Babi Na Hudu

Babi Na Hudu

BABI NA HUDU


WASU SASSA NA RAYUWAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

TAFIYE-TAFIYENSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashe masu yawa a sassa da dama na duniya, kusan ma ba wani sashe na duniya da bai je ba, kama daga Asiya, Turai, da ƙasahen Afirka. Misali, a yankin Asiya ya je ƙasashe kamar su; Iran, Iraƙi, Saudi Arabiyya, Dubai, Lebanon, Malesiya da sauransu. A ƙasashen Afirka kuwa ya je Sudan, Ghana, Saliyo, Mali, Habasha, Nijar, Kenya, Afirka ta Kudu, Libiya da sauransu. Sannan ya je manyan ƙasashen duniya masu tinƙaho irinsu Birtaniya, Amurka, Rasha, Faransa da sauransu. Dukkanin waɗannan tafiye-tafiye ya yi su ne ta hanyar gayyata bisa dalilai na addini, ko halartar tarurrukan ƙarawa juna ilimi.

“Haka nan in muka dawo nan cikin gida za mu ga cewa Sayyid Zakzaky (H) ya je birane da Æ™auyuka masu yawa a cikin Æ™asar nan don isar da wannan Da’awa da yake yi, kai mutum ma zai iya dukan Æ™irji ya ce a jihohin Æ™asar nan musamman ma na arewawacin Æ™asar, to, ba jihar da bai je domin isar da wannan saÆ™o na Allah Ta’ala ba” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 23).

ALAƘARSA DA AL’UMMAH:
  1. MUSULMI: Abu ne sananne ga kowa cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fi kowane malami a Nijeriya kyakkyawar alaÆ™a da sauran musulmin da ba fahimtarsu É—aya ba, domin ko kaÉ—an ba ya Æ™yamar musulmi na kowace Mazhaba ko AÆ™ida, hasali ma ya fi kowa jin zafi bisa rashin jituwar da ke tsakanin Æ™ungiyoyin musulmi. Kullum a cikin sa’ayi na haÉ—a kan musulmi yake, damuwarsa ita ce, aÆ™alla musulmi su yarda su dena aibata juna da sukan juna da kafirta junansu. Daga cikin Æ™oÆ™arin Shaikh Zakzaky (H) na haÉ—a kan musulmi ya sunnantawa kansa da almajiransa ziyarar Malamai na Æ™ungiyoyin musulmi daban-daban, daga lokaci zuwa lokaci Shaikh (H) yakan tashi takanas ya je gidajen manyan malamai ya ziyarce su don neman kusanci da fahimtar juna.
  2. Sannan duk garin da ya je don wa’azi ko halartar wani taro, yakan je ziyara ta sada zumunci da neman kusanci da fahimtar juna ga manyan malamai na garin, yakan ziyarci malamai ne mabanbanta na Æ™ungiyoyin musulmi. Sannan ya hana almajiransa warewa ko gina masallatansu na Æ™ashin kansu, don hakan zai Æ™ara kawo rarraba da farraÆ™a ne a tsakanin musulmi, wannan ya sa duk inda almajiran Shaikh Zakzaky (H) suke, suna Sallah ne a masallatai na al’ummar musulmi, kuma a bayan limamai na waÉ—annan sassan musulmin, tattare da cewa suna riÆ™o ne da tafarkin Ahlul-Bait (AS) wato Ja’afariyyah.

  3. KIRISTOCI: Ko ba a faÉ—a ba duniya shaida ce game da kyakkyawar alaÆ™ar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Kiristoci da ma sauran mabiya addinai a Nijeriya, domin in banda Shaikh (H) ba wani malami da Kiristocin Nijeriya ke yabawa salon Da’awarsa kamarsa. Ƙungiyoyin Kiristoci daban-daban sun sha rubutawa Shaikh Zakzaky (H) takardar yabo da godiya bisa gudunmawar da almajiransa suka ba su, na tseratar da rayukansu, ko na kariya ga dukiyoyinsu ko ga wuraren kasuwancinsu a lokutan rigingimun addini ko na Æ™abilanci ko na siyasa.

A wurin Shaikh Zakzaky (H) hanya mafi dacewa ta yin jihadi ga Kiristoci ita ce hanyar isar musu da saƙon musulunci na haƙiƙa ta kyakkyawar hanyar da za su fahimta su gamsu, ba wai ta hanyar hantara ko far musu da kisa ko ƙona dukiyoyi da wuraren ibadarsu dan kawai sun zaɓi su zama kiristoci ba.

