BABI NA BIYAR
RAYUWAR SHAIKH ZAKZAKY (H) A KANGIN AZZALUMAI
GWAMNATOCIN DA SUKA DAURE SHI:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sha kamu da É—auri a hannun hukumomin Nijeriya, an sha kama shi da azabtar da shi da É—aure shi a lokuta daban-daban, ya zuwa yanzu hukumomin Nijeriya sun kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) har sau 10, kuma jumlatan shekarun da ya yi a tsare sun doshi shekaru 15. Ya zauna a gidajen kurkuku na jihohin Nijeriya daban-daban, daga ciki ya zauna a kurkukun Zariya, Kaduna, Sakkwato, Inugu, Fatakwal, Lagos da Abuja, kuma an sha tsare shi a wuraren azabtarwa da bincike, daga ciki akwai inda ake Æ™ira “Interrogation Center” a Lagos, da kuma wuraren tsaro na musamman na jami’an leÆ™en asirin DSS a Abuja.
Bisa abin da ke tabbace a zahiri, daga lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara Da’awarsa a shekarar 1980 zuwa yanzu, mafi yawan gwamnatocin Nijeriya sun É—aure shi a gidan yari, wasu gwamnatocin ma sun masa É—auri ko kamu fiye da É—aya, yayin da wasu gwamnatocin ke gadar ci gaba da É—aure shi da gwamnatocin da suka gabace su suka yi.
Gwamnatin soja ta Janar Olusegun Obasanjo ta tsare shi a shekarar 1979 a Zariya, ta kuma sake kama shi a Sakkwato ta tsare a farkon shekarar 1981.
Gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari ta kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta É—aure shi tun daga wajajen tsakiyar shekarar 1981 zuwa 1984.
Gwamnatin mulkin Soja ta Janar Muhammadu Buhari, ta ɗaure Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a wajajen ƙarshen shekarar 1984.
Gwamnatin mulkin Soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ta É—aure Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1987 zuwa 1989.
Gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta sake kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1992.
Gwamnatin mulkin kama karya ta Janar Sani Abacha ta ɗaure Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1996 zuwa ƙarshen shekarar 1998.
Gwamnatin mulkin danniyar farar hula ta Muhammadu Buhari, ta kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta tsare shi a ƙarshen shekarar 2015 wanda har zuwa rubuta wannan littafi a farkon shekarar 2017 ba a sake shi ba.
JADAWALIN KURKUKUN DA YA YI:
Ga tsarin gidajen kurkukun da Shaikh Zakzaky (H) ya yi, da daÉ—ewar da ya yi cikin kowannensu;
| S/N | Gwamnati | Shekarar Kamu | Shekarar Saki | Gidan Yari |
|---|---|---|---|---|
| 01. | Gen. Olusegun Obasanjo (Soja) | 30th May, 1979 (4 Rajab, 1399h) | 10th June, 1979 (14 Rajab, 1399h) | Ofishin Ƴan Sanda A Zaria |
| 02. | Gen. Shehu Shagari (Farar Hula) | 15th April, 1981 (11 Jimada Thani, 1401h) | 15th May, 1984 (14 Sha'aban, 1404h) | Kurkukun Sokoto Kurkukun Inugu |
| 03. | Gen. Muhammad Buhari (Soja) | December 1984 (Rabi'ul Auwal, 1405h) | 1st September, 1985 (16 Zulhijja, 1405h) | N.S.O Kaduna I.C Legas Kurkukun Ƙiri-ƙiri |
| 04. | Gen. Ibrahim B. Babangida (Soja) | 28th March, 1987 (28 Rajab, 1407h) | 28th November, 1989 (30 Rabi'us Thani, 1410h) | Kurkukun Kaduna Kurkukun Suleja Kurkukun Fatakwal |
| 05. | Gen. Ibrahim B. Babangida (Soja) II | November 1991 (Jimada Ula, 1412h) | Kwanaki Shida | N.S.O Kano Kurkukun Legas |
| 06. | Gen. Sani Abacha (Soja) | 12th September, 1996 (29 Rabi'us Thani, 1417h) | 18th December, 1998 (29 Sha'aban, 1419h | Mopol H.Q, Kaduna Kurkukun Fatakwal Kurkukun Kaduna |
| 07. | Muhammad Buhari (Farar Hula) | 14th December, 2015 (3 Rabi'ul Auwal, 1437h) | 28th July, 2021 (18 Zulhijja, 1442h) | DSS H.Q, Abuja DSS Kaduna Kurkukun Kaduna |
Bisa wannan jadawali, za mu ga cewa gwamnatocin Soja ne suka fi yawan kamawa da tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), kuma zuwa yanzu an tsare Shaikh (H) a wuraren tsarewa aÆ™alla goma sha bakwai, daga cikin tsarewar da aka masa, an taÉ“a tsare shi a “Dungeon” wani wurin tsarewa na Æ™arÆ™ashin Æ™asa wanda mutum ba ya iya banbance dare da rana.
