Tambaya Da Amsa Karo Na 18

Tambaya Da Amsa Karo Na 18

Tambaya da Amsa karo na 18


TAMBAYA: Akramakallah, ko ya halasta ga likita ko mai ba da magani ya bayar da maganin da zai zubar da ciki ga matar da ta zo tare da mijinta saboda tana shayar da wani yaron?

SHAIKH ZAKZAKY: Idan dai ciki din ya kai wani mikdari wanda ana iya cewa an sami kamalan da a ciki, to zai zama ma kisan kai ne, sai dai hukuncinsa ba irin na a kashe mutum bane. Zai zama akwai diyyar tayi, wanda shi ne za a biya. Amma idan bai kai nan ba, sai a ce sun aikata haramun. Ba inda aka ce miji da mata sun samu su zubar da ciki, lallai ba su sami haka nan ba. Ta hanya guda ce zubar da ciki zai iya halasta, shi ne inda binciken Likita ya nuna cewa imma dai ta haihu ta mutu ko kuma a zubar da ciki din, to wannan ne kawai. Don a ceci nata ran, sai zabi tsakanin abin da yake cikin cikinta don a ceci ranta, wato a fifita rayuwarta a kan abin da yake cikinta. Amma in ba ta wannan fuska ba, ba ta inda zubar da cikin yake halatta.

TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, mutum ne yake bin mazhabar Maliki, sai ya ga wani hukunci a wata mazhabar, shin ya halasta ya dauka ko a'a?

SHAIKH ZAKZAKY: To wannan in ya tambayi Mazhabar Malikiyya zai ji bayani sosai. Duk ma'abota Mazhabobin nan na Ahlus sunnati ba wanda ya ce shi Mazhabarsa ita ce kawai addini, an gama. Har ma akwai wadanda suke cewa in an ga wani abu wanda ya fi nasu, to a koma ga wancan. Kuma cikin masu fadin wannan har da shi Imam Malik, Limamin Mazhabar Malikiyya din. Kuma kamar fadin Shehu Usman Danfodiyo da yake cewa, Ka sani ya dan uwa Allah bai lizimta mana wata mazhaba, ya ce ga mazhaba wance za ku bi ba. Mazhaba tamkar ra'ayi ne na wannan Malamin, abin da ya tafi a kai. Saboda haka yana da madogara, imma dai fahimtarsa ko kuma ya dogara da hadisi. Saboda haka ba a kayyade ka da bin mazhabar Malikiyya lazim ba, ko da ka ga wani abu a wani wuri, wanda yake ya fi na Malikiyya; wajibinka ne ma ka koma ga abin da ya fi na Malikiyya in ka gani.

TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, shin da gaske ne zakka ba ta hau kan takardar kudi ba?

SHAIKH ZAKZAKY: Akwai abubuwan da aka ambata wadanda zakka take hawa kansu, ciki har da zinare da azurfa. Saboda haka in ana batun jimlar dukiyoyi ne, ka ga zinare da azurfa ne, su ma din zinare da azurfan, wadanda aka maishe su kudi na kashewa, aka yi masu tambari kenan, Nakash, aka ce masu Dinar da Dirham. Sune ake da kiman dinare 20 ya kai nisabi ko Dirhami 200, cikakken mulki, cikakkiyar shekara, sannan zakka ta hau kansu. Amma shi kudi irin wannan wanda muke yi da takardu, to zakkarsu ba zai zo a babin Dinari da Dirhami ba, sai dai ya zo a babin zakkar ribar dukiyoyi, wanda yake mustahabbi ne yin haka nan. Saboda haka ka ga za ka iya ba da zakka kenan da Naira, amma ba a unwanin Dinari da Dirhami ba, a unwanin ribar ciniki. Saboda haka muna iya cewa a unwanin ribar ciniki, eh zai iya hawa, amma ba a unwanin dinare da azurfa ba. Domin kuskuren da wasu suke yi shi ne sun dauka shi takardar kudin shi ne za a komar da kimarsa a dinare da dirhami a ba da zakka. In haka ne sai mu ce a'a. Ba ina nufin Naira ta arce wa zakka ne kwata-kwata ba, za ta iya shiga a wani babin.

TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, yaya ake zama da matan aure fiye da daya a mazhabin iyalan gidan Manzo?

SHAIKH ZAKZAKY: Wannan yana bukatar ya karanta babi, ko ma littafi sukutum wanda ya shafi wannan. Amsa irin wannan ba za ta wadatar da shi ba. Amma illa iyaka, shi zama din ya shafi abubuwa da dama. Ya shafi kyakkyawar mu'ashara, ya shafi nafaka, ya shafi rabon kwana, ya shafi tufatarwa da wurin kwana da ire-irensu wadanda suke lallai ba zai yiwu in amsa masa a cikin dan gajeren magana ba. Sai dai in ce ya duba Risala amaliyya ta wani Mujtahidi dangane da abin da ya shafi wannan. Da ma littafai da dama wadanda suka shafi sha'anin zaman iyali, wanda yake kuma irin su na da yawan gaske a rubuce-rubucen Malamanmu. Alal misali yana iya duba littafin Ayatullahi Muddahari dangane da Matsayin mata a Musulunci. Da kuma littafin Ayatullah Ibrahim Amini, dangane da zaman iyali. Da kuma wadansu littafai masu dama wadanda suka shafi wannan bangare. Insha Allahu zai sami bayani.

TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, yaya ake neman aure da kuma ka'idodinsa a Musulunci?

SHAIKH ZAKZAKY: A takaice dai waliyyan mace su suke ba da aurenta, kuma su akan bidi auren a wurinsu, ko da kuwa za mu kaddara cewa ma'aura biyu din - mace da namiji - sun ga juna suna son juna, amma dai za a kai magana ta aure ne wajen waliyyinta a bida. A yayin da aka amsa za a daura masu aure akwai abin da ake ce ma khidba, in aka amsa cewa wance za ta auri wane, to bayan wannan kuma zai zama haramun wani ya zo ya ce shi ma yana son ya aure ta. Sannan kuma sai akadi, wanda yake shi kalmomi ne na siga da suke tabbatar da shi, wanda yake dole ya samu ijabi da kabul, wato "na aurar," "na karba." "Na aurar," a bangaren Waliyyi, "na karba," a bangaren mai aure ko Wakilinsa "Na karba masa," Wane misali. Sai kuma lazim sadaki, sannan akwai i'ilanin aure, walima. Karin bayani yana iya duba littattafan fikihu da suka shafi babin aure.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ina gaskiyar hadisin nan da ake cewa wai Manzon Allah (S) ya ce idan talauci ya damu mutum ya kara aure?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ban san inda ya ga hadisin ba, kila yana ji ne a rediyo. Irin wadannan hadisan kuwa na rediyawa suna da yawan gaske, ba lalai ya zama Annabi ne ya fada ba, kamar wannan, ba a san Annabi ya fadi haka ba. Amma tana iya yiwuwa a cikin littafai masu kwashe-kwashe, wadanda ba su yi la'akari da ingancin abu ba, ya aka same shi. Amma gaskiyar magana shi ne, wannan bai inganta ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Daga wane lokaci ne hidimar 'ya'ya ke fadi daga kan iyayensu, wato daukar dawainiya?

SHAIKH ZAKZAKY: Wajibi ne mutum ya ciyar da 'ya'yansa da ba su balaga ba, amma ba za mu ce hidimar ta fadi ba ne, sai dai mu ce wajibcinsa. Zamansa dole, shi ne bai zama dole ba in sun balaga, amma ba ya fadi ba ne. Ka ga shi ya ce ya fadi ne, ka ga kuwa in abu ya riga fadi shi kenan yana nufin ba zai yi ba kenan. Amma wajibi, ya zama wujuban ya ciyar da 'ya'yansa wadanda ba su balaga ba. Iyayensa kuma wadanda suka yi rauni, ya zama wajibi a kansa. Amma idan iyayen suna da wadata, ko kuma suna da karfinsu, bai hau kansa ba. Haka ma 'ya'ya, idan suka balaga, shi kenan bai hau kansa ba. Amma kalmar fadi, shi ne bai kamata ya fito ba a nan, sai dai a ce bai zama wajibi ba, amma ba ya fadi ba.

Post a Comment

0 Comments