Tambaya Da Amsa Karo Na 6

Tambaya Da Amsa Karo Na 06

Tambaya da Amsa karo na 06


TAMBAYA: Assalamu alaikum. Nakan ji mutane suna cewa zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya. Shin wannan gaskiya ne?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh! da gaskene idan mummunan zato ne, saboda zato akwai kyakkyawa akwai mummuna. To mummunan zato shi ba shi da kyau, saboda haka shi ne zunubi. Alal misali, in ka ga wani tare da wata suna tafiya, to kada zuciyarka ta sawwala maka cewa wannan yana nufin tsakaninta da shi akwai wani abu. Sai ka ce, wane ne da matarsa ka wuce abinka. To amma in ka munanan zato cewa yana nufin kaza ne, to ka ga ka fada cikin zunubi, ko da kuwa wannan abin da ka fada din gaskiya ne.

TAMBAYA: Dan kasuwa ne ya fara kasuwanci da 100,000, da shekara ta zagayo sai suka zama 200,000. Idan zai fitar da khumusi zai hada da uwar kudin ne ko a ribar kawai zai fitar?

SHAIKH ZAKZAKY: A riba kawai zai fitar da khumusi. Shi kuwar kudi tunda shi ake jujjuyawa, ba abin da ya hau kansa. Da a ce ajiye uwar kidin ya yi bai juya ba sam-sam, to da shi ne sai ya hau uwar kudin, amma tunda ya juya shi, to abinda ya hau shi ne zai fid da khumusi a kai.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Tun kafin na yi aure na yi alkawarin idan na haifi 'ya mace zan sa mata suna Nusaiba, kuma alhamdulillah na sa wannan suna. Shin wacece Nusaiba a tarihin Musulunci, kuma wace irin gudummawa ta bai wa addinin Musulunci?

SHAIKH ZAKZAKY: To alhamdu lillahi tunda har ya cika alkawari, Allah ya raya ita wannan Nusaiba din. Kuma ba tun fari, wannan ba muhallin ba da amsoshin tarihi bane. Amma yana iya zuwa ya duba lttattafan tarihi zai sami bayani.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Mahaifiyata ta kamu da ciwon da ya yi sanadiyyar rasuwarta, kuma ya zamana ba ta sami damar yin azumin watan Ramadan ba, kuma ni kadai ne danta. Shin ya kamata na rama mata azumin nata da ba ta yi ba? Kuma yaya zan rama din?

SHAIKH ZAKZAKY: Ya ma wajaba ne, idan ya zama a surar cewa za ta iya ramawa amma ba ta sami ramawa ba. Amma idan a surar da ba ma za ta iya ramawa bane, kamar ta rasu a cikin rashin lafiyan kuma ba ta warke ba, ko a Ramadanan ma, to zai zama mustahabbi ne, ba wajibi ba ya rama mata. Kuma yadda zai rama din yadda duk ya yi masa sauki ne, ba a ce lallai ya jera kamar yadda ta bari ba. Abin dai da zai biya shi ne adadin kwanakin da ta sha. Duk yadda ya saukaka masa da niyyar cewa yana rama mata azumi ne.

TAMBAYA: Akramakallahu. Ina mai da hankali sosai a wajen addu'o'in Ma'asurat na safe da yamma fiye da karatun Alkur'ani. Ko ina da laifi?

SHAIKH ZAKZAKY: To ya kamata ka yi 'balance' ne, ya zama kana karatun Alkur'ani kuma kana addu'a. Domin ya zo a Hadisi cewa wanda karatun Alkur'ani ya shagaltar da shi da ga barin addu'o'i, Allah zai ba shi fiye da wanda yake ba masu addu'a. Saboda haka karatun Alkur'anin ya fi addua din. Amma ala ayyi halin ba a ce ka yi daya ka bar daya ba, duk biyun za ka yi. Kamar yadda kake mayar da hankali wajen addu'o'i, to ka kuma mayar da hankali wajen karatu Alkur'ani, ka yi su duka. Duk ka mayar da hankali ka yi ta ta yi.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Meye matsayin mutumin da ana bin sa bashin sallar azahar da la'asar, sai ya yi sallar magriba kafin ya sallace su?

SHAIKH ZAKZAKY: Idan mantuwa ne, sai ya yi azuhur dinsa da la'asar bayan ya yi magriba. Amma idan magriba din ya ga lokacinta ne na falafala, to ya ma samu ya yi ta, daga nan sai ya biya bashin wadancan. Amma idan duk cikarsu suka zama a lokacin yalwa kamar bayan isha, to lallai sai ya jeranta su.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ko ya halasta mutum ya ba da kudi idan ya je wata Ma'aikata don a dauke shi aiki? Kuma ya halasta idan lokacin karin girma ya yi aka ki kara wa mutum yana iya ba da kudi don a kara masa?

SHAIKH ZAKZAKY: To idan aka tilasata masa sai ya ba da wannan kudin zai karbi hakkinsa, sai mu ce to shi in ya bayar ba shi da laifi, amma bai halatta ma shi wanda ya karba din ba. Shi wanda ya karba shi ya ci haramun. Ya karbi haramun kuma in ya ci ya ci haramun. Saboda wannan yana nuna kamar hakkinsa ne ba za a ba shi sai ya ba da wani abu. Amma abin da ya zama haramun shi ne ka ba da kudi a ba ka abin da ba yake ba hakkinka ba. Shi wannan haramun ne, amma in hakkinka ne wani ya tilasta maka in ba ka ba shi ku Din ba zai ba ka hakkin naka ba, to in ka ba shi kai ba ka yi laifi ba amma shi ya yi laifi.

TAMBAYA: To amma idan bayan an yi wa mutum wani abu ne fa sai ya ji dadi ya dauko kudi ya ba wanda ya yi masa wancan abin?

