Tambaya da Amsa karo na 04
TAMBAYA: Allah ya jikan Malam, menene ingancin hannun da ake sanya zobe, shin a hannun dama ake sanyawa, ko a hannun hagu bisa sunna ta Manzon Allah (S)?
SHAIKH ZAKZAKY: Idan kwara daya ne rak, dama ya dace da shi, idan kuwa ya fi daya, in ka sa hagu da dama babu laifi. Bilhasali, mustahabbi ne ka sa daya a dama, daya a hagu. A 'binsari' zai sa na dama. Sannan kuma a hagu, sai ya sa a 'khinsari'.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ko ya halatta mutumin wata jiha ya yi takardar zama dan wata jiha don ya sami aikin gwamnati a wannan jiha?
SHAIKH ZAKZAKY: In an fahimce shi a kan cewa ya canza jiha ne, yanzu ya koma dan wata jiha, to babu laifi da shi. Amma in yaudara ya yi, to ya yi laifi. Idan su sun dauka shi dan jihar ne, amma shi ya yi yaudara ne, ya yi karya kenan, ya nuna cewa shi dan jiha ne kawai don ya sami wannan, alhali shi ba dan jiha bane. Ala ayyi halin dai, na san kana iya canza mazauni idan ka ga dama. Saboda haka in wannan canza mazunin ka yi, ka ce yanzu ka koma dan waje kaza, babu laifi. In fata a 'unwanin' canzawa ya yi daga wata jiha zuwa wata jiha, ba a 'unwanin' yaudara da karya ba. In karya ne da yaudara, ya zama haramun. Kuma in ya sami wani hakki a nan wanda yake ba nasa bane, zai zama ya ci hakkin wani kenan.
TAMBAYA: Malam a ranar rufe tafsir, ka tabbatar da kwanan watan Sha'aban, amma bayan an shiga azumi sai ga gyara a ALMIZAN na karin kwana daya. An tashi da azumi Alhamis wasu ba su da bayani, kuma ba su yi azumi ba dogaro da wancan lisafi, to me ya kamata su yi, ramuwa ko kaffara?
SHAIKH ZAKZAKY: A bisa gaskiya dai tafsiri ba a rufe ba sai a cikin Ramadan. Ba a cikin Sha'aban aka rufe tafsiri ba. Saboda haka, ba wani bayani da ya nuna batun kwanan wata a ranar rufe tafsiri na Sha'aban. Saboda haka wannan magana da kake yi cewa ka ji a Tafsiri, ba gaskiya bane. Sai dai in ka ce Almizan ta gaya maka a lissafi. Kuma bisa cika Sha'aban kwana 30. Amma da aka tabbatar da kwanan wata, sai lissafi ya canza. Haka kuma ake yi a kowanne. Ai dama duk watan da ya zo in ba a san lissafi ba, ana cikawa ne, in an samu a gyara, haka ake yi dama. Amma kuma wanda zai dauki azumi, ya kamata ya duba ALMIZAN? Don haka, tun farko dama ba ka da hujja na tashi da azumi bisa yanayin ganin wata da ALMIZAN ta buga ko wanda aka fada a tafsiri, in ma an fada din. Zai yi la'akari da karshen Sha'aban ne, in an a ce an ga wata. Shi tashi da azumi, ana yi ne bayan an ga wata da daddare, a tashi da azumi kashegari. Saboda haka lazim ne ya saurara ranar Laraba da daddare ya ji ko an ga wata don ya tashi da shi Alhamis. Kodayake ran nan 28 ne a lissafin, amma shi ma an nuna da shakku don yana iya zama 29. In ba shi da hanyar sani, to shi kenan sai ramuwa ta kama shi. Amma in har ya san an ga wata ya ki yi ne, wai shi ya dogara da lissafin da ya ji, ko ALMIZAN ta rubuta ko kuma ya ji a tafsiri, to lallai sai mu ce ba shi da hujja. Tunda yake ba yadda za a yi a dauko lissafin da yake can baya, wanda ba zai iya gaya maka watan nan cika zai yi ko nukusani ba, ka ce da shi za ka yi aiki. Saboda haka shi wannan dole zai zama ramuwa da kaffara ya hau kansa, in har yana da labarin an ga wata ya ki ya tashi da azumi. Allahumma sai in dai sam ba shi da labarin ne, to sai mu ce ya rama.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam mutum ne Mai gidansa ba ya ba shi hakkinsa yadda ya dace, amma shi yaron idan an tashi sai ya rinka daukar wani abu, alhali shi Mai gidan bai sani ba. Ya wannan abin yake?
