BABI NA UKU
ALAKAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) DA YAWAN IBADA
IBADARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bawan Allah ne mai tsananin ibada, mutum ne da duk wanda ya san shi ya shaide shi da yawan ibada musamman salloli da azumomi da Azkar da yawan zuwa aikin hajji da umrah (kafin kafircin duniya ya sa shi a tarko). Yakan ce, awa 24 na yini da kwana sun yi masa kaÉ—an, da da yiwuwar a Æ™ara da zai so haka, ya ce “Duk duniya ba abin da ya kai Sallar dare daÉ—i, da azzalumai sun san daÉ—in da muminai suke ji (a Tahajjud), da sun ce ba su yarda (a riÆ™a yi) ba!” (Malam, Malam Ne, shafi na 07). Bari mu ambaci ‘yan misalai na yawan ibadarsa a fagen Sallah, Azumi, Hajji da sauransu.
SALLOLINSA:
A fagen sallolin nafilfili Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tun yana Æ™arami ya lizimci yin “Nawafilil Yaumiyyah” wato nafilolin da ake yi tare da kowace sallar farilla kafinta ko bayanta. Wato duk wanda ya san Shaikh Zakzaky (H), ya san shi da yin Nafilfilin dare (Tahajjud) raka’a 13, Nafila raka’a 8 kafin Azahar, raka’a 8 kafin La’asar, raka’a 4 bayan Magriba, raka’ar Wateera bayan Isha’i, in an haÉ—a da raka’o’i 17 na sallolin farilla guda biyar, zai zama kenan a kullum Shaikh (H) yana yin Sallah Raka’a 51 a Æ™alla.
Wannan banda keÉ“antattun Salloli na kowane dare da na kowane yini da yake yi, kuma banda raka’a biyun da yake wa iyayensa, da raka’a biyu ga ‘ya’yansa, da raka’a biyu hadiyya ga shahidai, wannan a kowane dare ne, kuma banda salloli na musamman a ranar Juma’a da ranakun Idodi da sauransu. Kenan, a kowane wata Shaikh Zakzaky (H) dubban raka’o’i yake yi na sallar Nafila.
Sannan yana yin keÉ“antattun nafilfili na dararen watanni uku a jere (Rajab, Sha’aban, da Ramadan) kamar yadda aka ruwaito su a littattafan ibada, sannan yana yin keÉ“antattun salloli na darare na musamman a kowane wata.
Lokacin da ya saba tashi don yin sallar Tahajjud shi ne Æ™arfe 2 na dare, wannan shi ne “Normal Time” É—insa a kullum, É—aya daga cikin manyan almajiransa yana cewa; “Ta É“angaren Mujahada kuwa, wannan kam ko yau daren nan ko gobe, Malam Æ™arfe biyu na dare ya tashi, kuma ba zai kwanta ba har sai bayan rana ta fito, ni ban san iyakar shekarun da ya É—auka yana yin wannan ba” (Malam Zakzaky, Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 08).
Amma a darare masu falala da alfarma ta musamman (kamar daren Juma’a, dararen haihuwar Ma’asumai (AS), dararen Mab’ath, Dahwil-Ardh, Nisfu-Sha’aban, Ghadeer, da kusan gaba É—ayan dararen watan Ramadan), ba ya ma bacci kwata-kwata a cikinsu. (Tasarrufi daga Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 07).
Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Yana da yawan Sallah, musamman da dare, kai barcinsa in ma yana yi, to fa kaÉ—an ne, sau da yawa za ka ji yana cewa; “Rabo na da barci tun kwana kaza”, ya ambaci wasu kwanaki” (Malam, Malam Ne, shafi na 08).
Shaikh Zakzaky (H) yana da wata alaÆ™a ta musamman da Sallah, domin a rayuwarsa ba abin da yake son yi kamar Sallah, na taÉ“a ji a wata ziyara da aka kai masa yana cewa; “Da za a tambayeni, me ka fi so? Zan ce Sallah! Da kuma za a tambaye ni, me ka fi jin daÉ—insa, zan ce Sallah!” wannan da kunne na na ji Shaikh (H) yana faÉ—in haka. Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Akwai wani mutumin Iran da ya ga Malam Zakzaky (H) yana Sallah, ya ce; “Wannan yana Sallah irin ta Annabawa da Waliyyan Allah” daga nan suka shaÆ™u da Malam” (Malam, Malam Ne, shafi na 08).
