja hankalin É—imbin al’ummar Nijeriya, musulmi suka fito Æ™wansu da Æ™warÆ™wata suka nuna goyon bayansu kan hukunci da AlÆ™ur’ani, su kuma Kiristoci suka ja daga a gefe guda suka ce ba su yarda ba.
A tsakanin wannan hayaniya, Shaikh Zakzaky (H) ya fito ya yi wa al’ummar Nijeriya jawabi, ya nuna musu cewa sam ba ta hanyar siyasa ake kafa gwamnatin musulunci ba, shari’a da AlÆ™ur’ani yana da matakai da marhalolin da ake bi kafin a samar da shi, dole sai an bi sunnar Manzon Allah (S) kafin a samar da duk wata gwamnatin musulunci a kowane zamani. Ya ce wannan siyasa ce kawai ta yaudarar mutane da É—auke hankalinsu daga abin da ya kamata a yi musu na kyautata rayuwa da samar da cigaba, domin Shari’a a Æ™arÆ™ashin tsarin kafirci mai cikakken iko, abu ne da ba zai taÉ“a yiwuwa ba!
Nan da nan malamai suka yi masa caa suna sukarsa da aibata matsayarsa, amma bayan shekara É—aya kacal da Æ™addamar da Shari’ar, sai mutane suka gane cewa ashe lallai an yaudare su ne an wawaitar da Æ™waÆ™walen su, ba wata shari’ar musulunci da ake yi a jihohin sai shegantakar ‘yan siyasa kawai. Daga baya wasunsu suka gaskata Shaikh Zakzaky (H) suka jinjinawa matsayarsa da zurfin fikirar da Allah ya yi masa.
A lokacin da Amurka ta kai hari kan tagwayen benayen cibiyar kasuwanci ta duniya (World Trade Center), da cibiyar tsaro ta Pentagon a 2001, da yake kafafen yaÉ—a labarai sun É—ora alhakin harin kan wasu musulmi Æ™arÆ™ashin Usama bin Ladin, al’ummar musulmin duniya musamman Nijeriya sun yi tsalle suna murna da farin ciki, malaman addini musamman Wahabiyawa suka rinÆ™a kwatanta aikin a matsayin babban jihadin addini, suka rinÆ™a yabawa Usama tare da nuna goyon baya da jinjina a gare shi.
Amma ta É“angaren Shaikh Zakzaky (H) tun washegarin ranar da abin ya faru, wasu sashen almajiransa suka kira shi a waya don jin matsayinsa game da abin da ya faru, nan take ya ce masu; Ai kar ku ruÉ—u da wannan abin, wani makirci ne na yaÆ™i da musulmi da Musulunci Amurka da Isra’ila suka kitsa! Shiryayyen shiri ne na yaÆ™i da addini, su suka kitsa harin, ba wani wanda ya kai musu hari!”. Wannan ya nuna yadda Allah Ta’ala ya kimsa shiriya a fikirar Shaikh Zakzaky (H), ta yadda ba a ruÉ—arsa balle a wawitar da Æ™waÆ™walwarsa.
Haka nan, a shekarar 2009, ba zato ba tsammani, sai ga wani makirci na Æ™oÆ™arin rage yawan musulmin Nijeriya ta hanyar kisa. Kwatsam wata Æ™ungiyar ta’addanci da ta kira kanta da suna “Ahlis-Sunnah Lidda’awati Wal-Jihad” wacce aka fi sani da “Boko Haram” ta bayyana, wai manufar Æ™ungiyar shi ne kafa gwamnatin musulunci. Amma maimakon Æ™ungiyar ta yi jahadin kawar da gwamnatin zalunci ta Nijeriya, sai kawai ta É“uge da ayyana arewacin Nijeriya inda musulmi ne tsantsa a matsayin cibiyar jihadinta !
Kuma a jihadin ta’addanci da ‘yan Æ™ungiyar ke yi, suna kashe kowa da kowa ne, suna kashe manya da yara, maza da mata, jarirai da marassa lafiya, suna kashe dabbobi da lalata gonaki da Æ™one duk garin da suka kama Æ™urmus! Suna kai hare-haren Bom a masallatan Juma’a da na “Khamsu-Salawat” adaidai lokacin da ake Sallah, su kashe duk masallatan. Suna kai hare-haren Bom da na kisan gilla a kasuwanni, da asibitoci, da tashoshin mota, da wuraren cin abinci, da wuraren bukukuwa, da gidajen Sinima, da wuraren Æ™wallon Æ™afa, da gidajen mai, da bankuna, da duk inda mutane ke taruwa, kuma a dukkan hare-haren da suke kaiwa sama da kashi 90 na mutanen da suke kashewa musulmi ne, amma wai jihadin Musulunci suke yi!
An ruÉ—i mutanen Nijeriya cewa da gaske wata Æ™ungiyar musulmi ta “Ahlis-Sunnah” ce ke yin wannan aika-aika, kuma jama’a duk sun yarda. Amma sai ga Shaikh Zakzaky (H) ya fito fili ya yi wa mutane jawabi, inda ya ce “Boko Haram” Æ™arya ce! Dirama ce kawai jami’an tsaron Nijeriya da haÉ—in guiwar CIA da MOSSAD na Isra’ila suka shirya don shafe al’ummar musulmin Nijeriya daga samuwa, da mallake kafofin arziÆ™in Nijeriya, da kuma É“ata musulunci a idon duniya, ba ruwan musulunci da wannan aikin, aiki ne kawai na ‘yan mulkin mallaka da masu shan jinin raunana!
Shaikh Zakzaky (H) ya ambaci misalai da shaidu masu yawa da ke tabbatar da cewa “Boko Haram” shiri ne tsararre na kafircin duniya da ke samun goyon bayan gwamnatin Nijeriya, wannan ya sa É—imbin al’ummar Nijeriya sun farka daga mayen da aka sa Æ™waÆ™walen su a ciki, suka gane cewa “Boko Haram” Æ™arya ce, wani makirci ne kawai na zaluntar musulmi da sabon salon mulkin mallaka.
Wannan misali ne kawai na irin baiwa ta ingantacciyar fikira da Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Zakzaky (H), ta yadda shi ba ya ruÉ—uwa da ruÉ—in masu ruÉ—i, ba a iya yaudarar tunaninsa ko cusa masa wahami, ba a iya wawitar da fikirarsa ko a gina shi akan holoÆ™o. A wata magana tasa yana cewa, bisa baiwa ta Allah Ta’ala gare shi, tunda yake bai taÉ“a samun matsalar fikira ba, ya ce; “Wannan fikira ba wai wani Æ™oÆ™ari ba ne, ko ilimi ko jarunta ko kuma dabara ba, a’a, baiwa ce daga Allah Ta’ala wacce ya yi mana”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 25).
Marigayi Dakta Kalim SiddiÆ™y (shugaban majalisar musulmin Birtaniya) ya taÉ“a cewa; “Bai taÉ“a haÉ—uwa da mutumin da cikin ‘yan mintoci zai gaya maka manufarsa, kuma ka fahimce shi, kamar Shaikh Ibraheem Zakzaky ba”. (Malam, Malam Ne, shafi na 30).
TSABTARSA:
Duk wanda ya san Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya san shi da tsananin tsabta da Æ™in Æ™azanta da datti. Mutum ne da tsabta ta zamo É—abi’a tamkar jinin jikinsa, duk inda yake rayuwa za ka ga wuri ne gyararre mai tsafta da ban sha’awa, hasali ma Shaikh Zakzaky (H) ne ya raya É—abi’ar ado da kwalliya da Fulawa a cikin al’ummar Hausawa, domin akan yi ado da fulawa a motarsa, da wuraren wa’azozinsa, da wuraren zamansa, da ma ko’ina a cikin gidansa. Kuma Shaikh Zakzaky mutum ne da ke tsananin adawa da wari ko Æ™arni ko duk wani abin da ba Æ™amshi ba.
Shaikh Muhammad Turi (RA) ya labarta tsananin tsaftar Shaikh Zakzaky a wata hirarsa da ‘yan jarida, ya ce, bayan an kama su tare da Shaikh Zakzaky a lokacin mulkin Abacha, sai aka kai su kurkukun Kaduna, aka sa su a wani waje mummuna mai matuÆ™ar Æ™azanta; “Wurin ga shi da Æ™azanta Æ™warai da gaske, sam wurin ba shi da kyawu, wurin shi ne mafi muni (a cikin kurkukun), sai mutum ya yi (babban) laifi a cikin kurkukun ne za a kulle shi a wurin… nan da nan Malam ya tura waje aka zo da farin fenti (aka fente wurin baki É—aya), aka zo da fulawowi da sauransu, wurin babu ko wutar lantarki, aka jawo wuta, nan take dai aka gyara wuri, sai ga shi ya fito fes-fes.
“Ina iya tunawa, wata rana (ko Konturola Janar ne) ya kawo ziyara kurkukun, yana shigowa wurin, sai ya cika da mamaki, ya ce; “Ah, wurin nan kamar za a kawo Amarya!” Saboda shi ya san wurin a baya can, shadda ne kawai za a iya cewa wurin, amma sai ya ga yanzu an yi fenti har da Fulawowi da sauran kayan Æ™awata wuri, nan fa ya jima yana cike da mamaki, to shi ne sai Malam yake cewa; “Shi wannan bai san akwai mutanen da idan aka sanya su a shadda, shaddar nan sai ta yi Æ™amshi ba?”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 100).
“Ka duba ka ga yadda Malam ya gyara inda ya zauna a gidan yarin Kaduna, ya yi fenti a wurin, ya shuka filawa, ya ja wutar lantarki, har wadoji na cewa wurin ‘Presidencial Villa’ wato “Fadar Shugaban Ƙasa”. (Malam, Malam Ne, shafi na 11).
Rayuwar Shaikh Zakzaky (H) gaba É—ayanta cike take da Æ™amshi da tsafta, É—akinsa Æ™amshi, falonsa Æ™amshi, gidansa Æ™amshi, motarsa Æ™amshi, duk inda zai zauna sai an Æ™amsashe shi. A duk sa’adda ya yi “Brush” sai ya yi anfani da “Mouth Freshner”. Komai nasa mai Æ™amshi kuma tsaf-tsaf gwanin ban sha’awa, sam ba ya son wari da datti da rashin tsafta.
“Malam mutum ne mai yawan anfani da turare, don Malam ko wucewa ya yi ta wuri za ka sani saboda Æ™amshin turarensa, balle a ce wani abin da ya fito daga hannunsa, Æ™amshi za ka ji yana yi, duk abin da ya taÉ“a sai ya yi Æ™amshi. Wata rana matata, Malama Zeenat ta sa ta zubar da ‘Dustbin’ (shara) na É—akin Malam, to wallahi Æ™amshi (sharar) take yi!”. (Malam, Malam Ne, shafi na 10).
Mai karatu ka ji fa! Sharar É—akin Shaikh (H) ma Æ™amshi take yi! Editan jaridar Almizan Malam Ibrahim Musa ya ce; Shaikh (H) ya taÉ“a bani kyautar rediyo Æ™arama ta É—aukar magana, rediyon ta daÉ—e a wurina tana Æ™amshi”. Wannan misali ne kawai na tsabtar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H).
TAWALI’UNSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) fitacce ne a fagen Tawali’u da Æ™anÆ™antar da kai, sam ba a shaide shi da girman kai ko jiji da kai ba, sai wanda ya kusance shi ne zai iya sanin zurfin tawali’unsa. Misali, duk wanda ke zuwa gidan Shaikh Zakzaky (H) a Gyallesu zaman yamma, ya san cewa Shaikh É—in ne da kansa ke zubawa mahalarta zaman Shayi a kofuna a mimmiÆ™a musu su sha, kuma wannan ya zama É—abi’arsa.
Shaikh Muhammad Turi (RA) yana cewa; “(A zaman da muka yi tare da Shaikh Zakzaky a kurkukun Kaduna), duk lokacin da aka kawo abinci, shi Malam ne ke raba mana abincin. Ba ni mantawa, akwai wani shugaban Wadoji a nan kurkuku É—in, wata rana ya shigo haka kwatsam, a daidai lokacin Malam yana rabon abinci, sai ya yi ta mamaki, har yana cewa “Leadership by Example”, yana ta mamaki...
“Kuma wata rana a lokacin irin tarukan makon haÉ—in kan nan, akwai wani malami daga cikin waÉ—anda aka gayyata ya zo, a irin lokacin cin abincin nan, sai ya ga Malam shi da kansa yake É—iban nasa abincin yana zubawa a kwanon da zai ci, sai shi malamin yana ta mamaki, har yake cewa; “Ah, ya za ku bari Malam yana É—iban abinci da kansa, ba za ku amsa ku zuba masa ba? Haka nan, wata rana mun yi tafiya a cikin dare a wata jar mota, lokacin ina ga ‘Bluebird’ ce, sai muka kafe, sai duk muka sassauko domin mu tura motar, kafin mu ankara, ashe har malam ya sauko ana tura motar tare da shi”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 101).
Daga cikin
A wani misali na tawali’un Shaikh Zakzaky (H), Malam YaÆ™ubu Yahya yana cewa; “Akwai wani wuri da ake ce ma Zawiyya (a gefen gidan Malam), Malam yakan É—an sauÆ™ar da baÆ™i a wurin, ni ma ina daga cikin baÆ™in da ake sauÆ™arwa. To, akwai wani zuwa da na yi, Malam da kansa ya shinfiÉ—a mani Katifa, ya É—auko zanin gado ya sanya mani, ya kukkunna mani fitila, abin ya ba ni mamaki! Haka kuma in na yi bankwana zan tafi, sai Malam ya yi mani rakiya, sai in ji kamar in nutse Æ™asa (saboda jin nauyi)”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 112).
