Tambaya Da Amsa Karo Na 3

Tambaya Da Amsa Karo Na 03

Tambaya da Amsa karo na 03


TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan za ka yi tafiya, da ka fara ganin daji shi kenan kasaru ta kama ka ko kuwa?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ba inda aka fadi haka nan. Ba a ce sai in ka ga daji ne za ka fara kasaru. Tana iya yiwuwa ma a yanzu yadda wurare suka caccanza, ina jin sai ka yi tafiya wanda ya kai 'musafa' ba ka ga dajin ba ma samsam, saboda duk an bi an nonnome wurin, an yi gidaje wurare da kauyuka da sauransu. Tun farko ma ba a taba cewa daji ba, abin da aka sani shi ne, idan ka bar ganuwar gari ko kuma ka daina jin sauti da ganin garin a lokaci guda, idan garin maras ganuwa ne. Saboda haka tun farko ba inda aka taba cewa in ka ga daji ballantana maganar daji ya fito. Kuma mafaran kasaru shi ne makaransa in ka dawo.

TAMBAYA: Akramakallahu. Menene hukuncin ajiye kare a cikin gida?

SHAIKH ZAKZAKY: To, haramun ne mutum ya ajiye kare in ba bisa wata lalura ba. Akwai wuraren da aka halatta amfani da kare, kuma wannan zai iya yiwuwa ya halatta a ajiye shi domin wannan amfanin. Amma haka kawai a ajiye kare domin nishadi kamar yadda mutane sukan yi na sha'awa, to wannan ya haramta ga musulmi. A inda kuma ya halatta, shi ne kamar wajen farauta don neman abinci, ko don gadi, inda wani abu ba zai tsaya ma a matsayin karen ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Na ga wasu sukan yi shafa'i sai su bar wutiri. Shin haka bai da wata matsala?

SHAIKH ZAKZAKY: To, duk salla raka'a biyu sunanta shafa'i. Amma dai ana son in mutum zai yi wutiri, to ya yi raka'o'i biyu saukaka kafin ya yi wutirin.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ni Malamin asibiti ne, wata mata tana nakuda, amma mijinta da iyayenta ba su kai ta asibiti ba, sai suka nemi da in duba ta. Da na je sai na yi mata allurar da ta dace, sai abin ya hadu da karar kwana. Idan mijinta da iyayenta sun yafe, kaffara ta hau kaina?

SHAIKH ZAKZAKY: (To, ya ce dai allurar da ta dace, a nazarinsa). Watakila wannan za a kai hukuncin wajen wani ne ba shi ba, ya ga ko allurar ta dace. Idan ya tabbata cewa allurar da ya yi ne ya yi sanadiyyar mutuwarta, to lallai kaffara ta hau kansa ko da sun yafe masa diyya. Idan kuma ba allurar ne ta yi sanadiyyar rasuwarta ba, to ba wani abin da ya hau kansa. Amma wannan kamar yadda na ce, hukuncin ba shi zai yi ba, sai a kai ma wani wanda ya fi dacewa da sassan wannan. Ya ce allurar ta dace, saboda haka mutuwar Allah da Annabi ne ta yi, ko kuma ya sami tangarda wajen yin allurar, ta yiwu maganin allurar ya dace, amma wajen yi ya dan janyo sanadiyyar ta rasu.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Shin ya halasta na yi shamfo don mijina?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ni ban san Shamfo ba. Amma dai abin da zan iya cewa shi ne duk abin da ba a hana ka ba a shari'a, shi kenan kana iya yi. Amma ban san menene Shamfo ba. Amma in dai shi ne mace ta fece gashinta ta shafa masa mai maimakon ta yi kitso, ko kuma ta yi kitso, to ta samu ta yi kowanne, duk halas ne.

TAMBAYA: Akramakallahu. Shin ya halasta in yi amfani da magani domin jin dadin jima'i.

SHAIKH ZAKZAKY: Idan ba zai cutar ba, babu laifi, sai dai kuma barinsa shi ne a'ala. Saboda galiba abubuwa sukan zama suna samar da wani irin sakamako. Wala'alla yanzu ya zama ya yi dadi amma daga baya ya kawar da sha'awa ko kuma ya rage karfi.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Shin ya halasta in yi amfani da mai na shafe-shafe don canza fatar jikina?