Za ka tabbatar da alaÆ™ar Shaikh Zakzaky (H) da Sallah in ka karanta labarin waÆ™i’ar Maulud ta 2015, cewa, duk ruwan wuta da sojojin Nijeriya ke yi suna kashe almajiransa (a lokacin da suke Æ™oÆ™arin isa gare shi don kashe shi), shi ba abin da yake yi a falonsa sai Sallah. ‘Yarsa Sayyida Suhaila tana cewa; “Daga lokaci zuwa lokaci ana sanar da mu abubuwan da ke faruwa, mu kuma sai mu shiga mu sanar da Abbah (Shaikh Zakzaky) haÆ™iÆ™anin halin da ake ciki, da yawan lokaci in na shiga sai in tarar Abbah yana Sallah, sai in sanar da Ummah akan in ya yi sallama ta faÉ—a masa” (Al-Mizan, bugu na 1240).
AZUMINSA:
A fagen Azumi, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ginu akan lizimtar Azumin Litinin da Alhamis na kowane mako, (tun daga watan Shawwal zuwa Æ™arshen Jimada-Thani), kenan yana yin Azumi 77 na waÉ—annan raneku. Sannan yana azumin kwanaki tara na farkon watan Zulhajji, kuma yana yin azumin baki É—ayan watanni uku a jere, wato Rajab, Sha’aban da Ramadan, kenan yana yin azumin kwana 90 a jere.
Shaheed Hafizu Dauda (É—aya daga cikin masu rakiya ga Shaikh Zakzaky), ya faÉ—i cewa, “A bisa al’ada, in Shaikh (H) zai gabatar da Muhadhara (jawabi) yakan zo da ruwan shansa, in ba mu gan shi da ruwa ba, to mun san a ranar yana azumi. To, kuma mun lura, daga ranar É—aya ga Muharram ba ya zuwa wurin zaman makokin Ashura da ruwa har sai ranar Arba’een (20 ga Safar) muke ganin ya zo da ruwan sha a tare da shi”. Wato yakan yi azumin watan Muharram baki É—aya (in banda ranar Ashura), da kuma kwanaki 20 na Safar, jimilla yakan yi azumin kwana 49 kenan a jere.
Sannan yana yin Azumi na dukkan ranakun haihuwar Ma’asumai 14 (AS), yana kuma azumtar muhimman ranakun idodi na shekara, irinsu ranar Mubahala, ranar Ghadeer, ranar Mab’ath, ranar shinfiÉ—a Æ™asa, ranar Nuzuri da sauransu. Jumlatan, a kowane kwanaki 360 da ke cikin shekara, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana azumtar tsakanin kwanaki 230 zuwa 260 a cikinsu. Kenan, in dai Shaikh Zakzaky (H) yana zaune a gida ba tare da tafiya karatu ba, yana azumi aÆ™alla na sama da wata takwas a cikin watanni 12 na shekara.
Ƙanin Shaikh Zakzaky (H) wato Malam Badamasi YaÆ™ubu yana cewa; “Na san Malam (tun) sama da shekaru 40 barcinsa Æ™anÆ™ani ne, kuma na san cewa tunda ya taso ya ga mahaifinmu yana yin azumin wata uku a jere, wato Rajab, Sha’aban, da Ramadan, (shi ma) tunda ya taso yake yi, kuma har yanzu Malam bai daina ba, tun kamar shekaru 40 da suka wuce yake yi, kuma har yanzu yana ci gaba da yi” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 64). A wani jawabi Malam Badamasi ya ce; Tun Shaikh Zakzaky (H) bai balaga ba yake azumin wata uku a jere.
Wani da suka yi zaman Fursuna tare da Shaikh Zakzaky (H), ya faÉ—i cewa; Lokacin da suka yi zaman gidan kurkuku, Malam ya kwashe wata tara cur yana Azumi, kuma abinci kimantacce yake ci!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).
KARATUN ƘUR’ANINSA:
A fagen karatun AlÆ™ur’ani za a iya cewa Shaikh Zakzaky (H) mutum ne na musamman, domin shi ba ya gajiya da karatun AlÆ™ur’ani, sai dai kawai sauran hidimomi su tilasta shi ya ajiye, uwargidansa Malama Zeenat tana cewa; “Na san a da (Shaikh) yana sauÆ™e AlÆ™ur’ani ne cikin kwana bakwai (wato mako guda)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 130).
