Tambaya Da Amsa Karo Na 34

Tambaya Da Amsa Karo Na 34

Tambaya da Amsa karo na 34


TAMBAYA: Ina sayar da man fetur ne, kuma ina amfani da galan gida biyu, kowannensu lita hudu ne, amma daya ya fi girma kadan. Shin ya halasta na zabi karamin in yi awo da shi?

SHAIKH ZAKZAKY: To, adalci dai wajibi ne a dukkan harkoki, ciniki ne ko wani abu mai kama da haka. Saboda haka kar ka zama cikin sifar wanda in shi zai sayar, sai ya tankware, in kuma shi zai sayo, sai ya cika. Mai yiwuwa kai in da za a zo a sayar maka, kila babban za ka dauko, ka saya da babba, in ka zo sayarwa ka sayar da karami. Ya kamata ya zama bai daya ne. Bai kamata ya zama shi abin da yake awo wani ya fi wani ba.

TAMBAYA: Sannan idan mutum ya sayi mai kuma na cika masa galan, to amma kafin na zuba masa, kadan daga cikin mai din yakan zuba a kasa, ko wajen zubawa a mota ko mashin, amma wanda aka sayarwa ba sa yin magana. Shin ko ina da laifi?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, in dai da gangan ne ka zubar masa da man kana da laifi mana, ka yi barna kenan. Sai dai idan irin wanda ba akan rasa bane bisa adatan yakan dan zuba, to wannan ba laifi.

TAMBAYA: 'Yan kasuwa ne suke zaune waje guda, idan mai sayen kaya ya zo kan kayan wani daga cikinsu, sai shi bai gan shi ba, sai wani ya kira shi kan kayansa.To meye hukuncin wannan?

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai ya kamata a bar mai saye ya zaga ya ga inda yake so ya sayi abu ya ga abinsa ya saya. Kar ka karkatar da 'costoman' wani zuwa gare ka, ka kyale har shi mai sayen kayan don zabin kansa ya tsaya ga wani. Ko ba komai kun kasa kaya kuma yana kallon kayan, mai yiwuwa yadda ya tsaya gaban wancen kayansa ya gani, saboda haka in ka kira shi zai dauka kamar kai ne mai wancen kayan.

TAMBAYA: Idan na dauki tsawon lokaci ina amfani da jarka ta kan kara budewa, ya zama tana ci fiye da abin da yake ka'ida. Ko ya halatta in ta bude in canza sabuwa domin ta ci daidai da ka'ida?

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai adalci din kenan, kamar yadda na fada a baya, cewa kamar yadda za ka saya, haka za ka sayar. Haka ya kamata ya zama 'Standart,' zaunannen abu ne, bai da tankware ba, bai da fadi.

TAMBAYA: Ina hukuncin Shugaban da ya karbe kudaden na kasa da shi da niyyar za a yi wani abu da su, amma ya ki yin abubuwan da ya fada masu?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ya ci amana kenan. Kuma za a tambaye shi dangane da wannan a duniya da lahira.

TAMBAYA: Ina so Malam ya yi mani bayani dangane da tauhidin Uluhiyya da Rububiyya. Sannan kuma wani Malami wanda ya wallafa wani littafi da ake ce wa Murshadatun, ya ce Allah ba shi kasa, ba shi sama, ba shi dama, ba shi hagu, ba shi gaba, ba shi baya. Yaya abin yake ne?

