Tambaya da Amsa karo na 23
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, akwai kayayyakin da jama'a suka manta a hannunmu, kuma sun yi shekaru akalla biyu ba a sami masu su ba, shin za a iya amfani da kayayyakin, ko ko me ya kamata a yi?
SHAIKH ZAKZAKY: Wannan dai hukuncin tsintuwa ne. Wanda yake abin da ya kamata shi ne in an tsinci abu a yi cigiya. Tana iya yiwuwa mutum in ya zo wannan Cibiya din za a tsammaci mai yiwuwa ya dawo. Saboda haka idan an fahimci mai yiwuwa ya dawo ne, yana iya yiwuwa a yi cigiyar a nan. Idan kuwa ana jin ya tafi kenan kuma ana tsammanin mutanen wuri kaza ne da suka zo, to ya kamata a yi cigiya a can. Kamar wani lokaci mutanen wani wuri sukan zo su bar wurin. In aka tsinci wani abu, ka ga abin da ya fi alheri shi ne a bincika can inda ake tsammanin za a same su. To har idan ya zamana ya shekara ba a sami mai abin ba, to sai a koma ga yadda ake sarrafa kayan tsintuwa. An samu a maishe shi sadaka don amfanin kowa. Kamar, tunda nan Cibiyar don amfanin al'ummar musulmi ne, a maishe shi don amfanin kowa da kowa. Ko kuma a sayar a zuba kudin a cikin asusun da zai shafi al'umma gaba daya. Amma duk wannan fa da sharadin, duk ko bayan shekara nawa ne, ranar da mai shi ya zo yana tanbayar kayansa, to za a biya shi. Wannan shi ne hukuncin tsintuwa.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Mutum ne ya saki matarsa, sai wani ya aure ta bayan ta yi idda, sai kuma daga baya yake yi wa wanda ya aure ta waya yana gaya masa cewa ya yi aure cikin idda, har ma yake gaba da wannan dan uwa. Ya mutum zai yi a irin wannan halin?
SHAIKH ZAKZAKY: Ba waya ya kamata ya rinka yi yana ce wa wancan ya yi aure a cikin idda ba, sai ya kai kara Kotu, ya kawo hujjojinsa. Idan ya tabbata haka nan ne, ka ga kotu sai ta yi hukunci. Amma ba shi ne zai iya zama alkalin wannan ba. Yanzu abin da muka fahimta, shi wannan wanda ya yi auren ya auri matar ne a kan ta gama idda. To in shi wancan yana da hujjar cewa tana nan a idda, to sai ya kai kara, ya kawo hujjarsa. Amma buga masa waya bai ce komai ba. Sai ya yi banza da shi tunda shi dai bai san ya aure ta da idda ba.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam idan mutum alwalarsa ta warware a cikin sallah, alhali shi ne Liman yaya zai yi? Zai fita ne kawai ko kuwa zai nuna wata alama ce? Idan akwai wata alama da zai yi a yi min bayani.
SHAIKH ZAKZAKY: Idan ya fara salla dinsa da alwala tare da jama'a, to yayin da alwalarsa ta warware, to su sallarsu ba ta warware ba, sallarsu tana nan. Saboda haka sai ya yi masu ishara da cewa shi kam sallarsa ta warware. Tunda ma ta warware din ne, ko magana yana iya ya yi, ya ce shi fa yanzu shi kenan. Ko kuma ya yi abin da wadansu sukan yi, ladabi, don kar ya zama a gane, tunda da kunya a ce alwalar Liman ta warware. Sai ya rufe hancinsa ya nuna kamar habo ne ya zubo masa, sai ya dan nuna alamar habo, sai ya fita a guje, ya yi waje abinsa. To su kuma a nan sai su cika sallolinsu. Kowa ya zama mustakillin kansa ba Liman.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Gafarta Malam da yake sharadin tuba akwai mai da hakki ga mai hakkin, to idan mutum ya zalunci wani mutun misali Naira 100 shekaru 10 da suka wuce, to yanzu idan yana son ya mai da masa da hakkinsa Naira 100 zai mai da masa ko ya zai yi? Da yake yanzu darajar 100 ta fadi, zai kwatanta darajar ne ko kuwa?
SHAIKH ZAKZAKY: Eh! lallai haka din ne saboda shi dama ita Naira a kashin kanta ba dukiya bace, kimanta dukiya ake yi da ita. Da dinare ne da aka yi shi da nakash dinsa da narkakken zinari, to in dinari 100 ne, yanzu ya dauko dinari 100 za a sami darajarsu a abin da za su saya kila ya zama daidai wa daida, koma na yanzu ya fi yawa, saboda mai yiwuwa shi dinarin yanzu ya kara daraja ne. Dinarin zinariya, kara ma daraja yake yi, ba raguwa ba. To tunda shi wancan kima ne, lallai sai a kimanta abin da Naira 100 zai iya saye shekara 10, a ga nawa ne ya kamata ya kasance yanzu.
TAMBAYA: Idan mutum yana takalidi da wani Marji'i zai iya yin aiki da fatawar wani Marji'in na daban a kan wata matsala kafin ya samu fatawar Marji'in da yake takalidi da shi?
SHAIKH ZAKZAKY: To shi Marji'in da yake takalidi da shi din, fi ma la budda yana da fatawa a kan wannan abin da yake tambaya. Mai yiwuwa ya ba shi fatawa a kan wannan. Saboda haka sai ya koma ga wannan. Allahumma sai dai in ba shi da fatawa sam game da wannan. Bai ce in ya kawo wani abu yana iya daukar na wani ba. Amma in haka nan ne, sai mu ce, to sai ya koma ga misali ga wani Marji'i a kan fatawar da shi nasa Marji'in bai yi ba samsam. To shi kuma wannan zai yi Mura'atin a'alamiyya a kan wanda zai koma wa din. A'alam fal a'alam a kan matsalar da zai koma wa wani Marji'in. Ala ayyi ahalin tunda dai yana magana batun Marji'i ne, fi ma la budda Marji'in ma yana da fatawa a kan wannan.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, menene hukuncin inshora a Musulunci? Da yake na ga kamar motar da ake sayar da ita dubu 600, amma idan na Inshora ne sai a ce dubu 800.
SHAIKH ZAKZAKY: Ba wani abin da ya haramta yin inshora a cikin addini. Illa iyaka dai in a bisa ka'idar addini ne dole ya zama cikin abin da ake yi, an fid da duk abin da zai yi kama da caca, sai ya zama tamkar alkawarin yarjejeniya ne tsakanin bangarori biyu. Daya ya dauki alkawarin indai ka ba shi kaza, ka yi hasarar wannan abin zai biya. Abin kyama dangane da al'amarin inshora shi ne akwai kama da caca, caca kuma ta haramta. To amma in aka kawar abin da ya yi kama da caca din a ciki, to babu laifi da shi.
TAMBAYA: Malam ina hukunci zama da mace wacce ba muharramar mutum ba a kujera daya ta motar haya da ake yi a kasar nan?
SHAIKH ZAKZAKY: Lallai gwama jiki da ajnaba da ma haramun ne. Saboda haka don kasantuwar mutane suna yi a nan ba yana nufin daidai bane, sai a yi kokari a ga an gyara. Ala ayyi halin akwai wasu wadanda yake su a motarsu suna kiyaye wannan, cewa akan yi sashen mata daban na maza daban. Sai dai idan ma'aurata biyu ne suka zabi su zauna kusa da juna.
0 Comments