MUTUNTAWARSA GA MATA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne alami mafi girma na ‘yancin mata da tausaya musu a wannan al’umma ta wannan nahiya, domin ya kawo gagarumin sauyi akan yadda al’ummar wannan nahiya suka É—auki mata, da yadda suke kallonsu, da irin mu’amalar bawa da maigidansa da ke gudana a tsakanin mata da mazajensu. Sannan a gefe guda Shaikh Zakzaky (H) ya yaÆ™i munanan al’adu na Æ™asÆ™anta mata da mayar da su haja ta biyan buÆ™ata kawai. Wanda ya san rayuwar Bahaushe da iyalinsa, da yadda Shaikh (H) ya kawo sauyi a cikinta ne kawai zai iya fahimtar abin da muke faÉ—a.

A matakin farko, Shaikh Zakzaky (H) ya darajta mata ne ta hanyar koya musu sanya suturar Musulunci (Hijab), wanda kafin Da’awarsa ba a san sanya hijabi a wannan nahiya tamu ba. Daga nan sai ya fito da su daga zaman dirsham na hidimar mazaje a gidajensu, zuwa fagen addini da sa’ayi kafaÉ—a da kafaÉ—a da maza wajan neman yardar Allah da gwagwarmayar ceto al’umma, wanda kafin Da’awarsa, a wannan nahiya tamu an manta cewa mata suna da wata damar bada gudunmawa a harkokin addini. Albarkacin Da’awarsa ne har mata suka samu damar riÆ™e sifika su yi wa’azi, suka samu ‘yancin yin karatu suna gidajen aurensu, wanda kafin Da’awarsa an takura damar matan aure ta yin karatu da neman ilimi a makarantu.

Shaikh Zakzaky (H) ya bada gudunmawa sosai ta hantar mutunta mata da raya darajarsu a cikin al’ummar Hausawa ta aÆ™alla fuskoki uku;

  1. NA FARKO: Ya kare su daga yawan saki barkatai ba tare da bin Æ™a’ida ba, domin a wani jawabin da yake matuÆ™ar nuna damuwarsa game da yadda maza ke yawan sake mata ba bisa Æ™a’ida ba a Nijeriya, Shaikh Zakzaky (H) ya taba cewa; “Da ina da iko, to da na sa wata Æ™a’ida a sakin aure, idan mutum zai saki matarsa, sai an sa rana, ya buga katin gayyata ya raba, an yi ta sanarwa a gidan rediyo, cewa wane É—an wane, ya sa ranar kaza ga watan kaza a matsayin ranar da zai aikata abin nan da Allah Ta’ala ke Æ™i, wato Saki! A taru kamar yadda ake É—aura aure, mai shela ya yi shela cewa; Ga wane É—an wane, ba tare da jin kunyar Allah ba, ba tare da jin kunyar Manzon Allah (S) da Mala’uku da Muminai ba, zai aiwatar da abin nan da Allah ba ya so, wato zai saki matarsa!

  2. NA BIYU: Ta É“angaren aure ma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya Æ™arawa mata kima da daraja a wajan maza, domin kuwa a bisa al’ada, a Nijeriya da Æ™asashe maÆ™wabtanta ana biyan kuÉ—i ‘yan Æ™alilan ne a matsayin sadakin mace, kai akwai ma al’adar bayar da ‘ya mace kyauta ko sadaka ga namiji ya aureta ba tare da wata wahala ko É—awainiya ba, hatta sadakinta ma ubanta ne ke biya masa, shi kawai a siddan za a kawo masa matar!
  3. Wannan al’ada ta tsananin arhar aure ta haifar da matsaloli masu yawa a zamantakewar auren al’ummarmu. Na farko ta haifarwa auren rashin kima, ta yadda an mayar da shi kamar wasa, daga mace ta É—an saÉ“awa miji ko da bisa kuskure ne sai kawai ya saketa, domin ya san zai samu wata sabuwa cikin sauÆ™i. Na biyu kuma hakan ya sabbabawa mazaje auren mata barkatai, alhali ba sa kiyaye haƙƙoÆ™in matan kamar yadda musulunci ya tanada, hakan ya taimaka Æ™warai wajan jefa mata cikin halin tagayyara da Æ™aÆ™anikayi a gidajen aurensu.

    Don taÆ™aita wannan mummunar É—abi’a ta wulaÆ™anta mata, sai Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya raya sunnar biyan Sadaki mai kima ga mata, don aÆ™alla mace ta samu darajtawa daga namiji, kuma hakan ya rage yawan saki barkatai ba tare da bin Æ™a’ida ba, sannan ya taimaka wajan daÆ™ile tara mata rututu ba tare da kiyaye haƙƙoÆ™i da dokokin Shari’a ba.