SHAIKH ZAKZAKY: To shi makaruhi ne wannan, an karhanta yin haka nan, saboda shi ke sabbaba daga nan sai ya zama ka'ida. Daga baya kuma sai ka ga mutum in ba a ba shi ba sai ka ga yana ta wani dan gunaguni, Daga baya ma sai ya ki yi sai an ba shi. Sai ya zama doka kuma yanzu sai an bayar.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Da yake mutum na da zabi tsakanin sallar Juma'a da azahar ko ya hada duka biyun. Ko mutum na iya gabatar da azahar kafin Juma'a?

SHAIKH ZAKZAKY: Na'am zabi ne, amma akwai ihtiyadi da yin duka biyu. Saboda haka duka biyu ne ya hau kan mutum, tun da kuma duka biyun sun hau kansa, to ba su 'muzahama' da juna, wato ba su rige-rige da juna, saboda haka duk tafiyarsu daya ne. In ya sami yalwan lokaci a kan ya yi wannan kafin wannan, babu laifi, ya samu ya yi.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ko ya halasta maharbi ya ci naman da ya harbe amma kafin ya kai gare shi ya mutu?

SHAIKH ZAKZAKY: In ya harba da sunan Allah. Don shi wanda zai harba kamar kibiya dole ya zama ya harba da sunan Allah ne sai ya za wannan kibiyar ita ce tamkar yanka din. Amma in ya same shi da sauran rai sai ya yanka. In kuma ya samu ya cika, shi wannan ya wadatar, ambaton Allah din kafin ya harba. Ko aika kare na mafarauta in an horar da shi a kan ya kamo ya kawo, ba ya kama ya ci ba. To idan ya ji masu ciwo ya zama ya mutu a sanadiyyar jin masa ciwon, shi ma zai iya ci. Amma zai aika shi da sunan Allah. Wato ya ce Bismillahi a yayin aikawa din.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Samun ruku'u da Liman shi ne samun raka'a a Malikiyya. Shin ko haka abin yake a mazhabar Ahlul Baiti?

SHAIKH ZAKZAKY: Wannan bai kamata ya zama a babin tambaya ba, ya kamata ya zama ya karanta wata risala amaliyyan ta wani Mujtahidi don ya san irin wadannan abubuwan. Amma ala ayyi halin in ka sami liman yana ruku'u ka sami raka'a, wannan haka ya ke a Imamiyya kamar yadda yake a Malikiyya. Amma kuma ina ba shi shawarar cewa ya kamata irin wadannan mas'aloli, bai kamata a dogara ga tambayoyi kamar irin wannan ba, ya kamata mutum ya karanta risala amaliyya ne ta wani Mujtahidi.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Idan mutum na salla da Liman, shin dole ne ya yi karatun fatiha?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai idan kana bin liman yana dauke maka karatu a raka'o'in farko guda biyu. Saboda haka ba za ka yi karatu ba. Sai dai a surar da aka ce kana iya yin karatu, shi ne idan ya zamana yana karatu a bayyane amma kai ba ka ji. Amma in yana yi a asirce, wajibinka ne shi ne ka yi shiru. Amma a raka'o'in biyun karshe wanda kake da zabi tsakanin Fatiha da tasbihi, to shi an fi son mai bin liman ya yi tasbihi ne kuma liman ba ya dauke masa wannan. Mai bin liman an so ya yi tasbihi ne maimakon karanta Fatiha. Shi kuwa liman an so ya yi Fatiha ne.

TAMBAYA: Allah gafarta ya Malam ko zan iya karatun Kur’ani a cikin sujada a sallar nafila?

SHAIKH ZAKZAKY: A’a, ba a karanta Alkur’ani a ruku’u da sujuda, sai dai in wani bangare nasa da ya bullo da unwanin addu’a, kamar ‘rabbana atina fiddunya hasana’, ko abin da ya yi kama da haka nan, amma ba matsayin kira’a ba. Kira’a a tsaye ake yi, amma ba a yi a sauran wurare.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, an ce balagar ’ya mace shekara 10, namiji kuma shekara 14. Tambayata ita ce, ‘ya ta shekararta 10, amma kuma azumi na ba ta wahala, ita da dan uwanta. Shin Malam me ya kamata in yi?

SHAIKH ZAKZAKY: To, na farko dai ba a ce shekara 10 ba ne, 9 ne ma, bai kai 10 ba, ga ’ya mace. Shi kuma namiji yakan zama galiban 12 ne. Yanzu muna ganin abubuwa na sassakewa na yanayin jikkunan yara din, wala’alla shi ya zo a rubuce haka nan. Don da mu mun saba yara din ba sukan balaga ba, kamar maza, sukan kai 17 a da can, mata kuma sukan kai 14, amma sai muka ga yanzu balagar tasu tana komowa baya, wala’alla shi ya sa shari’a ta zo da shi don ta san zai kai haka nan. To, idan yarinya ba za ta iya azumi ba, to sai a dauki wadansu matakin da za a iya saukaka mata, kamar misali a kirkiri tafiya. Amma dai lallai matukar tana nan, azumin ya hau kanta. Sai dai ni ina ganin wannan rashin iyawar, kila har da rashin tarbiyyantar da yaran su yi azumi tunda wuri. Tunda mu yaranmu nan, ba su shan azumin tun kasa da shekara 7, suna Ramadan din su cikakke, kuma har su kai balaga din. Amma lallai in har ba za ta iya ba, to lallai kuma ya hau kanta. Saboda haka sai dai a bi wata hanya ta shari’a, alal misali tafiya. Sai a kirkiri tafiyar da zai ja mata ta sha, har a jira in kafin wani Ramadan za ta yi azumi, sai ta rama.

Post a Comment

0 Comments