A wata hira da jaridar Al-Mizan, É—aya daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H) Malam Dawud Aliyu ya ambaci wani misali na Tawali’un Shaikh É—in, ya ce; “Zan iya tunawa, akwai wani lokaci, tun Malam yana Kwarbai, na zo na sami Malam (H) ya fito, akwai wani gida da yake tafiya can wajen yana yin abubuwa na karance-karance da wasu hidimomi, Malam ya É—auke ni a mota muka tafi wancan gidan, muka je muka shiga, akwai kayansa da ya jiÆ™a zai yi wanki, na nemi in karÉ“a in wanke masa, amma ya hana ni, da kansa ya wanke kayansa ya shanya”. (Shekaru 60 masu Albarka, shafi na 158).
Wani tsohon hadimin Shaikh Zakzaky (H) mai suna Abdullahi Manu, ya faÉ—i cewa tun asali Shaikh Zakzaky (H) da kansa yake wanke tufafinsa, ba ya bari wani ya wanke masa; “A bisa al’adarsa, yakan jiÆ™a wanki a bokiti tun safe, sai da yamma sai ya wanke, to in ya jiÆ™a ya fita sai in wanke in shanya masa kafin ya dawo, sai ya yi mun magana cewa ba buÆ™atar hakan, to amma ni sai na kasa bari. Washegari da ya jiÆ™a sai na sake wankewa na shanya, da ya dawo ya gani sai bai ce komai ba, bayan kwana biyu da wankin ya sake taruwa, da ya jiÆ™a sai ya É—au bokitin ya shigar da shi cikin falonsa ya kulle, ala tilas na haÆ™ura ina gani yana wankinsa da kansa, a garin wannan wankin da yake yi ne ma ya taÉ“a samun hatsari da bokiti har ya karye a hannu”.
Shi ma Malam Nuraddeen Aliyu AlÆ™aleri (É—aya daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky) ya labarta mana cewa; “A lokacin da Shaikh ke zaune a unguwar Kwarbai a Zariya, na taÉ“a zuwa na same shi yana É—ibar ruwa a bokiti daga Zawiyya yana kaiwa gidansa, sai na je zan karÉ“a, na yi na yi in karÉ“a amma ya hana ni, ya ce; “Ba damuwa, na gode!”, ya ci gaba da É—iban ruwansa da kansa”.
Shaikh Zakzaky (H) yana ban ruwa ga filawowin gidansa da kansa, kuma yana bawa tsuntsayen gidansa abinci da kansa, kamar yadda yake shara da dafa abinci ga iyalinsa. Tabbataccen abu ne cewa zurfin tawali’un Shaikh (H) ya kai ga yana yin aikace-aikacen da suka shafe shi ne da kansa, kama daga wanki, É—iban ruwa, shara, renon yara, har ma da dafa abinci. Wannan yana nuna sauÆ™in kai da Æ™anÆ™antar da kai irin na Shaikh (H).
ZUHUDUNSA:
Kamar yadda yake Æ™a’ida cewa, duk wani Malami na Allah ba a rasa shi da zuhudu (wato gudun duniya, ko É—aukar duniya ba a bakin komai ba), to shi ma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) haka yake, zahidi ne da dukkan ma’anar zuhudu, domin dukkan É—abi’unsa na zuhudu ne, tattare da irin yanayi na Æ™asa da al’ummar da yake rayuwa a cikinta.
Ga wanda ya san haÆ™iÆ™anin rayuwar da Shaikh Zakzaky ke yi, ya san cewa bawan Allah ne mai zuhudu, ga abin da É—aya daga cikin manyan É—alibansa ke cewa; “La’alla za ku ga Malam haje-haje da shaddodi, ga mota Marsandi (ko Jif), sai mutum ya zaci ko Malam baida zuhudu, ka tambayi na kusa da shi ka ji, sai a kwana uku ko huÉ—u ba a hura wutar dafa abinci a gidan Malam ba, ba a samu abin da aka É—an taÉ“a ba, ba kuma za ka gane ba, kuma har yanzu ma maganar nan da muke yi wani lokaci haka ne!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).
ÆŠaya daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H) ya taÉ“a labarta cewa; “Wata rana ya samu Rogo, sai ya ga ya kamata ya kai gidan Malam, da ya kai Rogon sai Malam yake cewa; “Allah ya saka da alkairi, yau kwana uku kenan gidan nan ba wani motsi”. (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).
“Kuma sau É—aya yake cin abinci a rana, wannan ko ka yarda ko kar ka yarda haka ne, musamman ma mafi yawancin lokuta ranar Juma’a, sai wajan Æ™arfe uku sannan ya karya kuma sai gobe, in kuma tafiya za a yi, za a tafi tunda safe kamar Æ™arfe shida, to ko ma ina ne za a, Malam ba ya karyawa sai an je wannan garin, ko za a kai faÉ—uwar rana ne!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).
Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Malam shi ko abinci bai dame shi ba, don sau da yawa Malam a gida yakan yi wasu kwanaki bai ci abinci ba. Na san wata rana za mu je Maulidi da daddare, sai ya ce; “Ku É—an jira ni in jefa wasu ‘yan lomomi, saboda rabo na da abinci tun shekaran jiya”. (Malam, Malam Ne, shafi na 15).
“Sannan Malam a gidansa a É—akinsa ba ya da katifar da yake kwanciya, ba kuma don bai da kuÉ—in da zai saya ba ne, amma dai shi ba ya zo kwanciya (a duniya) ba ne!”. (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).
Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Malam Zahidi ne mai gudun duniya, ba ka bi na bashin rantsuwa, amma Wallahi! Malam bai da ko katifa a É—akinsa na kwana balle Gado! A Æ™asa yake kwana. Da ya je ziyara wata jaha a arewa maso yamma, sai Gwamna ya je masaukin Malam da sassafe don ziyara, da gwamna ya shiga É—akin da Malam ke kwance, sai ya tarar da shi kwance a Æ™asa, wannan abu ya yi wa gwamna tasiri ba kaÉ—an ba, shi ganau ne ba jiyau ba, ya ce; “Wannan irin sauÆ™in kai haka!”. (Malam, Malam Ne, shafi na 28).
“Wani mai kuÉ—i ya yi wa Shaikh Zakzaky (H) tayin gina masa gida mai kyau, sai Shaikh ya ce shi ba ya fatan ya bar komai (na duniya) wanda wani É—ansa zai gada. Fulotin da É—an uwan ya ba shi ma, sai ya ce ba nasa ba ne, na al’umma ne, ko ya mutu ‘ya’yansa ba su da gado akai, to, ka ga ni fa!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 11).
Akwai lokacin da a wani jawabi (Shaikh Zakzaky) yake cewa; “Duk wanda ya fuskantar da zuciyarsa ga Allah Ta’ala, zai ga komai (na duniya) wulaÆ™antacce ne, zai ga sutura wulaÆ™antatta ce, zai ga komai a wulaÆ™ance, kai, duniya baki É—aya ba za ta kai darajar fuffuken Æ™uda a wajensa ba”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 32).
“(Shugaban Æ™asa na mulkin soja), Janar Ibrahim Babangida, ya shahara da rufe bakin Malamai da kuÉ—in rashawa, watarana sai ya tura wa Shaikh Zakzaky (H) saÆ™on magudan kuÉ—i, amma sai Shaikh (H) ya yi musu gatse irin yadda Annabawa da Mujaddadai suke wa ÆŠagutai. Ya dubi kuÉ—in ya cewa wanda ya kawo saÆ™on; “Ai kuÉ—in ba su kai yadda suka ambata ba”, wanda ya kawo saÆ™on jiki na rawa ya ce; “Wallahi Malam ba a taÉ“a komai a ciki ba”, sai Shaikh (H) ya ce; “Na duba ne ban ga Aljannar Allah a cikin abin da ka kawo ba”. Nan take É—an saÆ™o ya gane abin da Shaikh (H) ke nufi, sai ya ce; “Allah gafarta Malam, wannan kam babu”, sai Shaikh (H) ya ce; “To, a maida masa abinsa tunda babu Rahamar Allah a ciki, dama ni ita nake nema”.
ÆŠan saÆ™o ya kwashi saÆ™on Ubangidansa cikin kunya da Æ™asÆ™anci, yana tambayar kansa ashe akwai Malamin da zai Æ™i kuÉ—i irin wannan?”. (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1256, shafi na 21.).
Wani abu da zai Æ™ara nuna mana zuhudu da tsantseni na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne; wata rana ya yi tafiya zuwa wata Æ™asar waje, bayan ya kammala abin da ya kai shi, da zai dawo gida sai ya je Æ™aton shagon sayayyar kayayyaki na komai da ruwanka, wato “Super Market” don siyo tsaraba da sauran kayayyakin da yake buÆ™ata. Ashe lokacin da ya shiga “Super Market” É—in wani daga cikin almajiransa na Æ™asar ya gan shi, sai almajirin nasa ya zaga wajen mai karÉ“ar kuÉ—i na “Super Market” É—in wato “Cashier” ya ba shi katin cirar kuÉ—i na ATM É—insa, ya ce masa “Duk abin da Malamin can ya É—auka, ku yi lissafi ka cire a akawunt É—ina, kar ka karÉ“i ko kwabonsa”, sai ya juya ya fita ya tafi don ma kar Shaikh (H) ya ganshi.
Shi kuma mai kula da shagon “Super Market” da yake yana so ya yi babban ciniki, sai ya je ya samu Shaikh Zakzaky (H) ya ce masa; Ya Shaikh, wani mutum ya biya maka kuÉ—in duk abin da za ka É—auka, dan haka ka kwashi duk abin da kake so!” Da Shaikh (H) ya ji haka, sai ya fasa sayan duk abubuwan da ya zo da niyyar saya, ya É—auki abin share zufa “Handkerchief” guda É—aya rak, ya je wajan “Cashier” ya ce; “Ga iyaka abin da nake buÆ™ata!” Mai shago ya ce; “YallaÉ“ai ko ba ka fahimci bayanin da na yi ma ba ne?” Shaikh (H) ya ce masa; “Na fahimta sosai”, sai mai shago ya buÉ—e baki yana kallon Shaikh Zakzaky (H) yana mamaki!
AtaÆ™aice waÉ—annan abubuwa suna nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ya É—auki karikitan duniya a matsayin shirme, tattare da cewa a zahiri yana mu’amala da wasunsu, amma baida “Ta’alluÆ™-Ƙalbiyya” wato É—anfara zuciya garesu.
TAWAKKALINSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai matuÆ™ar tawakkali ga Allah Ta’ala da siÆ™a gare shi, duk wanda ya san zantukansa, to ya san shi da yawan maida al’amarinsa ga Allah. A farkon-farkon Da’awarsa, wani malami ya taÉ“a ce masa wannan Da’awa da yake yi gara ya dena ta ya nemi wani abin yi, domin abin da yake kira a kai na kafa gwamnatin musulunci, abu ne da ba zai taÉ“a yiwuwa ba samsam!
Sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce masa; “To, kana nufin akwai abin da ya gagari Allah ne, wanda shi wannan abin Allah ba zai iya yinsa ba samsam? Da ma ba cewa na yi ni ne zan yi ba, cewa na yi Allah Ta’ala ne zai yi, in kuma akwai abin da ya gagari Allah to ka faÉ—a mani!” wannan amsa tana nuna zurfin siÆ™ar Malam da Allah Ta’ala ne.
Wani abu da zai Æ™ara nuna mana zurfin tawakkalin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da tsananin dogaronsa ga Allah shi ne, a shekarar 2014, lokacin da Jami’an leÆ™en asiri na Nijeriya da haÉ—in gwiwar na Æ™asashen waje suka tsananta É—ane-É—anen tarko na Æ™oÆ™arin kashe shi a hanyarsa ta zuwa Hussainiyya wurin karantarwarsa, sai almajiransa na “Dandalin Ahlid-Duthour” suka zartar da shawarar saya masa motar da harsashi ba ya hudawa (Bullet-Proof) don samun kariya daga harsashin maÆ™iya.
Har sun tuntuɓi kanfanin sayar da motocin a ƙasar Jamus, sun ma yi ciniki sun gama za su biya, sai labari ya iske Shaikh Zakzaky (H) kan wannan yunƙuri da sashen almajiransa ke yi na saya masa motar da harsashi baya hudawa don sama masa kariya.
Sai Shaikh (H) ya ce musu; Lallai yana godiya bisa yunÆ™uri na bada gudunmawarsu ta kariya a gare shi, Allah Ta’ala ya saka musu da alkairi, amma ba buÆ™atar saya masa mota “Bullet-Proof”, domin Allah Ta’ala ne mai kariya kuma yana nan, Insha Allah zai ci gaba da karewa har zuwa wa’adi”. A haka ya rufe wannan batu na saya masa mota “Bullet-Proof”. Babu shakka wannan matsaya ta Shaikh (H) zai nuna mana zurfin tawakkali da tsagwaron dogaronsa ga Allah!
A shekarar 2015 jami’an tsaron Nijeriya da haÉ—in gwiwar na Amurka da Isra’ila sun tsananta É—ana tarko na Æ™oÆ™arin buÉ—ewa Shaikh Zakzaky (H) wuta a hanyarsa ta zuwa zaman makokin Ashura na tsawon kwanaki 50 da yake gabatarwa a “Hussainiyyah BaÆ™iyyatullah” da ke birnin Zariya, don ganin sun kashe shi ko ta halin Æ™aÆ™a.
Sun yi ta É—ana tarko don cimma wannan buri nasu, to amma sai Allah ya yi ta kunyata mummunan shirin nasu, duk lokacin da suka ajiye ‘yan ina da kisa akan hanyarsa, sai ya zo ya wuce ba tare da sun yi la’akari ba. Sai suka Æ™ara yin wani mummunan shiri na musamman, suka tsara ajiye makasa a wurare da dama, ta yadda in ya wuce waÉ—annan to ba zai wuce na gaba da su ba.