  4. NA UKU: Shaikh Zakzaky (H) ya tarbiyyantar da al’umma (musamman almajiransa) dangane da tausayawa iyayen ‘ya mace, ya nuna cewa; Idan iyaye suka haifi ‘ya mace, sukan kula da rayuwarta da tarbiyyarta baki É—aya, su yi ta É—awainiyar ciyar da ita, tufatar da ita, kula da iliminta da lafiyarta da sauransu har ta girma. To kuma in an zo batun aurenta, sai iyayen sun sha wata baÆ™ar wahala ta kashe magudan kuÉ—i, wani lokaci ko iyaye ba su da hali sai sun ci bashi sun yi É—awainiya.

Dan haka, kamata ya yi su masu neman aure, su riÆ™a tausayawa iyayen yarinya suna hutar da su daga manyan É—awainiyoyi a lokacin biki. Ma’ana, ya zamo wanda zai auri mace ya biya sadaki mai kima sosai, wanda zai isa iyaye su yi wa mace duk abin da ake buÆ™ata a gidan mijinta, sai ya zama a Æ™alla iyaye ba su riÆ™a wahala sosai a lokacin aurar da ‘ya’yansu mata ba, an taimakawa iyaye kenan wajan hutar da su daga É—awainiya mai galabaitarwa a lokutan bikin ‘ya’yansu mata.

Madalla da wannan darajtawa ta Shaikh Zakzaky (H) ga matan al’ummar nahiyarsa, madalla da wannan cigaba da ya samarwa mata, kuma madalla da wannan hutu da ya nemawa iyayen ‘ya’ya mata !

TAUSAYINSA GA MATA:
Shaikh Zakzaky (H) mutum ne mai matuÆ™ar tausayawa mata bisa halin da suka samu kansu a wannan al’umma tamu, yana yawan nuna damuwarsa game da cutar da mata da mazaje ke yi. Kullum yakan yi kira ga maza da su riÆ™a tausayawa mata, su dena cutar da su, su dena bautar da su, su riÆ™a musharaka da su cikin ayyukan gida, su riÆ™a biya musu buÆ™atunsu na rayuwa, su riÆ™a kyautata musu har su shagwaÉ“a su.

A wani jawabinsa na “Ranar Mata ta Duniya” wato “Makon Zahrah”, ya yi nasiha ga mazaje da su shagwaÉ“a matansu ta hanyar tsananta kyautata musu, a ciki yake cewa, maza su riÆ™a sayawa mata gwalagwalai na ado, in suna son mota ku saya musu, in suna son zuwa Hajji ku kai su, duk abin da suke so ku yi musu, ya ce idan maza suka yi wa matansu haka, sai kuma ya zamo matan sun nuna butulci, to a lokacin shi kuma zai yi wa matan faÉ—a ya ba su rashin gaskiya.

Kullum Shaikh yakan tausayawa ‘yan uwa mata idan ya wuce ya gansu akan titi suna tafiya da Æ™afa za su je wurin taro, musamman idan wurin taron da nisa, wani lokaci ma har tsayar da tawagar motocinsa yake yi ya umarci matan da ke tafiya a Æ™afa da su shiga a rage masu hanya, in kuma suna da yawa yakan cire kuÉ—i ya ba su ya ce su hau Tasi.

Wani É—an uwa ya bada labarin yadda Shaikh Zakzaky (H) ya taÉ“a taimakawa wata mace mai ciki tun a shekarun baya, ya ce; “Ina da wasu dangi a cikin garin (Zariya), kullum suna gargaÉ—i na game da bin Malam Zakzaky (saboda shi Shi’a ne). Ran nan sai kawai na ji mahaifiyar mai gidan ta ce ita ma ta zama ‘yar Shi’a, na ce meye dalili?

Sai ta ce “Ai ran nan É—aya daga cikin ‘ya’yanta mata sun dawo daga unguwar Ban Zazzau (a cikin garin Zariya), ga goyo kuma ga ciki ruÆ™u-ruÆ™u, (tana tafiya da Æ™yar da wahala), sai Malam ya zo wucewa a motarsa Bitil, ya tsaya ya É—auko ta da É—anta har zuwa kusa da gida. Ta ce yana tuÆ™i sai karatun AlÆ™ur’ani yake… Wannan shi ne dalilin É—aura É—amarar neman sai ta koyi karatun Ƙur’ani ta iya kuma ta haddace shi” (Wakilin Manzo (S) a Doron Ƙasa, Juz’i na É—aya, shafi na 26).

