Tambaya Da Amsa Karo Na 36

Tambaya Da Amsa Karo Na 36

Tambaya da Amsa karo na 36


TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne ya yi alwala sai ya ji rauni a wajen alwalar har jini ya fita, shin zai sake alwalar ne ko wanke jinin ya wadatar?

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai ba ma dai ko guda, domin fitar jini ba shi daga cikin abubuwan da ke warware alwala. Sai dai jini najasa ne, akwai daidai gwargwadon wanda akan yafe a salla da kuma gwargwadon da ba a yafewa. In jini ya fito daidai gwargwadon wanda ake yafe shi a salla, wanda shi ne bai kai fadin dirhamin alfadari ba, to ba ma ya bukatar ya wanke.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, nine na gabatar da sallar azahar kafin in yi la'asar, sai kaikayi ya kama ni a hannu, sai na yi ta susar hannun har ya yi fari. Shin kafin na yi salla sai na sake alwala ko kuwa?

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai susa ba shi daga cikin abubuwan da ke warware alwala. Ko ya yi fari, ko ya yi ja, ko ya yi baki; duk daya ne.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Sana'ata sai da dabbobi, sai na zuba a mota zan kai wani gari domin sayarwa. To ana cikin tafiya sai wata za ta mutu. Ganin haka sai na yanka ba tare da na kalli alkibla ba. Shin yankan ya yi ko kuwa?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, ya yi, sai dai ba a bi ladabi ba. Shi duban alkibla yana cikin ladubban yanka. Saboda haka idan wata lalura ta sa ba a kalli alkiblar ba, ba za a ce yankan bai yi ba.

TAMBAYA: Akramakallah, shin ya halasta mutum ya yi irin kiwon nan na tsuntsu, ya tsare shi a keji, kamar aku da kanari da sauransu?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ba abin da ya hana shi ya yi, matukar zai kiyaye da hakkin abin da yake kiwo din. In kuma ya tauye masa hakki, to lallai ya yi laifi. Kamar ya tsare shi bai ba shi abubuwan da shi (tsuntsun) zai bukata a rayuwa ba. Wala'alla ma wadansu daga cikin wadannan abubuwan da ya ambata, ko da an sake su a keji din, ya zama in sun fita za su je su dawo, ka ga sun riga sun aminta da wurin zaman nasu kenan saboda suna jin dadin zaman.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, mutum ne yana da dukiya kuma ta kai misalin a fitar mata da zakka, amma ba ya fitarwa. Sai aka yi masa nasiha kuma ya yarda zai fitar. Shin zai fitar da na shekarun da suka gabata ne, ko daga wannan lokacin ne zai fara fitarwa?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai duk zakkokin da suka hau kansa, matukar yana musulmi, akili, baligi, to lallai suna nan a kansa, ko da sun shekara nawa ne. Saboda haka wajibinsa shi ne ya fitar da duk na shekarun baya. Wato zai yi la'akari da duk yadda ta kama masa, bara nawa ya hau kansa? Bara waccan nawa ya hau kansa, da sauransu. Wato zai fitar da irin abin da ya hau kansa ne. Har ma inda dukiyar da ya hau ya amfana da su, har da su abin da suka hau din, duk zai bayar a matsayin zakka.

TAMBAYA: Akramakallah. An ce mace idan tana salla ba ta bayyana karatu a wurin bayyanawa, to idan ta manta ta bayyana fa? Kuma za ta iya bayyanawa idan a dakinta ne ita da mijinta?

SHAIKH ZAKZAKY: To, idan ta bayyana bisa kuskure, babu komai. Wannan hukuncin ma haka yake ko da ga namiji ne. A inda aka ce a boye karatu, in ya bayyana da kuskure ko da mantuwa, shi ma babu komai. Haka zalika in ya asirta inda ya kamata ya bayyana. Dangane da ita kuma mace, tana iya yin karatu ta bayyana muryarta a wurin bayyanawa in wani ajanabi ba zai saurare ta ba, kamar inda ya ce a dakinta ne, in mijinta ko 'ya'yanta ko muharramanta za su saurare ta, babu komai.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, menene hukuncin wanda ya kewaya Alkur'ani don an yi masa sata da nufin Allah ya kashe wanda ya yi masa satar, ko ya hadu da wani bala'i?