Da rahoton hakan ya zo ga Shaikh Zakzaky (H), sai ya yi jawabi ya fallasa shirin nasu, sannan ya tabbatar musu cewa; “Zan ci gaba da zuwa zaman makokin Ashura sai na kai har Æ™arshen watan! Zan nuna muku cewa; AKWAI UBANGIJIN DA KE KARENI! Ba zan taÉ“a fasawa ba! kuma hanyar da nake bi nan zan dunga bi (ba zan canza ba)!” (Yaumus-Shuhada, 1436-2015). Mai karatu, kalli zurfin tawakkalin Shaikh a wannan matsayar!
Haka nan, a lokacin waÆ™i’ar 2015, bayan sojoji sun kashe É—aruruwan almajiran Shaikh Zakzaky (H) da ke ba shi kariya, sun tunkaro gidansa, sai É—ansa Shahid Hammad ya shiga wajansa ya ce masa; “Mun Æ™iyasta cewa nan da awa É—aya sojoji za su shigo cikin gidan nan”. Sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce masa; “Mu wannan ba a hannunmu yake ba, mu abin da ke kanmu shi ne mu dogara ga Allah kawai, ba mu san me zai faru nan gaba ba, namu shi ne mu yi iyakar Æ™oÆ™arin mu, kuma mu dogara ga Allah, amma batun yaushe sojoji za su shigo, ba namu ba ne, saboda haka duk wanda ba ya wani abu musamman na taimakawa, to ya ci gaba da addu’a kawai”.
Zuwa É—an lokaci kaÉ—an sojoji suka iso Æ™ofar gidansa suna kisa ba ji ba gani, sai sashen almajiransa suka shiga wajansa suka nemi ya amince su fita da shi ta baya don tseratar da shi daga mummunan nufin sojojin; sai ya yi murmushi, ya ce “Ai ba batun gudu ko É“uya, su yi iyakar nasu Æ™oÆ™arin, mu kuma mu dogara ga Allah… in Allah ya tsara mutanen nan za su shigo su Æ™arasa mu ne, to shi ne nasararmu, idan kuma ya kasance za su tsaya ne, to haka Allah ya tsara. Mu dai muna neman afuwa ne a wajen Allah, kuma mu yi addu’a da tunanin muna neman afuwa a wajen Allah. Idan Allah ya tsara zai bar mu mu ci gaba da aiki a tafarkinsa, za mu tsaya, idan kuma za mu tafi ne (mu yi Shahada), to hakan ya tsara mana”. (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1240, shafi na 7).
Ana cikin haka, sai wani ya kira shi a waya daga Æ™asar Iran don jin halin da yake ciki, sai ya ce shi yana cikin gidansa bai je ko ina ba, kuma anan zai tsaya ba zai je ko ina ba, Allah ne kawai zai kare shi! “Only Allah Alone Can Deliver me!” Lallai waÉ—annan zantuka na Shaikh Zakzaky (H) suna nuna zurfin tawakkali da maida al’amuransa zuwa ga Allah Ta’ala ne a kowane yanayi.
YAƘINI DA SIƘARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai tsananin yaÆ™ini da siÆ™a ga Allah Ta’ala. Yawancin marubuta da manazarta rayuwar Shaikh Zakzaky (H) suna jinjinawa da Æ™arfafa batu akan zurfin yaÆ™ini da siÆ™arsa ga Allah Ta’ala.
A mafi yawan jawabansa yana tabbatar da cewa ba wanda ya isa ya dakatar da tabbatar addinin musulunci, wato duk da tinÆ™aho da Æ™arfin kafircin duniya, bai isa ya hana kafuwar addinin Allah a wannan zamanin ba, domin a yanzu Allah ya ga damar addini ya É—ago. A wani jawabinsa na “Yaumul-Arba’in” yana cewa; “Su (azzalumai) suna ganin za su iya hana Allah tabbatar da abin da ya so, saboda suna da bindiga sun iya kisa! To da kisa yana hana addini tabbata da tun a Karbala an kashe Musulunci!”
Haka nan, a jawabin “Yaumus-Shuhada” na 2015 yana cewa; Insha Allah kamar addinin nan ya kafu ma daram an gama!” Wato Shaikh Zakzaky (H) sam bai da shakku ko kokwanto akan tabbatuwar addini.
Wani abu ma da zai Æ™ara nuna mana siÆ™ar Shaikh Zakzaky (H) da Allah shi ne; A lokacin waÆ™i’ar Abacha, yana tsare a gidan yari, sai mutanen gidansa suka aika masa cewa, masu gidan haya sun matsa musu cewa su tashi daga gidansu, (wato sun shiga halin da ake cewa halin Lahaula wala Ƙuwata), amma amsar da ya ba su ita ce cewa, “Tunda ku ka ga an matsa mana akan gidan (haya), to insha Allah muna gab da mu soma ba da kyautar gidaje!”. (Malam, Malam Ne, shafi na 06).
Wannan yana nuna siƙar Shaikh (H) da Allah ne, domin a lokacin da ake karanta masa tsanani, ƙunci, matsi, da ƙalubalen da ake ciki, shi kuma yana bushara da albishir na farin cikin da zai biyo bayan ƙuncin ne! Wannan halin sai waliyyan Allah!
YaÆ™inin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai taÆ™aita akan al’amuran yau da kullum kawai ba, a’a, hatta a ibadarsa yana yin ta ne da cikakken yaÆ™ini. A lokacin da gwamnatin Nijeriya ta sa hannu kan wani shirin kashe shi a shekarar 2009. Shaikh Zakzaky (H) ya yi nasiha ga almajiransa a Æ™okarinsa na kwantar da hankalinsu, a ciki yake cewa; “Alhamdulillah! Allah ya yi min wannan baiwar, na san ko mutum ya Æ™i ni, in dai mun yi yarinta (tare), ya san tun ina yaro na taso ina ibada ne, kuma na san yau shekaru 40 cur ina ibada da YAƘINI kamar ina ganin zahiri! Saboda haka tafiya in ta zo ‘Falillahil-Hamd’, an kashe waÉ—anda suka fi ni!”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 176).
Wannan jawabi na Shaikh Zakzaky (H) ya nuna zurfin É—anfaruwarsa da Allah Ta’ala, da irin siÆ™a da yaÆ™ininsa cikin bautar da yake yi, ba mai iya faÉ—in wannan magana in ba salihin bawa ba.
HAƘURI DA JURIYARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne da aka shaide shi da haƙuri da juriya, misalan haƙuri da juriyarsa suna da ɗimbin yawa, amma ataƙaice za mu bada misali guda uku kacal;
A tsawon shekarun Da’awar Shaikh Zakzaky (H), gwamnatin Nijeriya kai tsaye ko a fakaice ta hanun ‘Yan tauri, ‘Yan Banga, zauna gari banza, Sarakunan gargajiya ko ta hannun malaman Fada, sun sha rusa makarantun almajiransa a wurare daban-daban! An sha abkawa a raunata É—imbin almajiransa a garuruwa daban-daban, an sha Æ™ona dukiyoyin mabiyansa ba iyaka a lokuta daban-daban, an sha É—aurewa kuma ana ci gaba da É—aure almajiransa a gidajen kurkuku daban-daban, an kori É—imbin almajiransa a wuraren aikin gwamnati, an kori É—alibai almajiransa daga manyan makarantun da suke karatu, an mayar da dubban ‘ya’yan mabiyansa Marayu, an mayar da dubban mata almajiransa Zawarawa, an mayar da É—imbin masu arziÆ™i a cikin almajiransa faÆ™irai! Amma duk waÉ—annan abubuwa da aka yi masa a tsawon waÉ—annan shekaru kusan 40 bai taÉ“a ramawa ba, bai taÉ“a cewa almajiransa su É—au fansa ba.
A shekarar 2014 sojojin Nijeriya Æ™arÆ™ashin mulkin shugaban Æ™asa Goodluck Jonathan bisa jagorancin Kanar M.S Oku suka kashe haziÆ™an ‘ya’yan Shaikh Zakzaky (H) guda uku, tare da almajiransa guda 30, sun yi hakan ne da nufin su fusata Shaikh Zakzaky (H) su ingiza shi ga yin bore da tada hankali, amma sai Shaikh Zakzaky (H) ya yi bayani cikin natsuwa da mayar da al’amari ga Allah, ya lallashi almajiransa cewa kada kowa ya mayar da martani ko ya yi wani abu da sunan É—aukar fansa.
An ce, a ranar da sojoji suka kashe ‘ya’yansa uku, labarin Shahadar biyu daga cikin yaran ya zo masa ne bayan sallar Isha, kuma adaidai lokacin da ya zauna don yin buÉ—a baki da almajiransa. Ya tsiyayi ruwan shayi zai sha kenan sai wayarsa ta yi Æ™ara, yana É—auka sai aka ji yana cewa “Innalillahi wa Innaa’ilaihi Raji’un!” ya maimaita sau uku.
Bayan ya sauÆ™e wayar sai ya shaidawa almajiransa cewa an Æ™ara kashe ‘ya’yansa biyu Ahmad da Hameed, nan take gun ya kaure da kukan baÆ™in ciki, amma shi Sheikh (H) babu ko É—igon hawaye a idanunsa, ya yi shiru na tsawon lokaci bai motsa ba (alamun yana munajati da Allah), har ya tashi ya shiga gida ba a ga hawaye a fuskarsa ba, duk da tsananin so da Æ™auna da shaÆ™uwar da yi da yaran nasa. Wannan juriya da ya nuna sai da ta zama abin tattaunawa a tsakanin almajiransa.
Shekara É—aya rak bayan haka, wato a shekarar 2015, sai ga bataliyar sojojin Nijeriya Æ™arÆ™ashin Janar Tukur Yusuf Burtai, sun zo Zariya takanas suka aiwatar da mummunan ta’addanci akan Shaikh Zakzaky (H) da iyalansa da al’majiransa, inda suka kashe É—aruruwan almajiransa, suka Æ™ara kashe ‘ya’yansa uku maza, suka kashe yayarsa Goggo Fatimah, suka yi masa ruwan harsashi shi da matarsa Malama Zeenatu, suka Æ™ona gidansa bayan sun harbi gidan da Gurneti, suka rusa masa cibiyon karantarwarsa irin su Hussainiyyah BaÆ™iyatullah, Darur-Rahma, Fudiyyah Islamic Center, da Hubbaren mahaifiyarsa da ke unguwar Jushi.
Sannan suka kama shi suka tafi da shi a mummunan yanayi, amma bayan ya farfaÉ—o ya samu sauÆ™i daga raunukan da suka yi masa, sai ga shi ya aiko gaisuwa da jinjina ga almajiransa da suka dake akan wannan tafarki na gwargwamaya. Kuma ya yi musu Wasiyya cewa su tsaya akan nizamin Harka Islamiyyah, kar a ce za a É—auki fansa, kawai a ci gaba da abin da ake yi da kuma addu’o’in neman sakayyar Ubangiji. Wannan ya nuna yadda Shaikh (H) ke da zurfin haÆ™uri da Æ™arfin juriya ne.
AFUWARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai yawan afuwa da shanye laifi, yana da yawan kauda kai da bada tazara. Duk wanda ya san shi zai iya bada shaida ga yawan afuwarsa, misali; A lokacin fitinar ‘yan Zuhudu, akwai waÉ—anda suka yi (munanan) maganganu ga Shaikh (H), wasu ma suka yi rubutu. To, daga baya wasu sun farga (da kuskurensu), saboda haka sai suka zo wajen Shaikh (H) domin ya yi musu afuwa, sai ya yafe musu, shi ne ma lokacin da ya zo jawabin rufe Ijtima ya yi magana, a ciki yake cewa; Duk wanda ya san ya ce wani abu gare shi, ba sai ma ya zo ya ce ya yafe masa ba, shi ya yafe masa!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 30).
Haka nan, wasu daga cikin almajiransa sun É“alle masa a shekarar 1993, suka yi masa tawaye, suka riÆ™a sukarsa da aibata shi da yi masa Æ™azafi da sharri iri-iri, amma da ya zo jawabinsa na cikar Harkar Islamiyyah shekaru 25 da kafuwa, sai ya ce; “Ina ‘yan Tawayiyya ku dawo! Duk wanda ya fita (daga cikin Harka Islamiyyah) to muna kiransa ya dawo, Æ™ofar da ya gani a wangale ya fita, to yanzu ma tana buÉ—e a wangale ya dawo, in dai ni ne (game da Æ™azafofi da cutarwar da kuka yi mani) na yafe!”
“Ka duba ka ga ‘yan Tawayiyya yadda suka cutar da Malam, kai sun yi niyyar kashe shi ma a masallacin Juma’a na Jami’ar Bayero da ke Kano, to amma Malam da me ya saka musu? Lokacin da ya je aikin Hajji, addu’a ya yi musu a Ka’aba, ya ce, “Ya Allah in waÉ—annan suna da rabo a lahira, to ka dawo da su mu ci gaba da abin da muke yi tare, kuma ni na yafe musu duk abin da suka yi mini”. (Malam, Malam Ne, shafi na 16).
Haka nan, a wajajen shekarar 2010, an kawo wa Shaikh Zakzaky (H) muryar da aka naÉ—a ta wani mutum da yake nuna yana tare da shi, amma a gefe kuma yake sukarsa yana aibata shi, yana faÉ—in munanan maganganu akansa. Bayan Shaikh ya ji maganganun sai bai ce komai akai ba, ya kauda kai daga abin. Sai sashen almajiransa da ke tare da mutumin suka nuna rashin amincewarsu ga abin da mutumin ya yi, aka soma samun rashin jituwa a tsakaninsu har dai batun ya zo gabansa.
A jawabin da ya yi wa almajiran nasa ya nuna musu cewa, wannan abin da mutumin ya yi ba komai ba ne, “Na so a ce ni kaÉ—ai na ji waÉ—annan maganganu da mutumin ya yi a kaina, da ba wanda zai san an yi su! Zan É—aga Æ™asan filona ne kawai in jefa kaset É—in, ba wanda zai ji labari balle a samu rigima, domin ba shi kaÉ—ai ne ke irin wannan maganganu ba, suna da yawa, muna da labarinsu, amma ba mu taÉ“a cewa komai a kansu ba, mun kauda kai daga garesu, ba za su cutar da mu da komai ba, kowa yana aiki ne don kansa”. Wannan jawabi na Shaikh Zakzaky (H) yana nuna mana zurfin kauda kansa ga al’amura.