A wata hira Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “(An tsare mu) a wani wuri wanda yake shi wannan wurin ba akan gane dare ko rana ba, amma wani lokaci akan fito da mu (dan suna yarda mutum ya yi wanka sau É—aya a mako), sai a fito da mutane wajan su hamsin duk a wuri É—aya, a sa musu bokitai (su tuÉ“e su yi wanka), sai su ga ni ban fito ba saboda suna yin tsirara, har wani ya ce mun; kai ba za ka yi wankan ba ne? Sai na yi masa shiru, sai ya ce; oho, don kai musulmi ne ko? To, sai ya yarda ni in dinga yin wankana ni kaÉ—ai” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 16).
Saboda tsabar tsarewar da aka yi ta yi wa Shaikh Zakzaky (H), an haifi uku daga cikin ‘ya’yansa ne a lokutan da yake tsare a gidajen kurkuku, misali, an haifi É—ansa Muhammad ne yana kurkukun Kirikiri a Lagos, an haifi Nusaiba yana kurkukun Kaduna, an haifi Hammad yana kurkukun Fatakwal. An sha azabtar da shi da nau’o’in azaba a kurkuku, wanda wasu azabobin har yanzu tasirinsu yakan motsa a jikinsa daga lokaci zuwa lokaci.
YUNƘURIN KASHE SHI:
Bisa lura, za mu ga an samu tazara mai yawa ta kimanin shekaru 17 (1998-2015), (wato tun fara aiwatar da mulkin farar hula na jamhuriya ta uku) ba a kama Shaikh Zakzaky (H) ba sai a Æ™arshen shekarar 2015, wanda wasu ke ganin kamar an Æ™yale shi ne; “A a, sun lura ne cewa duk kame-kamen da aka yi wa Sayyid Zakzaky a baya, ya daÉ—a haÉ“aka abin da yake kira akai ne. Bisa asasin haka, sai suka ga cewa wannan kamun da É—auri bai da wani anfani ga manufarsu, saboda haka sai suka canza salo da kuma makirci.
“Wannan sabon salon shi ne yunÆ™urin kashe Sayyid Zakzaky (H). Shi ya sa in muka duba a cikin waÉ—annan shekaru da aka samu tazara na rashin kama Malam, babban abun da suka sa ma gaba shi ne kashe Malam É—in ko ta halin Æ™aÆ™a! Za mu ga sun yi Æ™ulle-Æ™ulle da makirce-makirce iri-iri domin su cimma wannan manufa tasu, amma Allah Ta’ala bisa ikonsa duk ya wargaza shirin nasu!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 22).
Misali; Shugaban Æ™asar Nijeriya a Alhaji Ummaru Musa Yar’adua a shekarar 2008 ya bada umarnin kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) cikin mako uku, amma sai Allah Ta’ala ya tona asirin shirin, wanda daga Æ™arshe ya wargaje sakamakon kamuwa da mummunar jinyar da Yar’aduwan ya yi, wacce ta yi ajalinsa cikin Æ™anÆ™anin lokaci.