Tausayin Shaikh Zakzaky (H) ga mata bai taÆ™aita ga mata ma’abuta addini ba, hatta mata masu zaman kansu Shaikh (H) yakan tausayawa rayuwarsu Æ™warai, “Akwai lokacin da na ji yana cewa, lokacin da yana zaune a kurkukun Kaduna, yana sauraron BBC sashen Hausa, sai ya ji ana tattaunawa da wasu ‘yan mata musulmi, waÉ—anda suka maida fasiÆ™anci a matsayin sana’a, suka ce kuma da abin da suke samu ne suke É—aukar É—awainiyar kansu da ma na iyayensu, shi ne Sayyid (H) ya ce da ya ji hirar, saboda tausayinsu sai da ya zubar da hawaye” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 31).

HIDIMA GA IYALANSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana da hali irin na Manzon Allah (S) na taimakawa iyali a ayyukansu na cikin gida da hidimta musu, domin ya kasance yana yi wa iyalinsa wanki da guga, yana É—iba mata ruwa ya cika randuna, yana sharar É—aki da gyara shinfiÉ—ar kwanciyarsa da kansa, kuma yana dafa abinci ga iyalansa.

A wata hira da ‘yan jarida, uwargidansa Malama Zeenatu ta shaida musu cewa; “Ƙila kuna da labari cewa; Malam yakan girka abinci da yin sauran ayyukan gida. Tunda muka yi aure muna raba aiki ne ni da shi, ba wai komai ni nake yi ba, bilhasali ma wasu abubuwan shi yake mani, kamar wanki, (guga), da sauransu, sai ya ce in tara kayana in sun yi datti, shi sai ya wanke… kuma yakan ce kar a taÉ“a masa girkinsa, wato in yana girki ba ya so a sa masa hannu, ya fi so ya yi abinsa ya gama” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 41).

A wani jawabi Malama Zeenat tana cewa; “Shi (Malam) bai yarda mu ce komai mu za mu yi, shi ba zai yi ba, kuma Malam bai taÉ“a cewa in ba shi kaza ba, bai taÉ“a cewa É—auko min kaza ba, kai ba ma ni ba, har yaransa ba ya aikensu, har da su Zainab (Hameed) in za su gyara masa É—aki, to sai in ya fita za su shiga su gyara. Bai taÉ“a ce mun É—auko min kaza ba, ko bani ruwa ko menene ba, shi kawai yana so ya yi komai da kansa ne” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 128).

Haka nan Malama Zeenatu ta taÉ“a bayyanawa ‘yan uwa mata misali na hidimar da Shaikh Zakzaky (H) yake mata hatta a cikin barcinta, ta ce; “Kun ga ni mai yawan jin zufa ce, waÉ—anda muke tare sun sani, kuma ana yawan É—auke wuta, kuma idan aka É—auke wuta ba mu kunna AC da Janareto, don kar mu matsa masa, sai dai mu kunna fanka. To, duk lokacin da NEPA suka kawo wuta zai zo ya kunna min AC, ya kulle min windo, sannan ya koma (É“angarensa), wani lokaci yana komawa sai a Æ™ara É—auke wuta, shi kuma ba shi da nauyin barci, ko canza wuta aka yi yana tashi, sai ya zo ya kunna min fanka, ya kashe AC É—in, ya bubbuÉ—e windunan, kuma har yanzu yana yin hakan. Sannan kuma da abubuwa da dama, wanda mutum zai yi mamaki (in ya ji su)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 129).

Shi ma Shaheed Sayyid Ahmad É—aya daga cikin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ya faÉ—i yadda Shaikh É—in ya rene shi tamkar uwa, wato yana masa duk wata hidima da É—awainiyar da uwa ke yi wa É—anta, ciki har da reno da sauransu. Ya ce; “Da yake ni ina da Æ™ani, sai ya zama an haife shi shekara É—aya bayan an haife ni, sai ya zama ni an yaye ni tun kafin lokacin da ya kamata ya zama an yaye ni, sai ya zama Umma tana ji da Æ™anina, sai ya zama ni kuma Abba ne yake ji da ni, sai ya zama da wanka da duk wasu abubuwa da ka san uwa tana yi wa yaro, to ni Abba ne yake min, har ya zama na fi sabawa da shi Abban fiye da Umman” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 55).

Malama Maryam Sani, wacce makusanciya ce ga Malama Zeenat (uwargidan Shaikh Zakzaky) tana cewa; “Malam har girki yana yi (a gidansa), da yawanmu in ana wani “Programme” mun sha cin girkin Malam. Akwai ma lokacin da wata Yayata ta zo guna, amma sai ta sauÆ™a a gidan Malam, sai ta ga malam ya shiga kicin ya yi wanke-wanke ya dafa abinci, aka kawo musu suka ci, ba ta ga Malama (matar Malam) ta shiga kicin É—in ba ma, da ta komo take ce min ashe haka malaminku yake? Wannan ba Æ™aramin tasiri ya yi mata ba” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 196).