Sau da yawa in aka yi anfani da wasu wawayen mutanen gari suka abkawa ‘yan uwa, ko suka lalata dukiyar ‘yan uwa, sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce, “In ba don tausayi ba, da sai mu yi musu addu’a” amma don gudun lalacewa da asarar lahirarsu, Shaikh (H) ba zai musu addu’a É—in ba, sai dai ya yi akan azzaluman da ke ingizo su.
A shekarar 2011 wani É—an jarida ya tambayi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ko ya yake ganin mutanen da suka cutar da shi ta hanyoyi daban-daban?
Sai Shaikh (H) ya ce: “Ni ina ganin (waÉ—anda suka zalunce ni a matsayin) su mutane ne da sam ba su son canji, suna ganin hakan zai shafe su, mu a namu gefe muna Æ™oÆ™arin jawo hankalinsu, amma su kuma suna son murÆ™ushe mu (su kashe mu)… wannan shi ne tunaninsu, a ce ba mu nan, mu kuma a gefe guda ba mu fatan É—aya a cikinsu ya mutu, mun fi son su rayu, su fahimci abin da muke Æ™ira akai, muna so mu jawo ra’ayinsu ne, amma su suna so su murÆ™ushe jikkunanmu ne, mu (kuma) muna son mu rinjayi ruhunansu ne”…Saboda haka in mutum ya lura da mu, mu ba mu É—auka wani ne muke faÉ—a da shi ba, gaskiyar magana kenan, mu muna Æ™ira (Da’awa) ne, amma wasu ne suke faÉ—a da mu… suna faÉ—a da abin (da muke yi) ne” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 04 da 14).
Wannan ya nuna yadda zuciyar Shaikh Zakzaky (H) ke cike da hasken alkairi ga kowa, sam ba ya nufin kowa da sharri, hatta masu gaba da shi, da waÉ—anda suka cutar da shi fatan alkairi yake masu, madalla da irin wannan zuciya ta bayin Allah na gari.
ADALCINSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai adalci a komai nasa, sam bai da son zuciya ko fifita kai ko wani abu nasa, misali; A shekarar 1993 wasu sashen almajiransa sun juya masa baya suka yi masa tawaye saboda zargin cewa yana Æ™oÆ™arin Shi’antar da su da canza musu alÆ™ibla daga mabiya Sahabbai zuwa mabiya Ahlul-Bait (AS).
Bayan sun shelanta É“alle masa, sai suka lashi takobin sai sun wargaza wannan Da’awa tasa ta kowane hali, suka shiga yin wa’azozi unguwa-unguwa na cin zarafi da aibata Shaikh Zakzaky (H) da Da’awarsa. Da Shaikh (H) ya zo yin magana akansu, sai ya faÉ—i manufofinsu da dalilansu na É“alle masa, a Æ™arshe sai ya yi addu’a ya ce; “Ya Ubangijin Musa da Haruna! Idan abin da waÉ—annan mutane suke akai, shi ne daidai, shi ya fi soyuwa a gareka, to ka wargaza nawa ka tabbatar da nasu, idan kuma abin da nake yi shi ya fi kusa da daidai, ya fi soyuwa a gareka, to ka wargaza nasu ka tabbatar da nawa!”. Idan mun lura a wannan addu’a ta Shaikh Zakzaky (H) akwai tsabar adalci da rashin son kai a cikinta.
Harwala-yau, a wata ganawa ta keÉ“e da ya yi da mawaÆ™a a tsakiyar shekarar 2015, Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Ba mu ce wannan Da’awa tamu ita ce kaÉ—ai hanyar tsira ga mutum ba, shi ya sa ma ba mu kafirta mutane ba, amma abin da muke cewa shi ne, in za ka bar Harkar, to ka tabbata inda za ka je É—in ya fi nan inda ka bari, abin da ka bari a nan za ka samu wanda ya fi shi a can inda ka je!”. Ba shakka a cikin wannan zance na Shaikh (H) akwai babban abin la’akari na adalci!
HAIBARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bawan Allah ne mai matuÆ™ar kwarjini da Haiba, wani mawaÆ™i yana cewa, “Kwarjininsa wane Zaki!”. In kana magana da shi ba za ka iya kallon cikin idonsa ba saboda tsabar Haiba. Sau da yawa mutane kan kasa magana da shi in sun zo gabansa.
Ni kaina haka ta taÉ“a faruwa da ni, da ma na daÉ—e ina jin ana cewa magana da Shaikh (H) sai an samu Sabati, domin kwarjininsa yana rikita mutane su mance muhimman bayanan da suka zo da su. To, wataran da za mu je ganawa da shi, sai na gama tsara abubuwan da zan faÉ—a masa, na haddace abubuwan tsaf, sannan na yi ta addu’o’in samun IstiÆ™ama da rashin ruÉ—ewa, amma bayan mun isa falonsa, da ya zo ya zauna ya kalle ni ya ce bismilla, duk sai na manta abin da zan faÉ—a, ina ta kame-kame, ba ya jin ma abin da nake faÉ—a, Haiba da kwarjininsa duk sun lulluÉ“e ni!”.
Haka nan, wasu da suka je ganawa da Shaikh (H) kan wasu matsaloli, sai mai gabatar da batutuwan ya kasa gabatar da su yadda ya kamata, bayan sun fito sai wasu suka ce masa ya ba ka ambaci kaza da kaza ba? sai ya ce musu; “Hmnn, ba ku san magana da Shaikh (H) ta fi dutsen Uhudu nauyi ba ne? Ai Haibarsa tana rikitawa mutum lissafi”.
Wani É—an uwa cikin kundin adana bayanansa (Diary), ya rubuta labarin yadda ya fara ganin Shaikh Zakzaky (H) a rayuwarsa, da irin Haiba da kwarjinin da ya kama shi. Ya ce; “Na daÉ—e ina jin labarin wannan Malamin, amma ban taÉ“a ganinsa ba, sai na ce lallai ina so in gan shi tunda an ce anan cikin Zariya yake zaune… Da isata gidansa na tarar da wasu mutane (a falo suna zaune)… zuwa can sai Malam ya fito, ina ganinsa jikina ya É—au rawa, na ji numfashina ya É—auke, wani sanyi ya sauÆ™a a zuciyata. Malam ya zauna ya kalle ni ya yi mani sallama, na amsa masa… tun daga wannan haÉ—uwa ne na ji wani Ruhi na sanin waye ni ya shige ni, wata tsima ta neman ‘yanci ta shige ni, wani so ga Allah da sallamawa dokokinsa ta lulluÉ“e ni, na ji ba ni da buÆ™atar in tuna baya!” (Wakilin Manzo a Doron Ƙasa, shafi na 24-26).
Wata rana wani Laccara na “Islamic Studies” ya shigo aji, ya yi karatu akan nazarin ingancin hadisin da ke cewa; Ubangiji na da wasu bayi waÉ—anda da zaran an ambace su sai a girmama Allah (a ce ‘Allahu Akbar’)”. Laccara ya ce; Wasu Hadisai da bayanan Malamai sun tabbatar da cewa, sai “Waliyan Allah na Æ™oli ne ke kai wa wannan matsayi, domin kuwa su Allah ne ke son su har ya mayar da lamarinsu da an ji sunansu ko an gan su sai a tuna Allah”. Sai Laccara ya tambayi É—alibai, “A cikin malaman da kuka sani, wa ke da wannan matsayin?”
Sai wani É—alibi ya ce “Allah gafarta Malam sai shugaban ‘yan Shi’a É—in nan! Shi ne saboda sadaukarwarsa ga addini daga an faÉ—i sunansa ba ka sanin lokacin da bakin ka zai girmama Allah”. Sai Laccara ya tambayi É—alibin, “Ya sunansa?” É—alibin ya ce “Sunansa Shaikh Ibraheem Zakzaky!” ai yana faÉ—in haka sai baki É—ayan É—aliban ajin suka É—auka “Allahu Akbar!” daga ranar Laccara ya shiga nazarin rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) don sanin sirrinsa. (Tasarrufi daga littafin Wakilin Manzo (S), 01-27).
MARTANINSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne Fasihi mai hikima da hangen nesa cikin maganganu da furucinsa, sam ba ya fusata a yayin da ya fahimci an yi abu ne dan a tunzura shi. Tarihin rayuwar Shaikh Zakzaky (H) cike take da suka da kai farmaki ga Da’awarsa da ra’ayoyinsa da aÆ™idunsa daga Malaman hukuma da duk masu adawa da shi, amma abu mafi armashi shi ne irin raddi da martanin da yake mayar wa masu sukarsa daga lokaci zuwa lokaci, domin martani ne mai cike da fasaha da Hikima da Juriya, wannan yana cikin abin da yake burge jama’a game da shi.
Misali; A shekarun farko-farko na Da’awarsa, malaman hukuma sun yi ta suka da aibata shi da kushe fikirarsa, wani babban Malami ya taÉ“a aibata shi a kafafen yaÉ—a labarai cewa; “Su Al-Zakzaky masu cewa sai an yi shari’a da AlÆ™ur’ani ‘yan yara ne Æ™anana, kuma ba malamai ba ne ba su da wani ilimin addini mai zurfi!”.
Da Shaikh Zakzaky (H) ke mayar da martani ga malamin sai ya ce; “To, ai waÉ—annan abubuwan da aka aibata mu da su ba aibi ba ne, kuma ba su ne ma’aunin da za su nuna mutum yana kan É“ata ba, domin yarinta ba laifi ba ne, tunda muna raye ai wataran za mu girma, da ma ba a haihuwar mutum a tsoho, daga yaro yake girma har ya tsufa.
“Sannan rashin zurfin ilimi ma ba aibi ba ne, ba dai muna karatu ba? To, da sannu wataran za mu zama malamai, aibi shi ne a ce ba ma karatu, kuma muna gaba da ilimi, in mun ga littafi ma yagawa muke yi, wannan shi ne laifi, amma in dai muna karatu, to ai da sannu nan gaba za mu zamo malamai!”. Ba shakka akwai hikima da basira a wannan martani na Shaikh (H), ka yi nazari!
Wahabiyawa da Salafawa a shekarar 2002 sun cika kunnuwan jama’ar Æ™asa da farfaganda cewa wai shugaban Æ™asa na wancan lokacin Olusegun Obasanjo ya naÉ—a Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a muÆ™amin ‘Shugaban Zaman Lafiya’ na tarayyar Nijeriya, sun yi ta shelanta wannan magana a wuraren wa’azozinsu da kafafen yaÉ—a labaru.
To, a wata hira da gidan Rediyon tarayya na Kaduna suka yi da Shaikh Zakzaky (H) sai suka tambaye shi ko zai mayar da martani ga masu wancan iÆ™irari? Sai Shaikh (H) ya ce; “Akwai wani abu da na yi ta ji irin wannan, sai daga baya na fahimci asalin maganar. Akwai Ibrahim Musa Gashash, yana da wata Æ™ungiya wacce da turanci ake ce mata “National Tranquility Movement” da Hausa sai aka fassara ta da “Kungiyar Wanzar da Zaman Lafiya”. Wani Æ™ila sunan Gashash É—in bai saba ji ba, kuma Zakzaky ma bai saba ji ba, sai ya É—auka shi Gashash É—in shi ne Zakzaky, duk kuma akwai Ibrahim a sunanmu, ina tsammanin daga nan fa aka ce ai Al-Zakzaky shi ne shugaban zaman lafiya!
“Har nake cewa waÉ—annan surutan da ake yi, ya kamata in har da gaske ne gwamnatin Æ™asar nan ta yi wata Æ™ungiya mai suna “Ƙungiyar Zaman Lafiya” kuma har ta naÉ—a Al-Zakzaky a matsayin shugabanta. To, ai ya kamata a taya ni murna ne, ba a yi ta yi min surutu ba, sai a ce Alhamdulillah, ka ga yanzu za ka samar da zaman lafiya a Æ™asa. Amma sai ya zama suka suke yi, ma’ana yanzu sun fahimci cewa ita hukuma abin da take yi ba daidai ba ne, bai kamata ya zama wani mutumin kirki yana tare da ita ba, ina tsammanin haka suke kallo, shi ya sa ma suke neman su aibata ni akan cewa ina yi wa hukuma aiki!” (Mujaddadin Wannan Ƙarnin, shafi na 36). Kalli yadda Shaikh ya mayar da martani cikin ruwan sanyi da hikima kan wannan batu.
Lokacin da aka fara “Tattakin Arba’een” daga kusurwowin Nijeriya guda huÉ—u zuwa Hussainiyya BaÆ™iyyatullah Zariya a shekarar 2011. Ƙasar ta É—au É—umi ta hanyar surutai da aibatawa kala-kala daga malaman Wahabiyawa, suka yi ta cewa wannan abin da ‘yan Shi’a almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke yi na Tattakin É—aruruwan kilomitoci cikin yunwa da Æ™ishin ruwa, suna tafiya da Æ™afa suna dukan Æ™irjinsu sanye da baÆ™aÆ™en kaya, bautar da kai ne da azabtar da jikinsu ga aikin banza, wanda baida lada balle la’ada!
Da Shaikh Zakzaky (H) yake mayar musu da martani a wani jawabinsa sai ya ce musu; “Ina ruwanku! Me ya dame ku da abin da muka sa kanmu? Da Æ™afar wa muke takawa a Tattakin? Ba da Æ™afar mu bane? Ƙirjin wa muke duka? Ba Æ™irjinmu ba ne? Cikin wa yake shan yunwa? Ba cikinmu ba ne? A jikin wa muka sa baÆ™aÆ™en kayan? Ba a jikinmu ba ne? WaÉ—anne idanu ne suke yin kuka? Ba idanunmu ba ne? To, meye naku a ciki? Meye naku na Æ™orafi da surutu? Kusa mana ido mana kawai?” Mai karatu, kai ya ka gani?
KYAUTARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tamkar ruwan sama yake a fagen kyauta, duk abin da ya mallaka, to na kyautarwa ga al’umma ne. Kyautar Shaikh Zakzaky (H) tana buÆ™atar a yi wallafa ta musamman a kanta, amma tunda komai taÆ™aitawa muke yi, bari ita ma mu taÆ™aita da ‘yan misalsali;
A shekarar 2014 sojojin Nijeriya suka kashe manyan ‘ya’yansa guda uku, to, a lokacin da ake zaman karÉ“ar gaisuwa ta shahadar yaran, wata tsohuwa ta shigo ta yi wa Shaikh Zakzaky (H) ta’aziyya, bayan ta yi masa ban haÆ™uri tare da yi wa yaran addu’ar samun rahama, sai ta sa hannu ta É—auko É—ari biyu ta bayar ta ce a miÆ™a masa. Da Shaikh ya karÉ“a ya yi godiya, sai ya sa hannu a aljihu ya ciro adadin wasu kuÉ—i masu yawa ya miÆ™a mata, ya ce ga shi ta sai goro. Tana Æ™irgawa sai ga Naira dubu Ashirin cif! Da wani jikanta ya samu labarin abin da ya faru sai ya ce mata; Da É—ari biyar kika ba shi, da dubu 50 za ki samu! Domin “Man’jaa’a Bil-Hasanati, Falahu Asharu Amthaliha”.
Wani É—alibi ya samu takardar izinin shiga jami’a “Admission”, amma sai ya zamo shi da iyayensa ba su da kuÉ—in yin rijista, ga lokaci yana ta Æ™urewa, sai aka shawarci É—alibin cewa ya je ya kai kukansa ga Shaikh Zakzaky (H), sai kuwa ya zo ya samu Shaikh ya nuna masa takardar ‘Admission’ É—in da ya samu na shiga jami’a amma baida kuÉ—in yin rijista.
Sai Shaikh (H) ya ce masa, “Bari in shiga gida in gani ko Allah zai bada mafita”, zuwa can Shaikh ya fito da ambulan a hannu, ya ce ina É—alibin nan? Aka ce ga shi nan, ya miÆ™a masa ambulan ya koma cikin gida. Da É—alibin ya buÉ—e ambulan É—in sai ya ga Naira dubu É—ari biyu cur! Ya rinÆ™a tsalle yana murna. Ya je ya yi rijista sannan ya sayi mashin na zuwa makaranta, sauran canjin kuma ya kai wa iyayensa.
Kyauta a wurin Shaikh Zakzaky (H) ta zama tamkar jinin jiki, domin hatta manyan mutane in sun ziyarce shi ba ya bari su tafi hannu rabbana, sai ya ba su kyautar da ta dace da su, misali; da Ambasadan Iran ya ziyarce shi a gida a shekarar 2014, sai ya ba shi kyautar AlÆ™ur’ani rubutun hannu. Da Ambasadan Swiss ya ziyarce shi, shi ma ya ba shi kyautar AlÆ™ur’ani don ya yi nazari. Haka nan idan manyan malaman Ahlis-Sunnah sun ziyarce shi, yakan ba su kyautar littafin “Sahifa Sajjadiyya” da sauran muhimman littattafai. Duk dai wanda ya ziyarce shi yakan masa kyautar da ta dace da shi ne.
A shekarar 2007 ya sayawa Sarkin Makafin Zazzau da mutanensa makeken gida a unguwar Tudun Wada Zariya, sannan duk lokacin da dandazon makafin suka kai masa ziyara sai ya ba kowannensu magudan kuÉ—aÉ—e.
Shaikh Zakzaky (H) ya kasance yana ba matan da yake karatu da su a F.I.C kyautar kuɗi akai-akai, kuma suna karatun ne a ranar Talata ta kowane mako, amma bai taɓa gajiyawa ba, daga lokaci zuwa lokaci sai ya ba kowaccensu kuɗi mai kima. Haka nan matan da yake gudanar da karatun Daura da su duk bayan wata biyu, ya kasance yana ba duk wacce ta halarci Daurar kuɗi masu kima, har ta kai ga mata sukan ci bashi su biya wasu buƙatunsu in sun lura lokacin Daurah ya kusa, ko su ci bashin kuɗin mota su zo, don suna da tabbacin samun kuɗi muddin Shaikh Zakzaky na gari.
TAIMAKONSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya zama babban Bango majinginar bayi a Nijeriya, ya zama Baya mai goya marayu, Shaikh ya zama gatan al’umma baki É—aya! Babu mai musun hidimar Shaikh Zakzaky ga al’umma ko da kuwa hassada da Æ™iyayya ta makantar da shi, domin gudunmawar Shaikh ga al’umma ya shafi kowa ta zahiri ko ta baÉ—ini, ta kai tsaye ko a fakaice.
Shaikh Zakzaky (H) ya koyar da É—alibansa hidima ga al’umma, ya nuna musu cewa wajibi ne su yi hidima ga raunanniyar al’ummar da suke zaune a cikinta, domin al’ummar tana buÆ™atar masu yi mata hidima, kuma ya zo a hadisi cewa, “Mafi alherin mutane, shi ne wanda ya ke anfanar da mutanen”.
Albarkar wannan karantarwa ta Shaikh Zakzaky (H), dubban almajiransa a garuruwa da dama ke bada gudunmawar jini a manyan asibitoci da ƙanana don tallafawa marasa lafiya da majinyata. A kowane taro (musamman na Ashura da Maulidi), almajiran Shaikh Zakzaky a duk inda suke suna zuwa asibitoci su bada jininsu kyauta a ɗiba a sanyawa majinyata maza da mata, yara da manya, kiristoci da musulmi ba tare da nuna banbanci ba. Wannan gudunmawa da suke badawa ta sha tseratar da ɗimbin rayuka daga salwanta.
Haka nan, Shaikh Zakzaky (H) da kansa ya zayyana wasu ayyukan da ya kamata almajiransa su riÆ™a yi don taimakon al’umma, kama daga gyara maÆ™abartun musulmi, kwashe bola, tsabtace kwata, gyara hanyoyin ruwa, feshin maganin sauro da na kashe Æ™wayoyin cututtuka, bada gudunmawar abinci da kayan masarufi ga raunana da waÉ—anda wani bala’i ya shafa, gina hanyoyin ruwa don magance ambaliya da sauransu. WaÉ—annan abubuwa kuwa sune muhimman ayyukan da wasu Lajanoni na almajiran Shaikh Zakzaky irinsu “Youth Forum” da “Lajanar Hurras” ke aiwatarwa a ko da yaushe cikin al’ummah, wanda hakan ba Æ™aramin kyautata rayuwar jama’ar Æ™asa yake ba.
A gefe guda, Shaikh Zakzaky (H) ya sha daÆ™ile fitina da tarzoma a tsakanin mutanen gari. Farkon zuwansa unguwar Gyallesu ya samu Æ™ungiyoyi biyu na matasa ‘Yan daba suna gaba da juna da faÉ—ace-faÉ—ace, wanda kusan kullum sai sun yi kisan kai a junansu. Sai Shaikh (H) ya sa aka Æ™ira su gidansa, ya yi zama da su, ya yi masu nasihohi masu ratsa jiki, ya sasanta su suka dena kashe junansu. Sannan Shaikh (H) ya hana abkawa kiristoci a lokutan zaÉ“e ko na hargitsin addini, duk inda almajiransa suke, sukan baiwa kiristoci kariya da ba su mafaka don tseratar da rayukansu a lokacin rikici ko na hargitsi. Haka nan a shekarar 2011 lokacin zaÉ“en shugaban Æ™asa, duk da cewa Shaikh Zakzaky da almajiransa ba sa zaÉ“e, amma ya umarci almajiransa sun ba jami’an zaÉ“e kariya daga abkawar mutane a duk runfunan zaÉ“en da ke kewaye da unguwar Gyallesu da wasu sassa na birnin Zariya.
Shaikh Zakzaky (H) ya zamo gatan marar gata a cikin al’umma, misali; A shekarar 1994 wani Sarkin gargajiya a yankin Kudan ta jahar Kaduna ya Æ™wacewa wata tsohuwa makekiyar gonar da ta gada, sai ta kai Æ™ara wurin manya amma suka kasa Æ™wato mata gonarta, ta kai Æ™ara kotu, kotu ta tabbatar da cewa lallai gonarta ce, amma kawai ta yi haÆ™uri dan wanda ya Æ™wace gonar ya fi Æ™arfinta. Tsohuwar nan ta rasa inda za ta sa kanta, alhali tana da ‘ya’ya da jikokin da take so ta barwa gadon gonar. Sai mutane suka ba ta shawarar ta zo Zariya ta sanar da Shaikh Ibraheem Zakzaky halin da take ciki, kuma ta nemi taimakonsa.
Da ta zo ta gabatarwa Shaikh Zakzaky (H) shaidunta, da kwafin takardun hukuncin kotu, sai Shaikh da rakiyar ɗimbin almajiransa ya je garin na Kudan ya ziyarci gonar, sannan ya yi jawabi mai girgiza azzalumai, kuma ya ce ya dawo wa da tsohuwar nan gonarta tunda kotu ma ta tabbatar da cewa gonarta ce. Daga nan azzalumin sarkin garin bai ƙara iƙirarin ƙwace gonar ba, haka ya haƙura!
Haka nan, almajiran Shaikh Zakzaky (H) a garuruwa da jihohi da dama sun zama gatan raunana marassa gata a yayin da aka zalunce su ko aka yi musu danniya akan wani muhimmin haƙƙinsu, wannan ya nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ya zama gata ga wannan al’umma.
CIYARWARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne da ba abin da yake son yi fiye da kyautatawa al’umma, musamman al’ummar wannan Æ™asa tamu da ke fama da Æ™uncin rayuwa a É“angarori daban-daban. Tun asali Shaikh Zakzaky (H) ya taso ne da burin kyautatawa mutane musamman ta É“angaren ciyarwa, domin tarihinsa ya nuna tun yana Jami’a yake ciyar da É—alibai da abokansa.
Marubucin littafin “Tarihin Harkar Musulunci” a shafi na 94 ya kawo cewa; A lokacin da Shaikh Zakzaky (H) yake É—alibta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, É—alibai dare da rana suna yin Safa da Marwa zuwa É—akinsa don su sha Shayi, ko su ci cincin da dai sauran nau’ukan abincin da yake samarwa, domin a lokacin Shaikh (H) yana sawa a yo cincin kwalla-kwalla a kawo É—akinsa, domin É—alibai ‘yan uwansa ba sa rabuwa da zuwa É—akinsa komai dare don neman abin sawa a bakin Salati.
Haka nan, a zaman kurkukun da ya yi a Inugu, ya kasance yana ciyar da sauran ‘yan Fursuna da abincin da ake kawo masa daga maziyarta, É—aya daga cikin almajiransa Shaikh YaÆ™ubu Yahya ya labarta cewa; “A wani lokaci mun ziyarci Malam a kurkukun Fatakwal, kuma mun je masa da É—an guzuri haka, soyayyen nama ne da sauransu, (bayan mun shigar masa É—aki, da ya gani) sai ya ce a maida shi waje, aka dawo da shi waje, su Madara da Bonbita da sauran kayayyaki duk ya sa aka raba wa mutane, har wani (Inyamuri É—an fursuna) yana cewa; “Alhaji No Dey Chop, No Dey Sleep!” wato Malam ba ya cin abinci kuma ba ya bacci!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).
KARAMCINSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sarkin karimci ne da Baiwa ga duk wanda ya raÉ“e shi, yana da halin girma na kyautatawa kowa fiye da zatonsa. Misalai akan karimcin Shaikh Zakzaky (H) ba su Æ™irguwa, amma bari mu ambaci ‘yan Æ™alilan.
Malama Jameela Auwal (uwargidan Malam Mukhtar Sahabi) ta ba mu labarin wani karamci da Shaikh Zakzaky (H) ya yi mata, ta ce; “Lokacin da zan raka ‘yata Maryam Iran bayan É—aura aurenta, mun je yin Sallama ga su Shaikh (H), sai ya tambayeni ta ina za mu tashi? Sai na ce masa ta Legos ne, sai ya ce; Gobe da sassafe za ku bar Kaduna kenan tunda Æ™arfe 2 jirginku zai tashi” sai na ce ai yau ne ma za mu kama hanya zuwa Legos, don ta mota za mu tafi, sai Shaikh ya ce; A’a, ai mota akwai wahala, a ce wa Malam Mukhtar ya yi muku bukin na jirgi gobe sai ku tafi, zan turo masa kuÉ—in!” haka kuwa aka yi, ya biya mana kuÉ—in jirgi muka tafi Legos ta jirgin sama, anan na Æ™ara tabbatar da cewa; “Sayyidul Ƙaumi Khadimuhum”. (Dandalin Khairul-Amal na Whatsapp, 2016).
A watan Maulidi na shekarar 1437 Hijira, rundunar sojojin Nijeriya suka farwa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a gidansa da ke unguwar Gyallesu a cikin birnin Zariya, kafin su kai ga Shaikh É—in sai da suka kashe É—aruruwan almajiransa maza da mata har da jarirai. A lokacin wannan ta’addanci na sojoji da ya shafe tsawon yini uku suna yi, sashen mutanen wannan unguwa wacce ke cike da jami’an leÆ™en asiri, sun bada gudunmawa sosai da goyon baya ga ta’addancin da ake yi wa Shaikh É—in da almajiransa, wanda hatta wasu marubuta sai da suka kwatanta mutanen unguwar ta Gyallesu da mutanen Kufa, wanda suka ci amanar Imam Hussain (AS).