Bayan mutuwar Yar’adua, sai aka rantsar da shugaban Æ™asa Goodluck Ebele Jonathan, sai shi ma ya É—ora a inda Yar’adua ya tsaya kan batun kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), inda jami’an tsaron gida da haÉ—in gwiwar na Æ™asashen waje (musamman Amurka da Isra’ila) suka duÆ™ufa ka’in da na’in na ganin sun kashe Shaikh Zakzaky (H). Sun yi ta tsara hare-hare da nufin kashe shi a hanyarsa ta zuwa Hussainiyyah BaÆ™iyatullah ko a gidansa ko a hanyarsa ta zuwa wa’azi wani gari, amma Allah Ta’ala ya riÆ™a wargaza duk Æ™ulle-Æ™ullen nasu yana ba shi kariya, har ta kai ga a cikin duhun wani dare na shekarar 2012 sun zo da wani jirgin sama da zai yi ‘Bombing’ É—in gidan Shaikh Zakzaky (H), amma Allah ya hana su ganin gidan, suka yi ta shawagi suka koma.
Haka nan, a shekarar 2012 gwamnatin Jonathan ta ba fitaccen kamfanin kisan kai (Assasins) na wani shararre kuma Æ™wararren makashi mai suna Patrick Williams kwangilar kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Kanfanin mai mazauni a Amurka kwararre ne a fagen kashe mutane a duniya. Lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu labarin wannan shiri, ya yi jawabi ga É—imbin jama’a a filin Idi na birnin Zariya lokacin rufe muzaharar maulidi ta 17 ga watan Rabi’u Auwal na shekarar 1433. A ciki yake cewa, “Na farko, kai Patrick Williams sai in ce maka ‘Raina yana hannun Allah ne ba yana hannunka ba ne!’ Kuma Allah Ta’ala na yi imani da shi, ya ce “Ba ya yiwuwa ga rai ta mutu sai da izinin Allah, abu ne yankakke rubutacce!”.
Haka nan, a farkon shekara 2015, Æ™wararrun ‘yan ina da kisa daga cikin sojojin Amurka da aka É—auko hayarsu musamman don kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), sun É—ana masa tarko a hanyar zuwa Hussainiyya inda ya saba gabatar da Tafsiri, amma sai Allah Ta’ala ya aiko da ruwan sama mai tsanani ya wargaza shirinsu.
ƘOƘARIN HALAKA SHI A KURKUKU:
A wasu kurkukun da aka tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) an yi ta haɗa shi da ƙwararrun makasa da masu shaye-shaye da mahaukata, (duk dai dan su kashe shi, sai su kuma hukumomi su fake da cewa hatsaniya ce ta haɗa shi da wani a kurkukun suka yi faɗa har ya kai shi ga rasa ransa).
Misali; A kurkukun Sakkwato, an haÉ—a shi da wani Æ™wararren É—an ta’adda, wanda kuma É—an sanda ne na ‘Mobile Police’, wanda shaye-shaye ya juyar masa da Æ™waÆ™walwa, ana kiransa Jasper, Æ™ato ne Æ™aƙƙarfa. Da Shaikh Zakzaky (H) yake magana game da Jasper ya ce; “Ya taÉ“a É—aukar AlÆ™ur’aninmu haka, sai muka ce masa; kai AlÆ™ur’ani ne, sai ya wurgar! Kuma sai ya kama gilas É—in ido na wani É—an uwa da bai gani sosai, kafin ka ce haka ya mutsuttsuka shi ya watsar… kuma sai kawai ya malala fitsari (a cikin É—akin da muke), kuma in ya doki bango sai ka ji ya yi motsi! Haka dai Allah ya kiyaye mu, amma mun zauna tare da shi a É—aki É—aya” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 16).
