Tambaya Da Amsa Karo Na 40

Tambaya Da Amsa Karo Na 40

Tambaya da Amsa karo na 40


TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ni ne ban san an ga watan Ramadana ba, sai bayan da rana ta yi. Me ya kamata in yi, kuma ya azumina na ranar?

SHAIKH ZAKZAKY: To, in na fahimci abin da yake nufi da rana ta yi, ma’ana gari ya waye kenan yake nufi. Da ma idan mutum bai ci abinci ba, to shi kenan zai iya ci gaba da azuminsa, matukar zawwal bai yi ba, kuma yana da wannan azumin. Idan kafin zawwal ne, yana da wannan azumin, in bayan zawwal ne, to sai dai ya kama baki, zai rama bayan Ramadan. Amma idan kafin zawwal ne, zai yi azuminsa ne kawai matukar bai ci wani abu ba; in ya ci wani abu, wannan yana nufin ke nan ramuwa ta kama shi.

TAMBAYA: Akramakallahu, ina gudun hijira ne a Filato, idan na ziyarci gida Sakkwato zan kwana 2, ko 7. Ya matsayin azumi da kasarun salla a wannan muhalli, ganin cewa can ne garinmu na haihuwa?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, to tunda har yanzu yana ganin kansa a Sakkwwato yake, zaman lalura yake yi a Jos, saboda haka shi Sakkwato ne gida a wurinsa, kodayake Jos din ma ta zama gida. To, lokacin da yake wadannan wuraren biyu, duka zai cika salla ne, har sai lokacin da ya zama ba ya tunanin can garinsu ne, wato kamar ya canza gari kenan, to sai garin ya zama wani abu daban. Amma dai yanzu Sakkwato garinsu ne. In yana Sakkwato yana gida ne, in ma yana Jos kazalika. Saboda haka cika salla zai yi, kuma ya yi azumi.

TAMBAYA: Akramakallahu, zan yi alwala ne, amma sai yan kasance kaina da jikina duka a jike suke. Ya zan yi batun shafa, musamman in babu abin da zan goge a kusa da ni?

SHAIKH ZAKZAKY: To ai da ma, ko ruwa ma na alwala ba sai yana kusa da kai ne za ka yi ba, za ka je ka nemo ruwa ne. Saboda haka shi ma abin gogewar, sai a neme shi ai. Wannan ba hujja ba ne. Abin da ya hau kansa shi ne, sharadin shafa ne ya zama wuri busasshe. Saboda haka lazim ne ya nemi abin gogewa.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, a yi mani karin bayani game da hadisin nan da ke cewa Manzo (S) ya ce al’umma za ta kasu kashi 73, amma kashi daya ne gaskiya?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, wannan shahararren hadisi ne, wanda duka bangarorin nan biyu suka ruwaito shi. Sai dai akwai wadansu sigogi daban-daban da aka kakkawo na wannan hadisin. Daya daga ciki, shi ne wannan. To, da yake kuma wasu sun sa ra’ayi a ruwayoyin nasu, har ma sukan fito da wasu kungiyoyi su ce su ne firka din. To, amma dai shahararren hadisi ne za mu iya cewa. Saboda shahararsa ya zama karbabbe. Abin lura a nan shi ne, al’umma aka ce za ta kasu, ba addini ba, shi addini kwara daya ne. Saboda haka idan al’umma ta rarrabu a kan addini, zai kasance daya ke rike da addini kenan. Tare da fatan an fahimta.

TAMBAYA: Allah gafarta Malam, idan kaffara ta hau kan mutum sakamakon karya azumin Ramadan, kuma bai iya yi ba har wasu Ramadan biyu. Ya zai biya wannan kaffarar, kuma ya matsayin azumin nafilar da ya yi a wadannan shekaru?

SHAIKH ZAKZAKY: To, dama dai idan ramako ya hau kan mutum (shi kaffara kawai ya fada), lazim ne ya yi kafin wani Ramadan, haka zalika kaffara. To, idan wata lalura ta sa bai yi ba, bai fadi a kansa ba. Saboda haka duk ramuwar da ta hau kansa, ko bayan shekara nawa ne, duk yana nan a kansa. Haka ma kaffarorin da suka hau kansa, duk suna nan a kansa. In har ya san abin da yake yi, da ma mutum ba ya yin nafila idan akwai wajibi a kansa. Saboda haka in bai sani ba ne, sai mu ce, to yanzu shi kenan, ba za mu iya hukunci a kan abin da ya yi bisa rashin sani ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ganin yadda mashaya kwaya suka mayar da maganin tarin nan na Benylin abin sha su yi maye. Ko wannan ya haramta wa mai sayar da magunguna sayar da wannan maganin?