Amma abin mamaki, bayan watanni shida da faruwar abin, watan Ramadan ya shigo, sai ga Shaikh Zakzaky (H) ya aiko daga inda ake tsare da shi cewa; Lallai a rabawa talakawa da raunanan mutanen Gyallesu buhunan abinci na tallafin watan Ramadan da ya saba ba su duk shekara! Hakan kuwa aka yi, aka bi su gida-gida kowa ana ba shi abin da aka saba ba shi na Shinkafa da Masara da Gero da Sukari da sauran kayan masarufi. Wannan ya nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ke maida sharri da alkairi saboda karamcinsa.
Wani É—an uwa ya labarta mana cewa; “Wata rana da yamma muna zaune a falon Shaikh Zakzaky (H), sai wani É—an uwa mai hali ya ziyarci Shaikh, bayan sun daÉ—e suna hira muna saurarensu, da ya tashi zai tafi, sai ya miÆ™awa Shaikh makullin mota, ya ce; “Ga wata ‘yar mota can na kawo muku Hadiyya ko yara za su yi anfani da ita”, sai Shaikh ya karÉ“i makullin motar ya ce; “Masha Allah, Allah ya saka da alkairi”.
Bayan mutumin ya tafi, sai Shaikh (H) ya ce; Motar kuwa ta yi kyau, ina ganin za ta dace da Malam wane (ya ambaci sunan wani É—alibinsa da ke zaune a wurin)”, sai ya ce wa wannan É—alibi; “Ai wannan motar za ta yi tafiya a Sahara ko?” Kafin É—alibin ya amsa sai ya miÆ™a masa makullin, ya ce “To a je a yi ta fama da kuÉ—in mai”. Wannan ba Æ™aramin karimci bane musamman ga wanda ya san cewa ‘ya’yan Shaikh baki É—ayansu ba wanda ke da motar hawa a lokacin, amma maimakon ya ba su, sai kawai ya ba wani almajirinsa.
Haka nan Shaikh Zakzaky (H) duk shekara yana yanka wa almajiransa Ragon layya, wato duk shekara yana yanka Rago ko Saniya a madadin miliyoyin almajiransa da Allah bai nufe su da yin layya a wannan shekarar ba, kuma yana yankawa dukkan raunanan al’ummar musulmin duniya da ba su samu damar yin layya ba RaÆ™umi, kamar dai yadda Manzon Allah (S) ya yi wa al’ummarsa marassa galihu layya. Marubucin littafin “Malam, Malam Ne” yana cewa; “Na san duk sallar Layya sai Malam (H) ya yanka Rago, wato ya yi wa duk “Brothers” (‘yan uwa maza da mata) Layya, kuma ya ba su naman Ragon sun ci” (Malam, Malam Ne, shafi na 10).
JARUNTARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) jarumi ne da dukkan ma’anar jarunta, tun asali bai da tsoro, bai da fargaba bare razana, domin tarihi ya tabbatar da cewa tun yana yaro Æ™arami bai san tsoro ba. A wani biki na cikarsa shekaru 45, Shaikh Zakzaky (H) yana cewa, bai san me ya sa shi tun yana yaro baida tsoro ba, duk wani abu mai razanarwa shi ba ya razana shi, ko irin abin da ke faruwa bagatatan É—innan, wanda ke firgita mutane, to shi gabansa ba ya faÉ—uwa.
Marubucin littafin ‘Tarihin Harkar Musulunci’ yana cewa; “Akwai ma lokacin da yake cewa idan Akuya za ta ba shi tsoro, to arne ko Azzalumi zai ba shi tsoro, wato tunda Akuya ba za ta ba shi tsoro ba, to, babu wani abu da ya isa ya ba shi tsoro (a duniya!)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 29).
A wani jawabi da Shaikh Zakzaky (H) ya yi a ranar “Yaumus-Shuhada” na shekarar 2003 yana cewa; “(Mahukunta) su kan riÆ™a yin wani gadara wai su ce; Wa ya fi Æ™arfin gwamnati?’ To, mun fi Æ™arfin gwamnati! In ta ce Æ™arya ne ta zo! Iyaka dai kurkuku ne da kisa, ya wuce haka ne?....(ba ta yi harbin bane? Ba ga mu ba! Ba ta yi kamun bane? Ba ga mu ba!). To, ba ma kurkuku ba, wallahi tallahi ko da kuna da Jahannama, kuma ko da Jahannamar taku ta kai zafin ta Allah Ta’ala, a shirye muke mu shigeta! Don mun san ita Jahannamar taku mai Æ™arewa ce, ta Allah ko ba ta Æ™arewa. Ta Allah muke jin tsoro ba taku ba!”
Ba shakka Shaikh Zakzaky (H) ya gaskata wannan iÆ™irari nasa, domin duk kamun da ake yi masa bai taÉ“a gudun kar a kama shi ko ya yi rakin kamun ba, maimakon haka ma, shi nuna jin daÉ—in kamun yake yi. Misali, lokacin da aka kai Shaikh Zakzaky (H) gidan yarin azabtarwa na Kirikiri da ke Legos a shekarar 1984, ya rubutowa ‘yan uwa almajiransa wasiÆ™a, a ciki yake cewa; “Lokacin da ake tuÆ™ani zuwa Kirikiri, na ji wani daÉ—i da farin ciki wanda ban taÉ“a jin irinsa ba!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 42)
Ka ji irin wannan jarunta! Kirikiri fa; Waje ne da ake kai mutanen da ake so a musguna masu, ko a azabtar da su, domin akwai karikitai na azabtarwa daban-daban a ciki. Malam yake cewa; ko sauro mutum ya kashe sai an masa bulala, za a ce masa wai ya damu yaran gwamnati” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 43). Amma da aka kama hanya za a kai shi wurin, shi ne yake cewa ya ji wani daÉ—i da farin cikin da bai taÉ“a jin irinsa ba! Wannan wace irin jarunta ce?
Sannan bayan fitowarsa daga kurkukun Inugu, cikin jawabin da ya yi wa ‘yan uwa yana cewa; “Wani abu wanda yake shu’uri ne (wato a jiki ake jinsa), wanda sai in kai ma ka ji ne za ka iya fahimta, shi ne abin da na gani a zamana na kurkuku. (Amma) tunda ba a yarda mutum ya je ya Æ™wanÆ™wasa gidan kurkuku ya ce a buÉ—e masa ya shiga ba, (da ana haka da na yi, to, amma tunda ba a yi), duk ran da aka zo aka kamani zuwa can zan yi farin ciki!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 44). Mai karatu, ka ji mai neman shiga kurkuku, wanda bai taÉ“a tsoron É—auri a gidan fursuna ba, da me za ka kwatanta jaruntarsa?
Shaikh Zakzaky (H) jarumi ne da dukkan ma’anar jarunta, domin lokacin da gwamnatin Nijeriya Æ™arÆ™ashin jagorancin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta kama shi ta gurfanar da shi a gaban kotu, alÆ™alin kotun Justice Karibi White ya yanke masa hukuncin É—aurin shekaru huÉ—u a gidan kurkuku. Bayan an karantawa Shaikh Zakzaky (H) laifinsa da irin hukuncin da kundin tsarin mulki ya tanada ga masu irin wannan laifi, kafin a zartar da hukuncin, sai alÆ™ali ya tambaye shi cewa; “Ko kana da wani roÆ™o (na neman sassauci) da za ka yi ga kotu?”
Sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Ina roÆ™on kotu ne da ta zartar mun da mafi munin hukuncin da za ta iya, ta zartar mun da mafi tsananin hukunci na iya Æ™urewarta! Kar ta sassauta mini!” Sa’annan Shaikh Zakzaky (H) ya fuskanci alÆ™ali Karibi White ya ce masa; “Idan kana da zaÉ“i tsakanin harbi ko É—aurin rai da rai, to ka zartar mun da hukuncin harbewa!” Wannan jawabi ya girgiza alÆ™ali da duk waÉ—anda ke cikin kotun, dan ba su taÉ“a jin wanda ke fuskantar hukunci ya faÉ—i haka ba a tarihinsu!
Jaruntar Shaikh Zakzaky (H) za ta Æ™ara fito maka fili ne in ka san cewa; “(Saboda yawan) kame-kame na ba zata (da ake yi masa), sai da ta kai ga Malam a wani lokaci ya kai ga aje wata jaka, a cikinta ya sa sabulun wanka da na wanki, man shafawa, turare, (Makilin da Brush), da tufafi na canzawa da dai makamantansu, yake cewa jakar ba ya taÉ“a ta, tana aje ne kawai, da an zo kama shi sai dai ya É—auketa (ya rataya) ya ce mu je!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 44).
A lokacin mulkin sugaban Æ™asa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2007), labaran asiri sun yi ta zuwa cewa ana shirin abkawa da kashe jogaran Harka Islamiyyah Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da rahotannin suka yi Æ™arfi sai wasu suka shawarci Shaikh Zakzaky (H) cewa ko zai É—an yi hijira zuwa wata Æ™asa kafin abubuwa su daidaita, sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Ko Janar aka ce masa Zakzaky zai yi gudun hijira zai ce Æ™arya ne!!” wannan ya nuna jaruntar Shaikh Zakzaky (H) ne a fili Æ™arara!
Tabbas Shaikh Zakzaky (H) ya gaskata wannan iÆ™irari nasa, domin lokacin da gwamnatin shugaban Æ™asa Umaru Musa Yar’adua ta shirya jefa Bom a gidansa cikin dare a shekarar 2010, an shawarci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da ya bar gidan, amma ya ce wallahi ba inda za shi, sai dai su kashe shi a cikin gidansa, kuma haka aka yi, a cikin gidan ya kwana, Allah Ta’ala ya wargaza mummunar aniyarsu.
Haka nan, mummunan harin da bataliyar sojojin Nijeriya Æ™arÆ™ashin Hafsan sojoji Janar Tukur Yusuf Burtai, bisa umarnin shugaban Æ™asa Muhammadu Buhari suka kai gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a watan Disamba na shekarar 2015, inda suka kashe kusan mutum dubu kafin su iya kaiwa gare shi, tun kafin su ci Æ™arfin ‘yan uwa an buÆ™aci a fita da Shaikh Zakzaky (H) don tseratar da shi, amma ya ce ba inda zai je, yana nan a cikin gidansa, sai dai su zo su yi masa duk abin da za su yi!
Hakan kuwa aka yi, sai da aka shafe sama da awowi 48 ana ruwan wuta, har aka cimma gidansa, aka harbawa gidan Gurneti, gidan ya kama da wuta ya Æ™one Æ™urmus, amma Shaikh Zakzaky (H) yana cikin wani Æ™aramin É—aki na dakin shi da iyalansa, Æ™arshe har suka zo kansa suka yi ruwan harsashi suka kashe ‘ya’yansa uku, suka harbi matarsa a sama da wurare goma a jikinta, shi ma suka harbe shi a wurare goma sha É—aya a jikinsa, ciki har da cinya da Æ™irji da goshi da idanuwansa biyu har sai da idonsa na hagu ya zazzago ya fito waje, sa’annan suka É—auke shi suka tafi da shi rai a hannun Allah! Wannan jarunta irin ta Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tarihi ya daÉ—e bai ga irinta ba!
AMSA ADDU’ARSA:
Allah Ta’ala ya yi alÆ™awarin amsa addu’ar bayinsa a yayin da suka roÆ™e shi, tattare da haka bayin Allah managarta addu’o’insu sun fi karÉ“uwa cikin gaggawa da sauri. Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin bayin da Allah ke gaggauta karÉ“ar addu’o’insu da biya musu buÆ™atar abin da suke nema.
Misalin hakan shi ne; A shekarar 1991 an yi waÆ™i’a a birnin Katsina, inda jami’an tsaro suka farwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da suka fito muzaharar Allah wadai da zagin Manzon Allah (S) da wata jarida mai suna “FunTimes” ta kanfanin “Daily Times” ta yi. Jami’an tsaron sun farwa ‘yan uwa suka yi ta dukansu da kulake da gindin bindiga, inda suka raunata da dama, suka kwashe su cikin jini suka je suka kulle ba tare da sun kai su asibiti don magani ba.
Bayan kwana biyu da faruwar lamarin, sai ‘yan jarida suka tuntuÉ“i kwamishinan ‘yan sanda na Katsina a lokacin, wato Saminu Daura dan jin halin da ‘yan uwan da ake tsare da su suke ciki. Sai Saminu Daura ya ce duk waÉ—anda ake tsare da su suna cikin Æ™oshin lafiya da aminci, alhali a lokacin ‘yan uwa suna tsare a hedikwata da barikin ‘yan Sanda cikin tsananin galabaita da raÉ—aÉ—in ciwuka da raunukan da aka yi musu ba tare da ba su magani ba.
Da Shaikh Zakzaky (H) ya ji wannan hira sai ya yi raddi ga Saminu Daura, ya ce; Idan halin da ‘yan uwa ke ciki shi ne halin Æ™oshin lafiya da aminci, to yana roÆ™on Allah ya ba Saminu Daura irin wannan Æ™oshin lafiya da amincin! Ba a daÉ—e da wannan addu’a ba Saminu Daura ya kamu da matsananciyar jinya wacce wasu rahotanni suka ce har haushin Kare yake yi, zuwa É—an wani lokaci ya sheÆ™a barzahu.
Har wala yau, a Shekarar 1992, jami’an tsaron Nijeriya sun kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a birnin Kano lokacin da zai je wani taro a Æ™asar Ingila. Suna kama shi suka yi awon gaba da shi zuwa kurkukun Dodon-Barrack na Legos, da nufin tsare shi har illa masha Allah. Shi kuma Shaikh (H) a lokacin yana cike da shauÆ™in halartar wannan taro na London. Dan haka yana shiga kurkukun ya É—aga hannu ya roÆ™i Allah cewa ya tabbatar masa da wannan buri na tafiya London don halartar wannan taro da kuma haÉ—uwa da ‘yan uwa na Ingila.