Marubucin littafin “Tarihin Harkar Musulunci” yana cewa; “Sayyid (H) ya kasance mai yawan karatun AlÆ™ur’ani, akwai ma lokacin da yake cewa, lokacin da yake zaune a kurkuku, yakan so ya sauÆ™e AlÆ™ur’ani a Æ™asa da kwana uku, amma tunda Sunnah shi ne Æ™arancin sauÆ™a kwana uku ne, to yakan tsaya akan hakan” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 26).
Idan muka nazarci wannan magana ta Shaikh Zakzaky (H) za mu ga zurfin É—anfaruwarsa da karatun AlÆ™ur’ani mai girma, domin yana cewa ne, da ba don Sunnar Annabi (S) ta koyar da mu sauÆ™e AlÆ™ur’ani cikin kwana uku zuwa sama ba, to da shi zai riÆ™a sauÆ™e AlÆ™ur’ani ne a Æ™asa da kwana ukun, wato a kullum zai riÆ™a sauÆ™e AlÆ™ur’ani, amma tunda abin da Sunnah ta koyar kwana uku ne, to ya tsaya a haka!
ADDU’ARSA:
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ma’abucin yawan addu’o’i ne, ya yi imani da addu’a fiye da komai a rayuwarsa, komai nasa sai ya yi addu’a kafin ya yi shi da bayan kammala shi. Yana bin dukkanin ladubba na karanta addu’a akan komai, kama daga addu’o’in Alwala, wanka, bacci, sanya sutura, zama, tashi, hawa abin hawa da komai na rayuwarsa.
Sa’annan ya lizimci yin addu’ar kowane dare, da addu’o’in ranakun mako, da addu’o’in kwanakin wata, da kuma addu’o’i na musamman a wasu lokuta na musamman, ko a wasu fitattun ranaku masu alfarma. Ya wallafa littafi ma na nafila raka’a dubu da addu’o’insu na musamman da ake yi a watan Ramadan, mai suna “Ad’iyaati Nawafilir Ramadan”.
Shaikh Zakzaky (H) ya yi fice wajan yawan karanta sashen addu’ar nan ta Iftitah daga daidai “Allahummah Innaa Narghabu Ilaika Fiy Daulatin Kareemah…” zuwa Æ™arshen addu’ar, da kuma addu’ar Sabati da IstiÆ™ama ta “Yaa Allahu, Yaa Rahmanu, Yaa MuÆ™allibal Ƙuloub Thabbit Ƙalbiy Aladeenika”, da sauran addu’o’in tuba da na neman shiriya da taimako ga Allah, sannan ya lizimci yin addu’ar “Allahummah wa Ƙadshamalana Zaigul Fitan” a AlÆ™unut É—insa na Sallah.
A fagen addu’o’in murÆ™ushe kaidin azzalumai da ganin bayansu kuwa, Shaikh Zakzaky (H) ya yi amanna da addu’ar “Al-Ƙamah”, da addu’ar “Sahmul-Lail” da addu’ar “Ahliththugour” da kuma addu’ar “ÆŠairal Ababeel”. Sannan yana yawan karanta addu’o’in halaka azzalumai musamman na Imam Zainul Abidin (AS).
Shaikh Zakzaky (H) yana da yawan addu’o’in alkairi ga almajiransa, malamansa, iyayensa, al’ummar musulmi da kuma Shahidai, duk wanda ya san Shaikh ya san ba abin da yake roÆ™on a yi masa sai Addu’a, saboda zurfin imaninsa da ita.
MUJAHADARSA:
Mujahada na nufin Æ™oÆ™arin ko wani Æ™arfin hali na musamman a fagen ibada. Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mujahidi ne na musamman a fagen ibada, domin banda yawan ibadar da yake da, a gefe guda kuma yana da naci da dagewa a tsawaita ibadar, wato ba ya hanzari ko shaf-shaf a lokacin ibada, yakan tsawaita tsayuwar karatu, da Ruku’u, da Sujjada da sauransu a tahujjud É—insa.
Misali; Shaikh Zakzaky (H) ya shafe shekaru masu yawa yana aiwatar da dukkanin azumin watan Ramadan a Haramin Makka ko masallacin Annabi (S) da ke Madina, wato duk shekara yakan tafi Umrah tun a cikin watan Sha’aban, ba ya dawowa sai bayan Sallah (Idil-Fitr), yakan shafe gaba É—ayan watan Ramadan ne a cikin masallacin Harami, ba abin da yake yi sai ibada.