Ita ma Malama Maimunatu Abdullahi (uwargidan Shaheed Shaikh Muhammad Turi), ta labarta yadda Shaikh Zakzaky (H) ke hidimar gida ga iyalansa, ta ce; “Shi Malam rayuwarsa ta sha banban da yadda ‘yan uwa suke… Malam yana girki, sannan yana kula da ‘ya’yansa. Akwai wani É—ansa ma da yakan kwana a É—akinsa, shi ne yake kula da shi, ya yi masa wanka da sauransu, ko kuma idan ana goyon yaro Malam yakan fito falo wurin ‘yan uwa ya canza masa nafkin, ya yi masa tsarki, ya nuna ma ‘yan uwa yadda ake wanke nafkin, da yadda ake saka shi… (Mun taÉ“a ziyartar Malam a gidansa) Sai muka samu yana girki, ya É—ora miyar taushe da tuwon shinkafa, har ma ya dafa mana shayi (muka sha), sai muka ga duk al’amuran da Malam ke yi addini ne” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 206).

Wannan shaida ta iyalan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa, game da hidimar da yake wa iyalansa na ayyukan cikin gida da reno da kula da sauransu, babbar shaida ce ta koyi da halayyar Annabi (S) da Shaikh Zakzaky (H) ke da ita. Kuma a gefe guda, hakan na nuna karamci da maÉ—aukakan halaye da É—abi’unsa managarta, lallai rayuwar Shaikh Zakzaky sanfur ce ga al’ummah.

KARANTARWARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne da ya yi fice a fagen karantarwa, domin bai da aiki a rayuwarsa face karatu da karantarwa ga É—imbin É—alibansa. Yana da tsarin karantarwa na dindindin a É“angarori biyar, kama daga tafsirin AlÆ™ur’ani mai girma, karatun Nahjul-Balagah, karatun Daurori, da kuma Muhadharorin da ya saba gabatarwa a kusan ko da yaushe.

Tunda farko dai, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya assasa Harka Islamiyyah ne akan karantarwa ta gina fikira da kyawawan É—abi’un musulunci. Wannan karantarwa wacce ake kira ‘TA’ALIM’, ta cikinta ne ake sanin jauharin manufa da hadafin Harka Islamiyyah, ita ce asasi ko matakin farko da ake so kowane É—an Harka Islamiyyah ya bi ta kai kafin isa ga sauran karatuttukan Shaikh (H).

TAFSIRIN ALƘUR’ANI: Shaikh Zakzaky (H) yana gabatar da tafsirin AlÆ™ur’ani mai girma a kowace ranar Laraba ta mako, wato yana da zaunannen tsari na yin tafsirin AlÆ™ur’ani wanda ba wani abu da ke sa ya É—age tafsirin in ba tafiya Æ™asar waje ya yi ba, hatta a lokutan gudanar da taruka da suke É—aukar tsawon mako guda ana aiwatarwa, akan ware ranar Laraba a matsayin ranar tafsirin AlÆ™ur’ani ne a jadawalin, haka nan, ko ana ruwan sama ba ya É—age tafsirin sai ya gudanar da shi.

Salon tafsirin Shaikh Zakzaky (H) ya sha banban da na dukkan malamai, misali; A tafsirin AlÆ™ur’ani na farko da ya yi, tun daga “Suratul Fatiha” har zuwa “Suratun-Nass”, ya yi shi ne a salon Tarjama, inda ya riÆ™a gabatar da taÆ™aitattun bayanai game da ma’anonin ayoyin AlÆ™ur’ani ba tare da kawo ra’ayoyin masu tafsiri ko saÉ“aninsu ba.

Amma da ya zo zagaye na biyu na tafsirin, sai ya rika yin tafsirin a bisa doron bayanan Ahlis-Sunnah game da ma’anar ayoyin, wato idan ya karanto aya, sai ya yi tafsirinta ta mahangar Shi’a, sa’annan sai ya karanto tafsiri ko ruwayoyi da zantukan malamai da jagororin Ahlis-Sunnah da suka dace da wannan fassara ta Shi’a.

Sa’annan, da ya sake dawowa zagaye na uku na tafsirin, sai ya zamo a wannan karon, yana tafsirin ne kawai da zallar ruwayoyi da hadisai na Ahlul-Bait (AS), da kuma zantuka da fahimtar jagorori da malaman Shi’a (Radhiyallahu Anhum). Wannan ya nuna wata baiwa ta Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na IhaÉ—ar iliminsa da kuma salon da yake bi wajan shiryar da al’umma.