SHAIKH ZAKZAKY: To, wannan ilimi ne mai zurfi, kuma kar ka sa kanka a abin da kai ba ka gane ba.Ya ishe ka ka yarda cewa Allah daya ne, bai haifa ba, ba a haife shi ba, kuma shi ne ya cancanci bauta, sai ka bauta masa. Amma neman faifayewa da hakikanin Allah, ba zai yiwu ba. Ba za ka iya ganewa da hakikaninsa ba, amma za ka iya gane wani abu daidai gwargwado wanda zai kara maka imani, in abu ya fi karfin fahimtarka, to, ka ajiye shi a nan, ka bar shi nan. Saboda haka wannan ina iya ce maka, wani ilimi ne wanda yake sai an yi ilimi da zurfi ake zuwa ma ga wannan. Saboda haka ya kamata ka da ka sa kanka a ciki. Ka yarda da cewa babu Ubangaji sai Allah, kuma Muhammadu Manzonsa ne, wanda yake nufin shi kadai za ka bauta wa ta hanyar sakon da Manzon Allah ya zo da shi.Wannan ya wadace ka.

TAMBAYA: A littafin hadisai Arba'in na Annawawi, ya kawo hadisin da yake cewa, halas a bayyane take, kuma haram a bayyane take, amma akwai abubuwa da yawa masu rikitarwa tsakaninsu. Don haka ina neman karin bayani daga Malam.

SHAIKH ZAKZAKY: To, insha Allahu, wannan bayanin da shi Manzon Allah din ya yi ya wadatar.

TAMBAYA: A cikin Alkur'ani an ambaci maroki da mabaraci da suna guda. To meye dangantakarsu, kuma meye matsayin kowanne a addinance?

SHAIKH ZAKZAKY: To, mai roko dai shi ne mai bara din, ba wani abu ne daban ba, "lissa'ili wal mahrum." 'Sa'il,' shi ne wanda yake tambaya, yake cewa a ba shi, shi ne ya fi cancanta da mu ce masa mai bara. Sannan kuma 'mahrum' shi ne wanda ba shi da shi ko da bai tambaya ba. Amma dai roko da bara luggogi ne na Hausa. Sai dai a yanzu haka akwai wadansu mutane da a ke ce masu maroka. Su wadannan masu wani irin sana'a ne da sukan yabi mutum ya ba su. To ba su a ke nufi ba, ko sun buga ganga, ko ba su buga ganga ba, su ba su a cikin lissafin wadancen mutane. Bilhasali ma su wadannan hukuncinsu da ban ne. Su ba a ma karfafa maka gwiwar ka ba su ba, in ma za ka ba su sai ka ba su kadan, don gudun sharrinsu, saboda suna da harshen da za su iya cutar da kai da shi, da wake ne ko zambo, ko abin da ya yi kama da haka nan. To, amma ba su ne ake nufi da marasa ba. Akwai wadansu 'isdilahohi' na kamar miskini, wanda yake nufin shi ne wanda bai mallaki abin da zai ishe shi ya ci a shekara guda ba. Ko kuma wanda yake cikin halin bukata. Da fakiri wanda yake shi ya fi miskini munin matsayi. Wanda shi fakiri shi ne wanda ba shi da shi sam-sam. Duk wadannan wasu nau'o'in mutane ne da aka karfafa maka gwiwar ka ba su. Amma wanda ba ya roko, shi aka fi ba ka karfin gwiwar ka bayar. Shi ba shi da shi, amma ba ya tambayar kowa.

TAMBAYA: Ina so malam ya yi mani bayani dangane da taba sigarida shake wato 'Snuff',domin wasu malamai na ce wa haramun ne, yayin da wasu ke cewa bata da haramci?

SHAIKH ZAKZAKY: To lailai kamar yadda ya ji din nan ne, fatawoyin Malamaine daban-daban, wasu Malamai sun haramta. Saboda haka in kana taka lidi da mushtahidin da ya haranta, sai ka bari in, kuma ka aikata ka yi laifi. Wadanda kuma suka ce halas ne, shi kenan, ko da su ma na san ba sun ce halas ne kada'an ba, sun dan karfafa gwiwar mutane da su bari. Ala ayyi halin, wannan wani abu ne wannan yake ba wani taimako yake kawowa ko kuma wani lada ake samu dangane da shi. Amma mutane sukan ji dadin suna yi, kuma wasu malamai suna ganin tun da ba a rawaito akwai wani abin da ya hana ba, sun samu su yi haka. To dai ya rage maka, da wa kake ko yi, in kana koyi da malamin da ya halatta ne, to ruwanka, in kuma da wanda aya halattane, sai ka bari.