Wani mutum ya labarta yadda ya ga ibadar Shaikh Zakzaky (H) a masallacin Annabi (S) dake Madina. Akwai wani ginshiÆ™i a cikin Raudha na masallacin Madina da ake Æ™ira ginshiÆ™in Abu-Lubaba, anan Shaikh Zakzaky ke zama ya yi ta ibada, lokacin da mutumin ya ga Shaikh a wurin, sai ya yi ta zuwa sawu-sawu dan yana so ya samu damar yin magana da shi, amma duk sa’adda ya je wurin sai ya tarar yana ibada, hatta lokacin tsayawa cin abinci ma bai da shi, sai dai ya É—an ci Dabino ya sha madarar gwangwani ko É—an wani abu marar nauyi, amma ba ya fita waje don neman abinci.
Mutumin ya ce; “Wallahi duk sadda na je sai in iske shi yana Ruku’u, ko ya yi Sujjada, ko yana karatun AlÆ™ur’ani, sam ba ya zama haka nan (shiru), akwai ranar da na ga ya yi Sujjada da tsakiyar dare, har aka fara Æ™iran sallar Asubahi bai É—ago ba, har na yi tunanin in je in Æ™wanÆ™wasawa Askar su zo su É—auke shi ko ya rasu ne, (na yunÆ™ura zan je) sai na ga ya taso ya zauna ya maida nunfashi, a lokacin ba dan tsoron Askarawa ba da na ce “Labbaika ya Al-Zakzaky!” (Malam Zakzaky, Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 09).
Wani É—an uwa daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H) ya rubuta labarin mujahadar Shaikh É—in kamar haka; “Na daÉ—e ina samun matsaloli na rashin fahimta tsakani na da Babana, lamarin bai yi sauÆ™i ba sai da wata rana wani abokin Baban nawa ya dawo daga aikin Umrah, suna zaune suna hira sai ga ni na zo wucewa, sai na ji yana faÉ—a masa cewa; “Kai Alhaji, a wannan shekarar na ga shugaban ‘yan Shi’a (Shaikh Zakzaky) a Umrah, yana ibada kai ka ce Mala’ikan mutuwa ke jiransa, yana ibada ba ji ba gani, da ka gan shi sai ka ji so da Æ™aunarsa ta shigar maka rai” ya ci gaba da ba Babana labarin cewa “Larabawa sai zuwa suke zunÉ—ensa, ana faÉ—in ga wani baÆ™in fata yana ibada ganga-ganga, da wata irin baiwa wacce samunta sai a kundayen tarihi” sai na ji Babana ya yi shiru, daga lokacin ya fara canzawa, yana saurare na da hujjojina” (Wakilin Manzo (S) a Doron Ƙasa, juz’i na É—aya shafi na 26-27).
Daga cikin Mujahadar Shaikh Zakzaky (H) akwai cewa, shi ba ya umartar wani da yin wani aiki na ibada har sai wannan aikin ya zamo jiki a wurinsa. Misali; a lokacin da ya fara yi wa almajiransa magana akan falalar yin Sallah Raka’a É—ari a wasu darare masu alfarma, irinsu daren Nisfu Sha’aban da dararen “Layaliyal Ƙadari” da sauransu, to shi ya fi shekara goma yana yi. Haka nan, sai da ya shafe sama da shekara goma yana yin sallar nafilar nan mai raka’a Dubu ta tsakanin Magriba da Isha’i a watan Ramadan, kafin ya sanar da ‘yan uwa muhimmancin yin wannan Sallar, har ma ya wallafa É—an Æ™aramin littafi na yadda ake yin sallar da addu’o’inta.
Sannan tarihi ya nuna cewa shi ne mutumin da ya raya I’itikafi a aikace a Æ™asar nan, kafin tasowarsa ana karanta batun I’itikafi ne kawai a littattafan fiÆ™ihu, amma ba a san wani mutum na shiga I’itikafi ba. Kenan, a sama da Æ™arni guda da ya gabata Shaikh Zakzaky ne ya fara shiga masallaci ya yi I’itikafi tun yana yaro É—an shekaru 15, daga nan sannu a hankali yin I’itikafi ya bazu a cikin al’umma, yanzu yin I’itikafi ya zama jiki a wurin dukkan É“angarorin musulmin Nijeriya.
Yayar Shaikh Zakzaky Shaheeda Fatimah Yakubu (Goggon Ƙaura) ta faÉ—i cewa; Tun yana yaro yake shiga masallaci ya yi I’itikafi, tun 20 ga watan (Ramadan) sai Sallah yake fitowa. Ni dai ban san wani da yake shiga I’itikafi ba a lokacin sai shi” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 71).
0 Comments