NAHJUL BALAGAH: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana gabatar da karatun littafin “Nahjul-Balagah” a duk ranar Litinin ta kowane mako, shi ma karatun “Nahjul-Balagah” kamar na tafsirin AlÆ™ur’ani ne, ba abin da ke kawar da shi sai in tafiya Æ™asar waje ne.

A wannan karatu na “Nahjul-BalagahShaikh Zakzaky (H) yana faÉ—aÉ—a bayanai sosai, tare da zurfafawa wajan hallale ma’anoni na kalmomin da littafin ke Æ™unshe da su, kuma yakan zo da littattafai daban-daban dan faÉ—aÉ—a bayani ko Æ™ara bada haske kan wani abin da yake magana akansa, wannan ya sa zuwa yau an kwashe tsawon shekaru da dama Shaikh É—in bai iya kaiwa ga sauke littafin ba har yanzu.

DAURAR AMIRAI: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana gudanar da karatu mai zurfi a fannonin ilimummukan addini da dama tare da manyan almajiransa daga lokaci zuwa lokaci, shi tsarin wannan karatu da ake kira “Daurah”, ya keÉ“anta ne kawai ga manyan almajiransa, musamman wakilan ‘yan uwa na manyan Da’irori, da sashen masu wasu Mas’uliyya a Harka Islamiyyah, da makamantansu.

Shaikh Zakzaky (H) yana gudanar da wannan karatun Daurah ne ga manyan almajiransa duk bayan wata uku, kuma yakan shafe makwanni uku ne yana musu karatun a keɓe, a lokacin Daurar akan tattauna tare da zartar da muhimman shawarwari.

DAURAR ‘YAN UWA MATA: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yakan gudanar da irin wancan karatun Daurah ma ga ‘yan uwa mata masu Mas’uliya a Harka Islamiyyah. Ita ma wannan Daurah ta ‘yan uwa mata akan gudanar da ita ne tsawon makwanni uku, kuma akan shigeta ne da zarar an kammala ta ‘yan uwa maza, wakilan ‘yan uwa mata daga dukkanin Da’irori na faÉ—in Æ™asar sukan halarta.

MUHADHARORI: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana gabatar da Muhadharori masu yawan gaske a rayuwarsa, kusan a kullum ba ya rasa gayyata ta gudanar da wata Muhadhara a wani taro, sannan a gefe guda yana da zaunannun Muhadharorin da yake gabatarwa shekara-shekara. Kamar zaman makokin Ashura na tsawon kwanaki 50, da Muhadharar Yaumu-Arba’een, da wafatin Manzon Allah (S), da Maulidin Shaikh Usman bin Fodiye, da Maulidin Manzon Allah (S), da Wafati da Maulidin Sayyida Zahra (SA), da Maulidin Imam Ali (AS), da Yaumul-Mab’ath, da Nisfu-Sha’aban, da Wafatin Amirul-Muminin (AS), da Dahwil-Ardh, da Eedul-Ghadeer da sauransu.

Sannan a kullum yana cikin gabatar da Muhadharori ga Lajanoni da É“angarorin Harka Islamiyyah, da halartar Mu’utamarori, da zuwa taruka da sauran gayyace-gayyacen da ake masa a ciki da wajan kasa. A takaice, waÉ—annan abubuwa suna daga cikin aikace-aikace da hidimar yaÉ—a ilimi da koyarwar addini da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke gudanarwa a rayuwarsa.

WALLAFE-WALLAFENSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai yi fice a fagen rubuce-rubuce da wallafe-wallafen littattafai ba, wataƙil hakan yana da alaƙa da yawan ayyukansa da ƙarancin samun dama da lokaci na zaman yin rubuce-rubucen. A wata magana da ya taɓa yi game da wallafa, ya yi ishara cewa a kowane fage da kowane fanni an yi ɗimbin rubuce-rubuce masu kima da gamsarwa, sun wadatar wajan sanin duk abin da ake neman masaniya a kansa, wataƙil wannan falsafa ce ta sa Shaikh (H) ya fi maida hankali wajan tafiyar da lokutansa ga ibada fiye da zaman yin rubutu.

Amma tattare da haka, Shaikh Zakzaky (H) ya rubuta littattafai guda uku da hannunsa, É—aya na Turanci, É—aya na Larabci, É—aya kuma na Hausa, littattafan su ne;-

THE MISSION OF MAN ON EARTH”, wato “Manufar Halittar ÆŠan Adam a Bayan Ƙasa”.