SHAIKH ZAKZAKY: To, wannan ba a san shi ba a shari'a. Ba a san cewa idan an yi sata ana yin wani abu ne da Alkur'ani don mutum ya mutu ko wani bala'i ya same shi ba. Saboda haka tana iya yiwuwa wadansu irin tsaface-tsaface ne ko tsubbace-tsubbace, wadanda da ma can Maguzawa ke yi da wadansu itatuwa, yanzu kuma wasu suke neman su yi shi da Alkur'ani. Amma ba a san shi ba a addini, kuma ba zai zama ya halatta ba.

TAMBAYA: Akramakallah, menene hukuncin dan uwan da ba ya salla a masallacin kusa da gidansa saboda su ba mabiya Imamiyya bane?

SHAIKH ZAKZAKY: To, in ba su munana masa zato a kan cewa ba ya salla, babu komai. In kuma za su munana masa zato a kan cewa shi ba ya yin salla ne, to sai ya rika yin salla da su.

TAMBAYA: Malam ya taba cewa miji da iyaye ba su da iko a kan dukiyar mace, alhali ga hadisi ya ce mace ba ta da ikon ta yi tasarrufi da dukiyarta sai da izinin mijinta, ina neman karin bayani.

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai ni ma ina neman karin bayani dangane da ina na fadi wancan Magana. Tana iya yiwuwa wata magana ce ya dauko daga cikin wata magana ta daban, bai kawo bayaninta cikakke ba. Amma dai abin sani shi ne, ita mace tana da ikon tasarrufi a kan dukiyarta ba tare da izinin mijinta ba, sai a wadansu abubuwa kadan. Alal misali a cikin abubuwan da yake amfana da shi na yau da kullum wanda aka saya kila da sadakinta, kamar misali a ce Firij ko murhun girki ko gado ko abin da ya yi kama da haka, in ta ce ta sayar ko ta kyautar, yana iya musanta mata. Haka kuma idan wani abu ne babba kamar gida ko mota ko gona, in ya kai sulusin abin da ta mallaka, shi ma yana iya musanta mata. Amma a sauran abin da ba wadannan da muka ambata ba, tana da ikon tasarrufi a dukiyarta. Kuma ban san a ina ne aka yi batun cewa iyaye da miji ba su da iko a kan dukiyar mace ba. Ban san inda na fadi wannan ba. Illa iyaka wannan maganar tasarrufi din shi ne aka sani.

TAMBAYA: Mutane biyu ne suke kwance a daki lokacin watan azumi, sai suka makara yin sahur. Da suka tashi suka ga karfe 6:00ns ta yi, sai daya ya ci abinci, shi kuma dayan da ya ga shida ta yi, sai ya ki ci, to yaya matsayin azuminsu?

SHAIKH ZAKZAKY: To idan alfijir na ketowa kafin shida na safe, kuma an san haka, duk cikarsu sun sani, kamar shi wanda ya ci abincin ma ya sani cewa alfijir ya keto, in dai har ya ga 6:00 na safe, to ramuwa da kaffara ya hau kansa. Idan kuwa shi wanda ya ci abincin a zatonsa karfe 6:00 alfijir bai keto ba, sai ta bayyyana masa ashe ya keto, shi ramuwa ne kawai ya hau kansa ban da kaffara. Shi kuwa wanda da ma bai ci abinci ba, shi kenan, da ma ba wani abu dangane da shi tunda da ma bai yi sahur din ba.

TAMBAYA: Akramakallah, mutum ne bai da lafiya sai aka tashe shi don ya yi sahur, amma rashin lafiyar ta hana shi tashi da wuri. Bayan ya tashi yana cikin cin abinci sai ya ji ana ta sallar asubahi, to yaya azuminsa?

SHAIKH ZAKZAKY: To, in ya kaddara cewa lokacin da ya tashi din ya dauka cewa alfijir bai keto bane, sai ya ci abinci da nufin yana sahur, to sai ya ji cewa ashe ga shi can ana salla, wato ma'ana alfijir har ya keto, to sai ya yanke cin abincin kuma ramuwa ta hau kansa, ban da kaffara. Amma in ko lokacin da ya fara cin abincin ya tabbatar da ma lallai afijr ya keto ya dai ga daman ya ci ne saboda yana ganin bai iya tashi da wuri ya ci, to shi kuma ramuwa da kaffara ne ya hau kansa. Abin da dai za a la'akari da shi shi ne, alfijir ya keto ko bai keto ba, ka sani ko ba ka sani ba? In kana tsammanin alfijir bai keto ba, sai ka ci abinci, sai ta bayyana ashe ya keto, to ramuwa ya hau kanka. Idan kuwa ka san alfijir ya keto ka ci abinci, to ramuwa da kaffara ne, tunda ka yi da gangan, kamar wanda ya ci da rana ne.

Post a Comment

0 Comments