Addu’ar da ya yi tana da ma’ana kamar haka; Ya Allah, ka sani na yi zaman kurkuku a wuri kaza da kaza, amma daidai da rana É—aya ban taÉ“a roÆ™onka ka fitar da ni daga cikinsu ba, sai dai da kanka kake fitar da ni a lokacin da ka ga dama. Amma a wannan karon ina shauÆ™in haÉ—uwa da ‘yan uwa na Ingila da ganawa da su, ina so in halarci wannan taro da za a yi, ina roÆ™onka ka fitar da ni da ikonka, “Ya Allah ka gaskata zatona gareka”.
Yana yin wannan addu’ar sai kawai umarni ya zo na sakinsa, kuma aka ba shi takardunsa na izinin tafiya, ya kama hanya ya fita zuwa Ingila, duka-duka tsarewar da aka masa a lokacin ta ‘yan kwanaki ce.
Sannan, a shekarar 1994, bayan wasu almajiransa sun É“alle sun yi masa tawaye, sai suka yi gangami suka kafa Æ™ungiyar yaÆ™arsa da bishe hasken Da’awarsa mai suna “Jama’atu Tajdeedil Islam” wato JTI atakaice. Sai ya yi jawabi game da su, ya fayyace musu abubuwan da suke zarginsa da su na aÆ™idar Shi’anci daki-daki. Sannan daga Æ™arshe sai ya roÆ™i Allah Ta’ala cewa; Ya Ubangijin Musa da Harun, idan abin da waÉ—annan mutane suke akai, shi ya fi soyuwa da zama daidai a gareka, to ka rusa nawa ka tabbatar da nasu, idan kuma nawa ne ya fi soyuwa gareka da zama daidai, to ka rusa nasu ka tabbatar da nawa”.
Bayan yin wannan addu’ar ba daÉ—ewa Allah ya rusa wannan gungu na ‘yan Tawayiya, ya shagaltar da su da kawukansu, suka tarwatse suka dena batun Tawayiyanci suka shagaltu da neman duniya da neman abinci, ya zamanto su da Æ™ungiyar ta su ta JTI ba su da wani tasiri a cikin al’umma, hasali ma mafi yawan jama’a ba su san da Æ™ungiyar tasu ba. Wannan ‘yan misalai ne kawai na yadda Allah Ta’ala ke amsa addu’ar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).
KARAMOMINSA:
Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) karamomi masu yawa, waÉ—anda aka sani da waÉ—anda ba a sani ba, domin Shaikh Zakzaky (H) ya kasance mai É“oye karama da rashin son nuna ta, amma tattare da haka wasu karamominsa kan bayyana ba tare da nufi ba.
Misali; Kamun da aka yi masa na farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya cikin shekarar 1979, an kulle shi a ofishin ‘yan sanda ne na Zariya, ya shafe kwana uku ba ci ba sha, suka hana shi cin komai, bayan kwana uku sai suka fito da shi da nufin zai amsa wasu tambayoyi, da suka ba shi takarda ya rubuta jawabinsa (Statement), sai da ya rubuta musu shafi tara na amsoshin abin da suka tambaye shi, har su jami’an tsaron suna mamaki, suna cewa dubi rubutunsa mai kyau kamar wanda bai sha yunwa ba! A wata hira Shaikh Zakzaky (H) ya ce, duk da ya shafe tsawon kwanakin bai ci abinci ba, amma shi kwata-kwata bai ji yunwa ko Æ™ishin ruwa ba. Wannan karama ce babba! (Rairayowa daga Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 42)
A farkon shekarun 90s, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya je Umrah, a hanyarsa ta dawowa sai jirgin samansu ya samu matsala, (wasu sun ce da gangan aka so a halakar da shi). Jirgi ya rinÆ™a tangal-tangal, fasinjoji suka rikice suna ihu da neman taimako, amma Shaikh Zakzaky (H) yana zaune a natse akan kujerarsa yana ta karatun AlÆ™ur’ani, sam babu alamar damuwa a tattare da shi kamar bai san abin da ke faruwa ba. Da matsalar ta Æ™ara muni, hankalin fasinjoji ya tashi matuÆ™a, sai Shaikh cikin natsuwa ya É—aga hannu sama ya yi wata gajeruwar addu’a, nan take jirgin ya daidaita, sai ga sanarwa daga matuÆ™a jirgin cewa komai ya yi daidai. Wannan ya sa mutane da yawa a jirgin suka rinÆ™a neman tabarrukin Shaikh (H), har wani a cikin mahajjatan ya ce “Daga yau na zama É—an Buraza!” (Tasarrufi daga Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 09).
A shekarar 1992, lokacin da aka kama Shaikh Zakzaky (H) a filin jirgin Malam Aminu Kano sa’adda zai tafi Ingila, an kai shi wani wuri ne aka tsare shi ya kwana, washe gari sai aka zo da sabuwar mota aka sa shi a ciki, aka kama hanya ba tare da an ce masa uffan ko an sanar da shi inda za a kai shi ba. To, tun ba a fita daga cikin Kano ba, sai Shaikh Zakzaky (H) ya cewa jami’an tsaron da ke tafiya da shi; “Ku me ya sa ba za ku yi É—abi’a irin ta mutane ba! Wannan É—abi’a taku ta saÉ“a da É—abi’a irin ta mutunci, domin ni mutum ne kuka É—auko ba Akuya ba, idan za ka saka Akuya a cikin mota ka kai ta Legos, ba ka buÆ™atar ka yi mata bayani, ka ce Akuya zan kai ki Legos. Haka nan idan za ka É—auki buhun shinkafa, ba ka buÆ™atar ka ce masa zan kai ka wuri kaza, sai dai ka kai shi kawai. Amma ni mutum ne (ba Akuya ko Buhun shinkafa ba), menene ya hana a jiya ku ce min, an umarceku ne ku hana ni tafiya, kuma yau ku ce, an umarce mu da mu kai ka Legos? Shi kenan!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 45, da tasarrufi kaÉ—an).
A wannan abun da ya faru akwai nuna Karama a ciki, domin ba wanda ya ce wa Shaikh Zakzaky (H) Legos za a kai shi, sai ga shi cikin hikima ya faÉ—a musu cewa Legos za su kai shi, kuma Legos É—in suka kai shi kai tsaye. Wannan menene in ba Karama ba?
A shekarar 1994 a wani gari da ake kira Lushi a kusa da birnin Bauchi, Æ™asa ta kama hannun wani yaro saboda ya Æ™aryata Shaikh Zakzaky (H). Musu suke yi da ‘yar uwarsa, shi yana cewa Shaikh Zakzaky É“atacce ne kuma Da’awarsa halaka ce. Ita kuma yarinyar (wacce ‘yar Baffansa ce) tana cewa lallai Shaikh Zakzaky akan shiriya yake, kuma yana kira ne zuwa ga hanya madaidaiciya.
Sai suka yi ittifaÆ™i cewa su yi ‘yar Æ™asa-Æ™asa, (wata al’adar Hausawa ce da yara ke anfani da ita don gane marar gaskiya a tsakanin mutane biyu, za a tara yashi ne ko Æ™asa, sai wanda ake tuhuma ya cusa hannunsa iya wuyan hannu a ciki, sai ya yi rantsuwa cewa in ba shi ne akan gaskiya ba to Æ™asa ta kama hannunsa). Sai yarinya mai gaskata Shaikh Zakzaky ta fara sa hannunta a cikin Æ™asa, ta yi rantsuwa, kuma ta ce in ba haka bane Æ™asa ta kama hannunta, tana zarowa sai hannu ya fito. Sai shi ma yaro ya cusa hannunsa cikin Æ™asa, ya yi rantsuwa cewa Shaikh Zakzaky (H) akan É“ata yake, kuma Da’awarsa halaka ce, in ba haka bane Æ™asa ta kama hannunsa.
Abu kamar wasa sai hannu ya maƙale, ƙasa ta riƙe hannunsa ƙam, har sai da aka kawo masa ɗauki, aka yi aka yi a cire hannu ya ƙi fita, yaro sai kuka yake yi, sai aka ce masa sai in ya warware wannan rantsuwar ya gaskata Shaikh Zakzaky ne kawai hannun nasa zai fita. Haka kuwa aka yi, yana gaskata shiriyar Shaikh Zakzaky (H) da ya zaro hannun sai kawai ya fito. Jaridar Al-Mizan ta wancan lokacin ta hakaito wannan labari na karamar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).
Haka nan, a wajajen shekarar 1997, an yi wata gobara a gidan wani É—an uwa a birnin Gombe, inda gobarar ta cinye komai na É—akin gidan amma ta bar hoton Shaikh Zakzaky (H) da ke rataye a É—akin, hatta katakon da aka sanya hoton a jikinsa bai Æ™one ba, kuma wannan hoton shi kaÉ—ai ne ya tsira a É—akin, komai ya Æ™one Æ™urmus. Wannan karama ta Æ™arawa mutane da dama yaÆ™ini game da sha’anin Shaikh Zakzaky (H).
Haka nan, wani É—an uwa da yake neman wata budurwa da aure, ya yi tsananin kamuwa da so da Æ™aunarta, sai ya yi ta yin Istihara yana roÆ™on Allah cewa; Ya Ubangiji, in aurena da wance alheri ne, ka Æ™addara mun shi cikin sauÆ™i da yalwa, in kuma sharri ne, to ka rusa abin ka hana shi yiwuwa”. Yalai kuwa sai abu ya rushe, yarinya ta kawo sunan wani wanda take so, ya turo iyayensa suka biya sadaki aka sa ranar É—aurin aure.
Sai wannan ɗan uwa ya shiga halin ƙunci mai tsanani saboda son wannan budurwa da yake yi, ya kasa jurewa rabuwa da ita saboda ɗanfaruwar zuciyarsa da ita, ba ya iya bacci balle cin abinci, komai nasa ya dagule, ya rasa abin da ke masa daɗi. Watarana sai ya ce bari ya je majalisin yamma na gidan Shaikh Zakzaky (H) da nufin ko zai manta da damuwar da ke damunsa, kuma ya yi Tawassuli da nufin Allah ya yaye masa ƙaunar yarinyar nan da ya addabi zuciyarsa.
Ya je gidan Shaikh (H) da wuri ya samu wuri a gaba ya zauna, zuwa can sai Shaikh (H) ya fito ya zauna a wurin zamansa, yana gama gaisawa da mutane sai kawai ya kama magana akan Istihara da yadda ake yinta, ya ce; “Da yawan mutane ba su iya Istihara ba, sai su roÆ™i Allah cewa “In abin nan alkhairi ne ka tabbatar mun da shi, in kuma sharri ne ka wargaza shi ka hana shi yiwuwa”. Wani lokaci in abin ba alheri ba ne sai Allah ya hana shi yiwuwa, amma ya bar ka da son abun a ziciyarka. Kamata ya yi mutane su riÆ™a cewa “Ya Allah in wannan abin alkhairi ne ka Æ™addara mun shi cikin sauÆ™i, in kuma sharri ne gareni ka kore shi daga gareni, kuma ka cire mun Æ™aunarsa da sonsa a zuciyata”.
ÆŠan uwan yana jin haka sai kunya ta kama shi, ya duÆ™ar da kai Æ™asa yana matuÆ™ar mamakin wannan al’amari, domin shi dai bai faÉ—awa kowa abin da ya kawo shi ba, bai kuma faÉ—awa Shaikh (H) wannan labarin ba, amma ya aka yi Shaikh (H) ya iya fahimtar damuwarsa? Wannan tambayar har zuwa yau bai samu amsarta ba, amma dai daga wannan rana ya samu waraka daga ciwonsa na soyayya.
Babu shakka duniya shaida ce cewa Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Zakzaky (H) karamar Kashafi, wannan karama ta Kashafi wani abu ne da ke bayyane ga ma’abuta nazari, misali; duk wani Æ™ulle-Æ™ulle da makirce-makircen da maÆ™iya suka Æ™ulla masa, ko suke Æ™ullawa Harka Islamiyyah, to za ka ga ya tona asirin shirin.
Wani lokaci za a Æ™ulla abin cikin tsattsauran matakan tsaro don kar abin ya fita, amma sai ka ji yana bada labarin yanda abin ya gudana, wani lokaci ma mutum biyu ne ko uku za su Æ™ulla abin, amma sai ka ji ya tona asirin shirin, har ma ya fito da takardar “Blueprint” É—in shirin. Wannan hatta su maÆ™iya da jami’an leÆ™en asiri abin yana matuÆ™ar ba su mamaki, wani lokaci ma ba a Nijeriya ake shirya abin ba, amma zai sani, misali kwangilar da aka ba wani Æ™wararren kanfanin kisan kai da ke Amurka, na wani É—an asalin Birtaniya mai suna Patrick Williams a shekarar 2012.
ALBARKARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wani ɗan baiwa ne mai wata irin albarka wacce ba ta ɓoyuwa ko kaɗan! Komai nasa cike yake da albarka komai ƙarancin abin kuwa, duk wanda ya san Shaikh Zakzaky (H) zai iya zama shaida kan wannan abu da muke faɗa.
Misali; Æ™anwar Mahaifin Shaikh Zakzaky wacce ake kira Goggo Fatimah, ta faÉ—i cewa; “Lokacin da aka haife shi mun ga abin mamaki, akwai jama’a da kuma abubuwan gudunmawa da aka samu, duk cikin ‘ya’yanmu ba a samu wanda aka samu falala (ta cikar jama’a da samun gudunmawa) irinsa ba!” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 67).
Anan, Goggo Fatimah tana cewa ne tun daga haihuwar Shaikh Zakzaky (H) aka ga albarkoki masu yawa a tattare da shi, É—imbin jama’a suka halarcin bikin sunansa, kuma ba Æ™aramar gudunmawa mahaifansa suka samu daga abokan arziÆ™i, makwabta da dangi ba, kenan Shaikh (H) tun asali da albarkarsa ya shigo duniya.