TARIHIN ZAZZAU” wato “The History of Zazzau”, wanda yake rubutawa da harshen Hausa.

AD’IYAATU NAWAFILIR-RAMADAN” wato “Addu’o’in Nafilfilin watan Ramadan” wanda ya rubuta da Larabci.

A cikin waÉ—annan littattafai guda uku, É—aya ne aka samu damar kaiwa ga É—ab’insa, wato “Ad’iyaati Nawafilir-Ramadan”, sauran biyun zuwa yanzu bai iya samun damar kammala rubuta su ba.

Amma a gefe guda, akwai É—imbin littattafan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) cikin harsunan Turanci da Hausa, wanda laccocinsa ne da yake gabatarwa a wurare da lokuta daban-daban ake rubutawa a maishe su littafi. Ba za mu iya ambatarsu gaba É—aya ba saboda yawa, amma daga cikin fitattun akwai; “Nasihohi ga ‘Yan Uwa Musulmi”, na daya zuwa na biyar, sai “Nijeriya Ina Mafita?” (wanda an ce har wani gwamna ya taÉ“a ba shi lambar yabo akan wannan littafin), sai “Rayuwar Imam Khumain (QS)” da sauransu.

Sannan akwai jerin laccocin da yake yi a ranar tunawa da Shahidai “Yaumus-Shuhada”, wanda kowace lacca ana mayar da ita littafi É—auke da sunan “Shahada Maganin Mutuwa”, akwai kuma laccocin da yake gabatarwa a zaman makokin Ashura da ake mayar da su littafi É—auke da sunan “Jawaban Ashura”, akwai laccocin da yake gabatarwa ga matasan Harka Islamiyyah a lokutan taronsu na shekara-shekara, wanda ake mayarwa littafi É—auke da sunan “Zuwa Ga Matasa”, akwai laccocin da yake gabatarwa a makon tunawa da Imam Khumain (QS), wato “Imam’s Week” da ake mayar da su littafi É—auke da sunaye daban-daban.

Akwai laccocin da yake gabatarwa a ranakun Maulidi da ake mayar da su littafi É—auke da sunan “The Meassage”, akwai jerin laccocin da yake gabatarwa a wa’azozin dare a garuruwa, da laccocinsa na rufe tarukan Mu’utamar, da laccocinsa na tarukan Æ™arawa juna ilimi da ake mayar da su Æ™ananan littattafai ana rabawa jama’a a bisa kulawar cibiya mai suna “Cibiyar Wallafa da YaÉ—a Jawaban Shaikh Zakzaky”, akwai ma jerin littattafai na zaÉ“aɓɓun zantukansa da ake tattarawa wuri guda ana maishe su littafi da dai sauransu.

HAUSARSA:
Harshen Hausa shi ne yaren da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke magana da shi a rayuwarsa ta yau da kullum, duk da cewa yana jin harsuna aƙalla huɗu, wato Hausa, Turanci, Larabci da Fulatanci.

Kamar yadda aka sani, Shaikh Zakzaky (H) É—aya ne daga cikin bayin Allah waÉ—anda Allah Ta’ala ya yi wa baiwar faÉ—aka da lura da la’akari cikin komai na rayuwa, domin hatta a furuci Shaikh (H) yana anfani ne da zaÉ“aɓɓun kalmomin Hausa a jawabai da mu’amalolinsa, ba kawai yakan yi anfani da kalmomin da ya ji Hausawa suna furtawa ba ne, a’a, kafin Shaikh ya yi furuci da wata kalmar Hausa sai ya tantance ma’ana da kamalar kalmar, wato yakan yi anfani ne kawai da kalmomin da suka dace da koyarwar addini da tarbiyya.

Kullum Shaikh (H) a faÉ—ake yake kan Hausar da yake furtawa. A wasu lokuta yakan yi magana kan rashin dacewar furta wasu kalmomi ko ‘Karin Magana’ na Hausa, a wasu lokuta kuma nazari da la’akari ne zai tabbatar maka cewa baya anfani da wasu kalmomi na Hausa. Ga ‘yan misalai akan haka;-

DODO GUDA SUKE YI WA TSAFI: Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana” a yayin da yake magana kan mutanen kirki, ko ma duk wani musulmi mai aÆ™idar Tauhidi, wataÆ™il kai ma za ka iya fahimtar rashin dacewar anfani da kalmar in ba ga maguzawa ma’abuta tsafi ba.

RIGA MALAM ƘALU-BALE: Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana” a yayin da yake so ya kushe gaggawar wasu mutane, domin riga Malam zuwa masallaci abu ne mai kyau a musulunci, dan haka bai kamata a kushe yin hakan da “Karin Magana” ba.