TAMBAYA: Ko ya halatta malami ya yi zaune ya na karantarwa ba tare da wata sana'a ba, sai dai abin da almajiransa suka kawo masa?

SHAIKH ZAKZAKY: To wannan sai mu koma ga urfi, bisa urfin mutane yana iya samar mana da mafita dangane da wannan. Idan su mutane dama haka suka saba, cewa shi malami a kan dauki dawainiyarsa ne, shi kuma ya zo yana ta karantarwa, to wannan babu laifi da shi. Idan kuwa har zai zama yana wata sana'a ne, kuma yana koyarwa, ka ga kamar 'Part time' kenan yake yi. Don in zai hada sana'ar ciyar da kansa da kuma koyarwa, to lallai zai zama koyarwar baina-baina ne ,ba dai koyarwa na ko da wane lokaci ba. Saboda haka wannan urfin mutanen za ka za ka koma ka gain ya suke yi ala ayyu halin dai, shine cewa ya halatta, tun da shi an hana masa wata sana'a kenan don ya shagalta da koyarwa.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam idan iyaye suka doki yaronsu har suka ji masa rauni. Ko akwai wani hukunci da ya hau kansu?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, lallai za su biya diyya. Sai a yi kimar wanan raunin da suka ji ma 'ya'yan, sai su biya 'ya'yan. Da ma tun asali bai kamata a daki yaro a ji masa ciwo ba. Ya kamata in ya kai ma za a buge shi, to ya zamana an yanke masa hukunci ne a kotun gida, bayan an yi masa uzuri, kila ba laifin farko ne ba, ba na biyu ne ba, ba ma na uku ba ne, ya cancanci a yi masa bulala. To, sai a ce an yanke masa hukunci za a fyada masa rula a tafin hannu har sau uku, rular a kwance, ba a kaifin ba, karamar rula. In wata rana ya sake sai a yanke masa hukunci kila sau biyu. Har ma ina magana da yara, wata rana na ce, kila da hankici za a buge shi. Karo na biyu ne sai a ce da rula za a buge shi. Amma da ma ba ana dauko tsumagiya ba ne a dunga tsala ma yaro ko ta ko'ina ba, ba a yin haka nan. Ana yanke masa hukunci ne. Bulalar kuma ta kowane hali, kar ta kai goma, ko kuma in ce kada ya wuce goma.

TAMBAYA: Wa zai yi masu alkalanci?

SHAIKH ZAKZAKY: Shi a kansa yana iya ma kansa adalci. Sai ya kiyasta ya biya, ko ya sami wasu su yi masa kiyasi, sai ya biya. An ce Imam Khomaini ya taba biyo 'ya'yansa yana dan ba su tsoro kamar zai buge su, amma ba zai buga din ne ba, to sai daya ta fadi ta ji ciwo, sai ya sa aka yi kimanta, sai ya biya ta.

TAMBAYA: Yayan mahaifina yakan zagi mahaifiyarmu a gabanmu saboda Harkar Musulunci. Za mu iya mayar da abin ba komai ba, mu hakura, ko kuwa akwai matakin da za mu iya dauka?

SHAIKH ZAKZAKY: Abin da ya kamata, wannan su kai shi kotu ne a ladabtar da shi, don ba abin da ya hada shi da ita. Matar dan uwa ne, muharramarsa ce, kuma ita ajnaba ce a wurinsa, ba abin da ya hada shi da ita. Ko da a unwanin ladabi ba abin da ya hada shi da ita. Saboda haka ya kamata su kai shi kotu ne.

Post a Comment

0 Comments