Kamar yadda muka faÉ—a, ba kawai Shaikh Zakzaky (H) ne ke da albarka a tattare da shi ba, duk ma wani abu mai alaÆ™a da shi ba Æ™aramar albarka yake da shi ba. Misali; masu sana’ar buga fosta ta hotunan manyan malamai, ba fostar da suke cinikinta kamar ta Shaikh Zakzaky (H), sam ba sa tsoron buga fostar Shaikh komai yawanta, domin sun san za ta Æ™are, an Æ™iyasta cewa É—aruruwan mutane ne ke cin abinci ta hanyar sayar da zallar hotuna, sitikoki, littattafai da fostocin Shaikh Zakzaky (H).
Haka nan, duk lokacin da aka rubuta littafi akan Shaikh (H) ko akan wani abu da ya dangance shi, to ba a samun kwashe na wannan littafin, ko da za a yi ta maimaita bugawa, to kuwa zai yi ta maimaita ƙarewa! Sau da yawa idan Shaikh (H) zai je wani gari, har hanyar garin ake bi a gyara wuraren da suka lalace, dan haka hatta masu bin hanya sukan samu albarkar wucewar Shaikh (H).
Idan Shaikh Zakzaky (H) zai je wa’azi ko ziyara wani gari daga cikin garuruwan Æ™asar nan, masu sana’o’i na abinci, da abin sha, da sauran kayan buÆ™atu, da masu motocin haya, da masu gidajen man fetur, ba Æ™aramar darawa suke yi ba. An taÉ“a ruwaito wani mai sayar da Shayi yana cewa; “Da Shaikh Zakzaky zai riÆ™a zuwa garin nan duk shekara, to da zan yi arzikin da zan fi Æ™arfin sayar da Shayi!”
Wani abin da ke Æ™ara tabbatar da cewa duk wani abu da ya shafi Shaikh Zakzaky (H) albarkarsa ba ta misaltuwa shi ne abin da ya faru a zauren “Marital Solutions” na ‘Whatsapp’ a cikin watan Yuni na shekarar 2016, inda wata ‘yar uwa ta faÉ—i laÆ™abin da uwargidan Shaikh Zakzaky (H) Malama Zeenatu ke kiransa da shi, wanda a sakamakon haka sai da membobin zauren suka yi mata hadaya ta wuridin Salatin Annabi (S) dubu É—ari biyu da hamsin a matsayin tukuici.
Mai karatu, idan faÉ—in laÆ™abin Shaikh Zakzaky (H) na “Khaleel” kawai zai sa a yi wa mutum Salatin Annabi (S) kwata Miliyan a matsayin tukwici, to, lallai wannan mafificin shaida ne cewa duk wani abu da ke da alaÆ™a da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) albarkarsa ba ta da iyaka! Wani mawaÆ™i yana cewa; Mai albarka, É—an albarka, Al-Zakzakiyu kogin albarka!
TASIRINSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin zaÉ“aɓɓun bayin Allah Æ™alilan da Allah Ta’ala ya yi wa baiwar tasiri a zukatan al’ummar da yake rayuwa a cikinta, domin a fili yake cewa zantukan Shaikh Zakzaky (H) da ayyukansa ba Æ™aramin tasiri suke yi ga almajiransa da ma al’umma baki É—aya ba.
Misali; Tun bayan lokacin da mutane suka fahimcin cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana yin azumomin watanni uku masu alfarma (Rajab, Sha’aban, Ramadan) a jere, sai ya zamo É—imbin jama’a sun tasirantu da hakan, sun lizimci yin azumomin watannin a jere, duk da cewa Shaikh É—in bai taÉ“a umartar wasu da yin hakan kai tsaye ba, kuma abin bai tsaya ga almajiransa kawai ba, har da sauran jama’ar gari.
Haka nan, a ranar tunawa da waÆ™i’ar Ashura na shekarar 1434 Hijiriyya, wanda ya yi daidai da shekarar 2012 Miladiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sauka a motarsa ya yi tattaki da Æ™afafuwansa ba tare da takalmi ba daga Æ™ofar Doka zuwa babban masallacin Idi na Zariya. Ya yi wannan Tattaki ne akan kwalta kuma a lokacin ana tsananin zafin rana.
Wannan tattaki da Shaikh Zakzaky (H) ya yi ya zama wata Sunnah abin É—abbaÆ™awa ga almajiransa da dama, ta kai ga akwai waÉ—anda suke Tattakin Arba’een tun daga garuruwansu har zuwa Husainiyyah BaÆ™iyatullah Zariya, wanda tafiya ce ta kwanaki, amma ba tare da takalma a Æ™afafunsu ba, dan kawai koyi ga aikin jagora (H).
A wasu lokutan baya, Malam ya ziyarci garin Lokoja, inda ya ziyarci ƙaburburan wasu sarakunan Musulunci da Bature ya kai su garin Lokoja suka rasu a can, irin su Sarkin Kano Aliyu ɗan Abdullahi, da Sarkin Zazzau Aliyu ɗan Sidi, da su Sarki Kwasau da Sarkin Bida da na Gwandu.
“Sadda Malam ya je da farko duk waÉ—annan Æ™aburbura sun zama Bola da wurin kewayawa da gidajen É“era da burgu, an manta da su, musamman ma Sarkin Kano. To amma cikin hukuncin Allah zuwan Malam ke da wuya sai kowace masarauta ta tashi haiÆ™an da gyara maÆ™abartar Sarkinsu, misali, na Kano sun gine wurin, an yi azuzuwa, kuma an kewaye wurin da gini, mai buÆ™ata ya je ya gani.
“Na Zazzau su ma ba a bar su a baya ba, sun gina masallaci a wurin Æ™abarin Aliyu É—an Sidi, da wasu azuzuwa. Kafin ziyarar Malam Zakzaky waÉ—annan Æ™aburbura lallai an manta da su, don kafin mutum ya shiga wurin sai ya rufe hanci don wari da Æ™azanta. Wannan abu da na gani a Lokoja na sanya shi a cikin nasarorin Malam Zakzaky!” (Malam, Malam Ne, shafi na 36).
Tasirin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai tsaya ga almajiransa da sauran al’umma kaÉ—ai ba, hatta gwamnatin Nijeriya a wasu lokuta in ta fito da wani tsari da ya shafi al’umma wanda take so ta cimma nasarar aiwatar da shi, ba mutumin da take sauraron tsokacinsa akan shirin nata kamar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin da zaran ya yi magana akan abu, to al’ummar Æ™asa sukan samu waraka game da abin, idan ya kushe abin ko ya nuna illarsa, to al’umma za su bijirewa abin, gwamnati ba za ta taÉ“a iya cimma nasarar aiwatar da shirin ba (allrar Poliyo ta isa misali), amma idan ya yi shiru akan lamari, to, gwamnati kan samu Æ™arfin gwiwar aiwatar da shi. Wannan tasiri na Shaikh Zakzaky (H) ga al’umma yana É—aya daga cikin abin da ke É—agawa gwamnatin Nijeriya hankali, domin tana ganin ya za a yi a samu wani mutum ya fi hukuma tasiri ga al’umma?
Tasirin Shaikh Zakzaky (H) ya haifar da canje-canje da dama a sassa da É“angarorin al’umma masu yawa, kama daga É“angaren Malamai ta sashen wayewarsu, ‘yancinsu, da salon tsaronsu. Zuwa É“angaren É—alibai, talakawa da sauran É“angarori. Tasirin da Shaikh Zakzaky (H) ya yi a sassa na rayuwar jama’a ne ya sa manazarta ke cewa ya riga ya yi nasarar juyin juya hali “Ravolution” a Nijeriya.
A takaice, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi matukar tasiri a kowane fanni na rayuwar al’ummar Æ™asarsa, domin za ka ga jama’a suna matuÆ™ar koyi da shi a dukkan sassa na rayuwarsa, kama daga tsabtarsa, adonsa, zamantakewarsa da iyali, har ma da kwaikwayon salon kalmomi na maganarsa. Wannan tasiri da Allah Ta’ala ya ba Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana É—aya daga cikin abubuwa mafi muhimmanci da suke jan hankalin hukumomi da manazarta akan rayuwar Shaikh Zakzaky (H) da dalilan da suka sabbaba masa wannan tasirin.
RAHARSA:
Babu shakka, wasu mutanen da ke hangen Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) daga nesa, za su É—auka mutum ne mai kaushi da tsanani, amma ga duk wanda ya kusance shi, zai gane cewa shi mutum ne mai tsananin sauÆ™in kai da raha, ba yadda za a yi ka zauna tare da shi na tsawon mintuna 15 ba ka mance da duk damuwowin ka ba, domin mutum ne mai matuÆ™ar hikima da raha, duk inda ka gan shi a cikin jama’a muddin ba lokacin juyayi ba ne, to za ka ga annuri da alamar fara’a a fuskar duk na tare da shi, domin tabbataccen abu ne Shaikh (H) zai sanya nishadi da farin ciki ga kowa ta hanyar raha mai cike da ilimantarwa da hikima.
Shaikh Zakzaky (H) mutum ne mai saukin kai matuka, wani Fasto da ya taÉ“a kawo masa ziyara gida, bayan sun daÉ—e suna tattaunawa cikin raha da nishaÉ—i, sai ya ce; Gaskiya Malam yadda muke hangenka daga nesa ba haka kake ba, mu ba mu É—auka kana da sauÆ™in kai haka ba, da a musulmin Æ™asar nan na tsane ka fiye da kowa, amma yanzu na ji ina son ka fiye da kowa!”.
Shi kuwa Fasto Meter Peller na cocin Abuja, cewa Kiristoci ‘yan uwansa ya yi; “Kiran da zan yi ga al’umma da sauran Fastoci shi ne, ya kamata kowa ya buÉ—e Æ™ofa ga waÉ—annan jama’a (‘yan Shi’a almajiran Shaikh Zakzaky) don a fahimci juna, abin da ke tsakaninmu shi ne rashin fahimta, duk wanda ya nazarci kiran Malam (Zakzaky) to ba zai taÉ“a muzanta shi ba, dole ne ya yarda da kiran Malam! Wasu za su ji kamar ina siyasa ne ko wani abu mai kama da haka, amma (na tabbata) idan har suka samu ganawa da Malam, to lallai su ma sai sun zama ‘ya’yan Malam kamar yadda na zama!” (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1256, shafi na 08).
Marubucin littafin “Malam, Malam Ne” ya labarta cewa; “Wani É—an jarida, bayan saduwarsu da Malam ya ce; “(Wannan) ko cutar da Æ™uda ba zai iya ba” (He can hardly wound a fly)” (Malam, Malam Ne, shafi na 15). Wannan É—an jarida ya ga sauÆ™in kan Shaikh (H) ne da zurfin ilimi da fikirarsa.
WASIYYARSA:
Bisa al’ada akan ambaci Wasiyyar mutum ne bayan ya bar duniya, to amma babu laifi ga ambatar Wasiyyar mutumin da ke raye a duniya ma, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi buÉ—aÉ—É—iyar Wasiyya aÆ™alla guda biyu.
BuÉ—aÉ—É—iyar Wasiyyarsa ta farko ta faru ne a watan Ramadan na shekarar 1430 (2010), lokacin da rahoton sirri ya zo masa cewa an gama duk wani shiri na halaka shi a wannan dare da zai shigo, har ma ya samu kwafin takardar “BluePrint” da shugaban Æ™asa Umaru Musa Yar’aduwa ya sawa hannu na zartar da “Operation” É—in a wannan dare.
Shaikh Zakzaky (H) ya yi Wasiyya ga É“angarori uku na al’umma, ya yi Wasiyyar gargaÉ—i ga azzalumai, ya yi Wasiyyar juriya ga almajiransa, ya yi Wasiyyar farkawa ga al’ummar musulmi, sa’annan a Æ™arshe ya yi albishir ga almajiransa, ya ce; “Ba zan Æ™arÆ™are maganar nan ba sai na yi muku albishir, ko an Æ™i ko an so addinin Allah zai tabbata! Ba yadda za a yi a ce wai bakin bindiga ko bom zai tarwatsa Da’awa zuwa ga Allah!”
Wasiyya ta biyu ta Shaikh Zakzaky (H) ita ce wacce ya yi wa ‘ya’yansa uku da suka rage a duniya, wato Sayyid Muhammad, Sayyida Nusaiba da Sayyida Suhaila, a ranar da sojoji suka kai hari gidansa, suka kashe kusan mutum dubu daga almajiransa, kuma suka kashe ‘ya’yansa maza uku, da babbar Yayarsa, suka harbi matarsa, shi ma suka yi masa ruwan harsashi, da yake bai É—auka zai rayu ba, ya yi keÉ“antacciyar Wasiyya ga ‘yarsa Sayyida Suhaila wacce yake tare da ita a lokacin.
Ta ce, daga cikin Wasiyyarsa gareni ya ce; “In kula da Sallah, sannan mu É—au fansar abin da aka yi mana, kar mu Æ™yale abin da aka yi mana ya tafi (a banza), kar mu yi shiru akan abin da aka yi mana. Sannan in yi hakuri, in kalli rayuwar Sayyida Zainab (SA), in yi haÆ™uri irin nata, in yi rayuwa irin yadda ta rayu. Ya yi batun komawa makaranta, yana wannan halin ya riÆ™a Æ™arfafamu ni da Sajida akan muhimmancin ci gaba da karatunmu, ya ce in mun rayu mu tabbata mun koma makaranta, kar mu ce ba za mu koma ba, kar mu tsayar da komai namu dan abin da ya faru, amma kar mu Æ™yale abin ya tafi a haka nan (siddan)” (Jaridar Al-Mizan, bugu na 1240).
Jumlatan a waÉ—annan Wasiyyoyi na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shiryar da al’umma ne a cikinsu, za mu ga yadda ya yi Wasici da kula da Sallah, da dagewa da neman ilimi, da rayuwa tare da ruhin gwagwarmaya da zaluncin azzalumai.
0 Comments