Shaikh Zakzaky (H) ya sake bada labarin wani mahaukaci da aka haÉ—a su zama a wani kurkuku, ya ce; “Haka kuma wata rana aka zo da wani tuburan, ina ga shi mahaukaci ne ma tuburan sosai É—aure cikin sarÆ™a a Æ™afafunsa, …To, haka dai (muka zauna) ya yi ta haukatakunsa, har kashinsa yana ci, sai ya É—auko fo wai zai yi kashi ya ci in gani, sai na ce masa in ka kuskura zan mangareka, to, sai na nuna masa nima mahaukaci ne, na ce masa ina fasa kan mutane! To, sai ya ji tsoron fasa kai É—in, to yadda na Æ™waci kaina kenan, daga baya dai Alhamdulillah aka É—auke shi, ban san inda aka kai shi ba”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 17-18 da Tasarrufi).
A kurkukun Fatakwal kuwa, an haÉ—a Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a É—aki É—aya da wani Æ™wararren É—an ina da kisa na CIA, Ba’amurke ne baÆ™ar fata, yana kiran kansa “Jew” wato Bayahude, amma a kurkukun suna ce masa Tony ko Sony, kuma ya daÉ—e a hukumar ta CIA yana aiki, har ma ya tsufa. Ya yi aikin leÆ™en asiri da na kisan kai a Æ™asashen duniya da dama, a wata hirarsu ya faÉ—awa Shaikh Zakzaky cewa; Bari in gaya maka gaskiya, ni an bani kwangila na kashe mutane da yawa, kuma har yanzun akwai waÉ—anda aka ce in kashe su, kuma zan kashe sun!” Shaikh Zakzaky (H) ya ce; Ko saboda ni suka kawo shi, wallahu’a’alamu, to in ma don ni ne Allah Ta’ala dai ya hana shi (zartar da mummunar manufarsa), bai samu cimma burinsa ba” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 19-20, bisa taÆ™aitawa).
AZABTAR DA SHI:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fuskanci jarabawowi na azabtarwa a hannun azzaluman mahukunta a lokuta daban-daban a tsawon wannan Da’awa tasa ta Harka Islamiyyah. Za a iya wallafa manyan littattafai akan zallar azabtarwar da ya sha da irin jarabawowin da ya fuskanta a hannun hukumomin Nijeriya, amma bari mu É—an yi tsokaci kawai a matsayin misali.
Duk da cewa Shaikh Zakzaky (H) ma’abucin tsabta ne da tsananin Æ™in datti da dauÉ—a, amma da aka kama shi a Sakkwato cikin shekarar 1981 aka tsare, an hana shi yin wanka da wanki na tsawon makwanni masu yawa, a wani jawabinsa yana cewa; “Lokacin da muke tsare a Sakkwato, an haÉ—a mu Sel guda da mahaukaci, an buÆ™atar da mu ga rashin wanka na makwanni, wankanka shi ne ka É—auko hannunka ka mulmula dauÉ—a ka jefar, muka yi makwanni a haka, ba wanka ballantana wanki, riga ba ta sawuwa sai dai na dole”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 213).
A wani misali da yake bayarwa na jarabawar da ya fuskanta a gidajen kurkukun ya ce; “An buÆ™atar da ni tare da wasu ‘yan uwa da muke tsare ga Æ™warÆ™wata a jiki tare da kuÉ—in cizo, ko’ina ka shafa a jikinka kuÉ—in cizo ne da Æ™warÆ™wata, har ta kai ma lokacin da aka kai ni kurkukun Inugu sai da aka yi min aski Æ™walkwabo, domin duk Æ™warÆ™wata ta cinye kan! Kuma an buÆ™atar da ni zama da faÉ—e (takalma irin na danÆ™o), ina ta yi masa faci har shekara uku, kuma an buÆ™atar da ni a kurkukun Inugu in yi wanka ba sabulu har tsawon wata shida, kuma ba man shafawa, har jini na ketowa (a jikina saboda bushewar fata)” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 214).
Sannan an tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a kurkukun Kirikiri dake Legos tsawon watanni, shi Kiriri wuri ne na azabtarwa da sunan bincike, akwai karikitai na azabtarwa iri-iri a wurin. Shaikh Zakzaky (H) ya ce ko sauro ka kashe a Kirikiri sai an yi maka bulala, wai kana kashe yaran gwamnati, kuma hatta tufafi riga da wando ba a yarda mutum ya shiga da su ba, sai dai a shigar da mutum daga shi sai Pant.