SHAIKH ZAKZAKY: Lallai abin da ya dauka, tunda ba hakkinsa ba ne, to duk cikarsu sun zalunci juna kenan. Maigidansa ya zalunce shi ya kin ba shi hakkinsa, shi kuma ya zalunce shi ya yi masa sata.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ko zan iya wanke bakina da makilin da rana a lokacin azumi?
SHAIKH ZAKZAKY: Mun sha amsa irin wannan tambayar. Yana iya wankewa matukar dai ba zai hadiye ba. Wadansu sukan ce yana da dandano, to dandanon abu, in dai ba ya wuce makoshi ba ne, ba komai. In dai ya dandana ya furzar. Saboda haka ba laifi da wanke baki da shi, ko da kuwa yana da dandano.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ni dai mutum ne mai rauni a ibada. Ina barar addu’a da kuma shawarar da zan bi don inganta kwazo a ibada?
SHAIKH ZAKZAKY: Masha Allah, ina fata raunin nasa a nafiloli ne, ba a farali ba. In a nafiloli ne, akwai a cikin ‘misbahul Mutahajjid’, ya kawo shawarwarin yadda wanda ke sake da sallar dare zai yi idan yana sake da sallar dare, akwai wasu surori da zai karanta. Yanzu ba zan kawo su ba, amma ya duba littafin zai gani. Amma ina fata na nafila ne, ba yana sake da farali ba ne.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ko zan iya daukar wacce zan aura a mashin, duk da kuwa ba a daura auren ba?
SHAIKH ZAKZAKY: To, dai wadda zai aura bai dai aure ta ba. Saboda haka muharramarsa ce. In abin da yake nufi shi ne jikinsu zai hadu, yana ganin tun da zai aure ta, sai mu ce masa a’a, tana nan a muharramarsa har sai an daura masu aure.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, wasannin tashe da ake yi idan azumi ya kai kwana goma, menene asalinsa, kuma ya matsayinsa a Musulunci?
SHAIKH ZAKZAKY: Al’ada ce dai kawai. Kuma abin mamaki kusan ko’ina a kasashen musulmi suna wannan al’ada din, yakan bambanta tsakanin wannan wuri da wannan wuri, kasashen Larabawa suna yi, wasu wurare ya zama zaunennan abu, mai yiwuwa saboda yanayin rayuwa irin ta da mutanen da, da duhu, da kuma sai an ta da mutane. Amma kuma yanzu ya zama kawai wasannin ne, ba a bukatar sa. Amma a da ana bukatar sa sosai don a tashi mutane su dafa abinci, amma yanzu ba a bukata, saboda mutane suna da agogwanni masu karaurawa, da kuma yanzu ma daren ma ba a cika barci sosai ba. Amma dai al’adar mutane ne, kuma ba laifi da shi, tun da ba an ce aibada ne da aka ruwaito ana yi ba. Al’ada ce kuma ba ta yi karo da shari’a ba, saboda haka ba komai. Allahumma sai dai in akwai wasu abubuwa da ake yi a tashen, wanda ya saba ma shari’a, sai a ce to su a bar su. Amma shi tashe a kashin kansa kawai al’adar mutane ne.
0 Comments