SHAIKH ZAKZAKY: Shi ma in ba zai cutar ba, in ba zai cutar da mutum ba, babu laifi. Sai dai bari zai fi, don galiba wadanan abubuwan wani lokaci sukan haifar da wadansu abubuwa daga baya, ko da ba a sani ba yanzu. Amma in an aminta cewa babu wani cuta dangane da shi, babu komai. Tana iya yiwuwa mutum ya ce ai Shaidan ya ce zai yi wa mutane wahayi su canza halittar Allah, to an fahimci cewa canza halittar Allah din shi ne umurtar su da su yi wadansu miyagun ayyuka wadanda suka saba ma yadda aka sani bisa fitira da ma dabi'a ta mutum, kamar yadda ya yi masu wahayi na yadda maza ke zaike wa 'yan uwansu ko mata suke zaike wa 'yan uwansu (Ludu ko madigo), yana daga cikin canza halitta din. Da ire-iren wadansu abubuwan da Shaidan yakan kikiro su. Hatta ma shi wancan canje-canjen fata din in ta kai ma mikidarin wani aiki da wahayin shaidan, to shi ma yana iya zama irin haka din.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Meye hukuncin karin jini a asibiti, alhali jinin najasa ne kuma ba ka san jinin wanene ba aka kara maka?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai shi karin jini ba shan jini bane, shan jini ne ya haramta. Kuma na san ko da ma nama ne, ai ba a cin na mutum. Saboda haka in dai karin jini ne ko ma karin fata ne, in zai yiwu a yanko fata daga wani wuri a dasa ma wani ya dasu, shi ma zai zama babu laifi da shi. Kuma wannan ma ko wane iri ne, ko da kofiri ne ko musulmi ne shi, idan jinin nasa ya shiga cikin jikin nasa, insha Allahu ya zama jinin musulmi.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, kusan a kowane lokaci idan ina salla ni kadai sai na samu shakku a cikin sallata, kuma na fi samun shakka a wajen zaman tahiya na farko. Malam me ya kamace ni?

SHAIKH ZAKZAKY: To, mai yawan shakka, yana mantawa da shakkan ne. Zai dauka sallarsa ta yi daidai, ya manta da shakka. Don in na fahimce shi, shi mai yawan shakku ne, shi kuwa mai yawan shakku yana mantawa da shakkar ne, musamman in ya zama duk salla sai ya yi shakka, to shi kenan sai ya manta da shakkar kawai.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ni ne ina salla, na manta ban yi tahiya ta farko ba, kuma ban tuna ba sai da na mike na fara karatu. Me ya kamata in yi a wannan lokaci?

SHAIKH ZAKZAKY: Zai ci gaba da salla ne, sai in ya sallame sai ya rama zama na farko. Zama na farko da sujada daya in an tsallake su, ana biyan su a wajen salla, ana kada’insu. Amma banda wadannan ba wanda ake yin su a wajen salla. Wato bayan ya sallame sai kuma ya sake yin tashahhud, a na tsakiya din kenan da bai yi ba.

TAMBAYA: Akramakallahu, ni ne zan yi tafiya, amma ban bar garinmu ba sai da zawwal na lokacin salla ya shiga, amma farkon shigar lokacin ne na bar gari, misali karfe 1 na rana. Shin in na je tafiyar nan, kasaru zan yi ko, kuwa duk zan yi ihtiyadan?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ashe shi kansa ma ya san amsa din kenan. Tunda cika salla ya kama shi yana gida, to lallai ko ya yi tafiya din cika salla zai yi, kuma sai ya yi kasaru, Ihtiyadan. Haka zalika ma, abin da bai tambaya ba, in zai dawo gida, to idan lokacin salla ya same shi yana kan tafiya, sai ya iso gida bai yi sallar ba, idan yana nan a lokacin, to zai cika salla ne, sai ya yi kasaru ihtiyadan. Amma shi ihtiyadan na farko ya fi karfi. Lallai shi wannan duka sallolin biyu sun hau kansa, sabanin na dawowa gida, in dai lokacin salla bai fita ba, in ya cika shi kenan, ihtiyadan, bai zama lazim ba.

TAMBAYA: Allah ya kara wa Malam lafiya da kariya. Na wayi gari da azumi, saboda wani dan uwa ya ce an ga wata. Amma sai na ji a BBC an ce sai gobe ne za a dauki azumi, sai na ci abinci. Daga bisani kuma sai Maigidana ya ce lallai duk ’yan uwa suna azumi. Me ya hau kai na?

SHAIKH ZAKZAKY: To, in dai kamar bayanin da ya yi, shi ya dauka an ga wata, sai kuma ya dawo ya dauka ba a gani ba, sannan sai ya dawo ya tabbatar cewa an gani, saboda haka ya ci abinci da tsammanin ran nan ba Ramadan ba kenan. Saboda haka yanzu abin da ya hau kansa kawai shi ne ya yi ramuwa.

Post a Comment

0 Comments