Lokacin da aka kai Shaikh Zakzaky (H) suka ce ya tuɓe tufafinsa, ya ce wannan kam ba zai yiwu ba, dole da tufafinsa zai shiga, su kuma suka ce bai isa ba! suka kama shi da kokawa za su tuɓe masa tufafi da ƙarfin tsiya, kawai sai jinsa ya yi a cikin ɗakin tare da tufafinsa, dole suka haƙura suka ƙyale shi da tufafin, har waɗanda ya samu a cikin wurin suna ta mamaki, shi kansa Shaikh Zakzaky (H) yana cewa yana ganin shi ne mutum na farko da ya shiga Kirikiri da tufafi a jikinsa.
A Kirikirin akwai wani sashen azabtarwa na musamman, wanda sel ne a Æ™arÆ™ashin Æ™asa, a wajan ba a gane banbancin dare da rana, wuri ne mai tsananin duhu, wanda ko tafin hannunka ba za ka iya gani ba, a cikin wurin aka cusa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na tsawon lokaci, Shaikh (H) ya bada labarin wurin a wata laccarsa, ya ce; “A wancan lokacin yadda na riÆ™a yi nike gane lokutan Sallah shi ne; Suna kawo abinci da rana, in za su kawo abincin to gab da Azuhur suke kawowa, to in na ci da yake kofin ruwa guda É—aya ne za a ba mutum, to sai in sha rabi in yi Alwala da rabi.
“To, sallar Magriba yadda nike gane ta shi ne, in an kawo abincin yamma, saboda galibi sukan kawo (abincin) gab da Magriba ne, to jim kaÉ—an sai in yi sallar Magriba. To, sallar Asuba ba yadda za a yi in gane, yadda nikan yi wani lokaci (shi ne), in na yi sallar Asuba bisa tsammanin ta yi, sai in zauna in yi ta yin Azkar har lokacin da suka zo da safe suna Æ™wanÆ™wasa Æ™ofa suna tambayar mutum nawa ne cikin wannan É—akin, to Æ™arfe bakwai ne suke wannan, to sai in yi ‘Estimate’ (in Æ™iyasta) daga lokacin da na zauna zuwa yanzu an yi awa nawa? To wani lokaci sai ta bayyana na yi sallar asubar ne Æ™arfe ukku na dare, ko ma Æ™arfe É—ayan dare” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 136).
Haka nan a waÆ™i’ar Maulud ta 2015 wadda sojoji suka kashe almajiransa kusan mutum Dubu kafin su kai gare shi, da suka isa É—akin da yake ciki suka yi masa ruwan wuta, harsashi ya farfasa jikinsa har sai da idonsa na hagu ya zazzago ya fito waje, shi ya kama idon ya mayar da kansa, idon dama kuma harsashi ya sauÆ™a a samansa shi ma ya samu matsala.
An yi masa harbi a wurare daban-daban aÆ™alla goma sha É—aya a jikinsa, suka É—auke shi ba rai suka tafi da shi, sai bayan kwana 4 Allah Ta’ala ya dawo masa da ransa ya farfaÉ—o. Tattare da cewa bayan tsawon lokaci ya yi ta samun sauÆ™in raunukan da aka masa, amma idonsa na hagu yana masa tsananin ciwo da zogi, ta kai ga ba ya iya karatun AlÆ™ur’ani saboda ba ya ganin rubutun, kuma a hakan gwamnati ta hana a fita da shi waje don yi masa aikin idon, burin da jami’an tsaro ke da shi shi ne lalacewar duk idanuwan nasa guda biyu.