ƘALU-BALE: Shaikh (H) ba ya nafani da kalmar Ƙalu-bale a yayin da yake so ya nuna ko ya yi wani “Challenge” ga wasu, domin in an bi zirin ma’anar ‘Ƙalu-bale’ za a taras kalmar ba ta da wani ma’ana in an kwatanta ta da ma’anar da aka É—orata a kai, yakan yi anfani ne da kalmar “Kule” a madadinta.

IN GEMUN ÆŠAN UWANKA YA KAMA DA WUTA, TO, KA SHAFAWA NAKA RUWA: Wannan “Karin Magana” ma Shaikh (H) ba ya anfani da ita, ya sha faÉ—i cewa karin maganar bai dace ba, domin musulunci yana Æ™arfafa ‘yan uwantaka ne da taimakon juna. Don haka, in gemun É—an uwanka ya kama da wuta, kamata ya yi ka kawo masa gudunmawar ruwa ka taya shi kashewa, in kun kashe wutar, to, kai da shi duk sai ku shiga shafawa gemunan naku ruwa don kar wani a cikinku ya sake samun gobarar gemu! Amma in gemun É—an uwanka ya kama da wuta, sai ka ja gefe ka shafawa naka ruwa, ai ka nuna halin ko in kula gare shi da son kanka kenan, alhali musulunci ya yi hani ga hakan. Ko ba a lura ba?

SO DUK SO NE, AMMA SON KAI YA FI: Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana”, domin ya saÉ“awa karantarwar addinin musulunci. Hafizahullah ya nuna cewa cikar imanin mutum shi ne ya so wa É—an uwansa abin da yake so ga kansa, ayar AlÆ™ur’ani a “Suratul Hashr” Aya ta 9 ta nuna cewa mumini cikakke shi ne wanda zai hana kansa ya baiwa É—an uwansa abin da yake so. Sannan musulunci ya haramta son kai, dan haka wannan karin maganar ya saÉ“awa koyarwar addini, domin yana koyar da son zuciya ne da handama. Shaikh (H) ya canza wannan “Karin Magana” da wani sabo, inda yake cewa “So duk so ne, amma son É—an uwa ya fi”.

WAL-BANI WAL-BAKA, WAL-HANANI WAL-ƘEMEME: Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana”, domin ya saÉ“awa koyarwar addini. Wannan karin maganar yana koyawa mutane rowa ne da son kai a fakaice, don yana cewa ne, in mutum yana baka abin hannunsa, to, kai ma sai ka riÆ™a ba shi naka, in kuma yana hana ka na shi, to, kai ma kar ka ba shi naka ko da yana cikin matuÆ™ar buÆ™ata!

A Hadisai da yawa Manzon Allah (S) ya yi umarni ga musulmi cewa; “Ka rika yin kyauta ga mai yi maka rowa, ka rika kyautatawa mai munana maka”, dan haka karin maganar “Wal-bani Wal-baka…” ya saÉ“awa karantarwar addini. Shaikh (H) ya canza wannan “Karin Magana” da wani sabo, inda ya ce; “Wal-bani wal-baka, Wal-hanani Wal-baka!”. Ko ba a lura ba?

IN KA YI MUN KAN KARA, ZAN MAKA NA ITACE: Shaikh Zakzaky (H) ba ya cewa azzaluman da suke cutar da shi, “Duk wanda yai mana kan kara, za mu yi masa na itace”, domin yin hakan ya saÉ“awa karantarwar addini. Addini bai hana ramuwa ba, amma ya hana wuce gona da iri akan ramuwa. In aka yi maka wani abu to ya halasta ka rama daidai yadda aka yi ma ne, amma É—aukar fansa fiye da laifin da aka yi maka laifi ne a musulunci, kuma yin hakan ne abin da wannan “Karin Magana” ke koyarwa.

YA TAKA MUHIMMIYAR RAWA: A yayin da Bahaushe ke so ya bayyana girman gudumawar da wani ya bayar, yakan ce; “Wane ya taka muhimmiyar rawa a abu kaza”. Sheikh (H) ba ya anfani da wannan karin maganar, domin taka rawa ba wani abu ne kyakykyawa a musulunci ba, sannan ko a al’adance ma mutum mai kima da daraja ba ya rawa, dan haka bai kamata a kwatanta wani abu maras kima ga wani mutum mai daraja da kima ba, maimakon “Ya Taka Rawa”, Shaikh (H) yakan ce “Ya Bada Muhimmiyar Gudunmawa” ne, ko ba lura ba?

Post a Comment

0 Comments