SHAIKH ZAKZAKY: A’a, sayar da maganin ba zai haramta masa ba, amma in ya san wani hususan shi yana sha ne ya yi maye, to ba zai sayar masa ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ni ne nake kasuwanci daga garinmu zuwa wani gari, in na je ina yin kwana 4 sannan in dawo gida in yi kwana 3 in koma. Shin zan yi kasaru ne a matsayi na matafiyi, ko kuwa ya zan yi?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai a yayin da duk yake tafiya, sunansa matafiyi. Saboda haka wannan tafiyar tasa, in dai ta cika sharuddan tafiya. In na fahimce shi, ya san ka’idar tafiya din, na tsawon matafiya din, ya kuma san cewa akwai adadin kwanakin da zai yi niyyar kwanakin nan zai yi, sannan ya daina kasaru. Saboda haka in ya san wannan, sunansa matafiyi, kuma kasaru zai yi, ko ya kuwa ya kasance, ko da kuwa da wane lokaci yake tafiya. In yana son ya daina kasaru, sai ya bayar da tazara mai yawa daga wannan tafiya zuwa wannan. Ko ya je ya yi niyyar kwanaki daidai yadda zai dauke masa kasarun. Amma dai matukar ka’idar kasaru ta cika, kasaru ta hau kansa.

TAMBAYA: Allah gafarta Malam, ko ya halatta in sayar da kayan mata masu nuna tsaraici, ganin cewa wasu na sanyawa ne a gidajen mazajensu?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, amma in ya san wata khasatan ita tana tabarruji ne da shi, ita ba zai sai da mata ba. Kamar shigen wancan mai tambayar Benelyn. Idan wata da ma ita tabarruji take yi, ita ba zai sai da mata ba. Amma wanda ya san ita mahajuba ce, a gidanta za ta sanya, ita zai sayar mata. Wacce ma bai san halin ta ba, ita ma zai sai da mata.

TAMBAYA: Allah gafarta Malam, ni ne janaba ta same ni alhali ina yananin da ba zan taba ruwa ba. Me ya kamata in yi don ci gaba da ibada?

SHAIKH ZAKZAKY: To ban san ko ya san yanayin da ba a taba ruwan ba. Saboda ba ya fadi yanayin da ba zai iya taba ruwan ba ne, don ta yiwu shi ba ya son ya tabi ruwan ne, sai ya ce yana yanayin da ba zai taba ba. Ko kuma kamar yana jin sanyi. To amma idan ya san yanayin da ba za a ita taban ruwa ba. Yanayin da ba za a taba ruwa ba shi ne, taban ruwan zai sabbaba cuta ko mutuwa. Amma in ba haka nan ba, in dai sanyi ne yake ji, to sai ya daure, ko kuma ya dumama ruwa. Saboda haka yanzu tunda ba ya fadi yanayin bane, sai mu dauka ya san yanayin kenan. Kuma idan wanka bai yiwu ba, kamar yadda in alwala ba ta yiwu ba, taimama na tsaya mata, haka ma in wanka bai yiwu ba, za a iya yin taimama a yi salla, har kafin a sami ruwa a yi wanka.

TAMBAYA: Allah gafarta Malam, ko mai kasaru zai iya jan mazaunin gida salla, haka shi ma mazaunin gida ya ja mai kasaru?

SHAIKH ZAKZAKY: In na fahimci abin da yake nufi, yana iya zama Liman kenan, ko kuma daya yana iya koyi da daya kenan. Mai kasaru zai iya bin mai cika salla, haka ma mai cika salla zai iya bin mai kasaru, amma kowa zai bi sunnar da ta hau kansa. Wato mai kasaru, ya yi kasaru, mai cikawa ya cika sallarsa. Idan mai cikawa ya bi mai kasaru, in mai kasaru ya gama nasa sai ya cika. Idan mai kasaru ya bi mai cikawa, in mai cikawan ya yi raka’a biyu, yana iya sallamewa.

Post a Comment

0 Comments