Wannan kaÉ—an kenan daga gallazawar da Shaikh Zakzaky (H) ya sha a hannun azzalumai, a taÆ™aice, Shaikh Zakzaky (H) ya fuskanci jarabawowi na azabtarwa sosai daga É“angaren azzaluman mahukunta, sun sha kama shi da É—aure shi da gallaza masa ta hanyoyin azabtarwa daban-daban, amma tattare da haka bai taÉ“a saranda ko miÆ™a musu wuya ba, hasali ma Æ™arin yaÆ™ini da sabati yake samu akan abin da ya sa a gaba na ceto al’umma daga Æ™angi.
YUNƘURIN KASHE SHI:
Allah ne kadai ya san iya yawan yunƙurin da aka yi ta yi na kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a lokuta da wurare daban-daban, kama daga yunƙurin kisan gilla na zahiri zuwa kisa ta hanyar sihiri da tsatsuba. A matsayin misali, ga jerin yunƙurin kisan da aka yi masa wanda suka bayyana a zahiri.
- NA FARKO: YunÆ™urin kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) karo na farko da ya bayyana shi ne wanda aka shirya shi tun Shaikh É—in yana É—alibta a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, wato farko-farkon Da’awarsa, wanda aka shirya yin anfani da wasu É—alibai da za su je É—akin da yake cikin dare su kashe shi, an samu labarin wannan shiri ne daga wani É—alibi mai suna Alpha Bolaji.
- NA BIYU: Yunƙurin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin Ibraheem Babangida ta yi a lokacin da aka kai shi Kirikiri a 1992, lokacin an shirya za a yi masa kwaf ɗaya ne kawai a gama da shi, to amma sai Allah ya wargaza shirin, sai suka sake shi da gaggawa.
- NA UKU: YunÆ™urin kashe Shaikh Zakzaky (H) da ‘yan Tawayiya suka yi, bayan sun rutsa shi a masallacin Jami’ar Bayero dake Kano, a shekarar 1994.
- NA HUÆŠU: YunÆ™urin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin Abacha ta yi a shekarar 1996 a kurkukun Kaduna, inda aka shirya kashe shi ta hanyar allurar mutuwa kamar yadda aka yi wa Janar Shehu Musa Yar’adua a lokacin.
- NA BIYAR: YunÆ™urin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin farar hula ta Ummaru Musa Yar’adua ta yi a shekarar 2010, wacce ta tsara “Bombing” É—in gidan Shaikh da kashe duk waÉ—anda ke cikin gidan, an samu kwafin “BluePrint” ne na umarnin yin hakan.
- NA SHIDA: YunÆ™urin kashe shi da hukumar CIA ta Amurka ta yi a ranar bikin cikarsa shekaru 63 a duniya cikin shekarar 2014, wanda suka turo Æ™wararrun makasa jar fata rufe da fuskokinsu da “Mask” irin na “Ku Klu KlaÉ—”. Suka É“oye a hanya da nufin aiwatar da mummunan nufinsu, amma sai
Allah Ta’alaya aiko da ruwan sama mai tsanani ya rusa shirinsu. - NA BAKWAI: YunÆ™urin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin Ebele Jonathang ta yi ta yi a shekaru biyunta na Æ™arshe (2013-2015), wanda a Æ™arshe suka yi nasarar kashe ‘ya’yansa uku a shekarar 2014 a madadin gagararsu kasuwa da ya yi.
- NA TAKWAS: Yunƙurin kashe shi da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi a ƙarshen shekarar 2015, wanda ya janyo kashe almajiransa maza da mata kusan mutum Dubu da ke ba shi kariya, da kuma yi masa ruwan harsashi a goshinsa da kirjinsa da cinyoyinsa a ƙoƙarinsu na halaka shi, amma
Allahya raya shi da ikonsa.
Waɗannan sune yunƙure-yunƙuren kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da aka sha yi, wanda suka bayyana a fili ƙarara kamar hasken rana, wanda duniya ta shaida kuma ake da dalilai da hujjoji na zahiri a kansu. Amma kamar yadda muka faɗa a baya, ba suke nan ba, yunƙurin kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Allah ne kaɗai ya san iyakarsa, mun ambaci fitattu ne kawai a matsayin misali.
0 Comments