Tambaya Da Amsa Karo Na 11

Tambaya Da Amsa Karo Na 11

Tambaya da Amsa karo na 11


TAMBAYA: Akramakallah. Duk lokacin da nake salla sa hutu ya rika zuwa mani amma sai in rika matsawa sai wasiwasi ya rika zuwa mani. To yaya zan yi?

SHAIKH ZAKZAKY: Akwai haddin da zai zama salla ta baci. Amma idan dai har mutum ya ji, ya rike, ya zama bai hana dumanina ba (abin da ake ce ma dumanina, natsuwa a salla ba), ya zama shi kenan sai abin ya koma bai fito ba, shi kenan zance ya kare ba wani abu. Amma da zai zama suna ta kokawa da shi, har ya rasa natsuwa, to salla ta baci, saboda natsuwa salla wajibi ne.

TAMBAYA: Akramakallah. Na dauki ruwan da abokina ya ajiye na yi alwala da shi, amma ba ya nan, amma ina da tabbacin cewa in yana nan ba zai hana ni ba. Yaya matsayin sallata?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai wannan ba komai saboda shi abin da al'ada ta riga ta gudana kan cewa ana iya amfani da shi na ruwa, shi kenan ba komai, ko da ba da izinin mai ruwan ne ba, in dai ka san al'adar mutane an saba irin wannan, in an ga ruwa haka nan ana iya amfani da shi.

TAMBAYA: Allah ya ji kan Malam, ana cewa fita jihadi sai da yardar iyaye, kuma idan mutum ya je ba da yardarsu ba aka kashe shi, bai yi shahada ba. Ya abin yake?

SHAIKH ZAKZAKY: Cewar bai yi shahada ba, lallai ban san wannan ba. Saboda shi izinin iyaye ga yaro karami wanda bai balaga ba, hakki ne na iyaye din, amma ba a ce in ya je ya yi shahada kuma shi ba shahidi ne ba! Sai dai hakkinsu ne yaro, karami, wanda bai balaga ba shi ma ake nufi, ya nemi izini. Ba a ce baligi, magidanci shi ma sai ya nemi izinin iyayensa ba. Saboda haka hakkinsu ne ga yaro karami ya nemi izininsu. Haka ma yanzu wannan jihadin kila yana fadin abin da yake kila karantawa kawai, to hatta ma kamar azumin nafila misali, ko wadansu ayyuka irin wadannan na nafila, shi ma sai da izinin iyaye. Amma ba a ce in ya yi ba da izinininsu ba, ba shi da lada ba. Ba a ce haka nan ba, sai dai hakkinsu ne, ya kuma kamata ya ba su.

TAMBAYA: Akramakallah, menene hukuncin a mayar da bunsuru taure ta hanyar dandaka?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai malamai sun nuna cewa in dai don gyaran nama ne kuma bai cutar da shi bunsurun ba, shi kenan. Akwai fidiya akwai dandaka. Na'am tana iya yiwuwa daidai lokacin da ake yin bunsurun ya dan ji wahala, to amma daga baya shi kenan zai yi nasa sha'ani, tunda dai bunsuru ne, babu laifi. Amma ga mutum namiji bawa, shi wannan haramun ne, wanda har yanzu abin mamaki a wadansu wurare ana yi. Sai a ce wannan bawa ne sai a dandake shi, a sa shi ya shiga cikin mata yana masu hidima. To wannan kam ya haramta.

TAMBAYA: Assalamu alaikum Malam. Na yi alwala sai na ci goro, ina cikin salla sai na ji shi a bakina har na dan hadiye, ya matsayin sallata?

SHAIKH ZAKZAKY: To babu laifi ga wani dan abin da ba a ka rasa ba, wanda ya dan kude ma mutum a baki, ba da shi ya ji shi ya yadiye shi da unwanin yana ci ba. Amma da da ya ji dan kulun goro din, ya dan ji ashe dan ragowar goro ne, sai ya dan tauna da gangan, to za mu ce ya ci goro. Amma idan dai kawai haka nan sai ya ji dan miyau ko ya hadiye, to ba sunansa ci bane. Ma'ana ci da sha su suka haramta a salla. Amma idan wani abu ya shige bakin mutum ba da unwanin ya ci ko ya sha ba, to ba zai zama ya bata masa salla ba. Saboda haka muna iya cewa in dan guggubin ya ji shi ya yi ta'ammudin taunawa musamman da nufin yana cin goro, sai a ce ya ci goro. Amma in don wani dan bangare ya dan fada masa a baki tare da miyau, wannan ba komai.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ko zan iya in bi jam'in salla a bayyane, alhali ina nufin salla ni kadai?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh! ya halatta. Kuma kana iya ruku'u da sujada tare da Liman alhali kai da unwanin kai kadai kake salla. Kuma ma kana iya bin Liman a wani wuri a wani bangare na sallar kuma ka koma kana yi kai kadai a wani bangare, wato kamar dama can ka fara bin shi daga wani lokacin, kuma sai ka yanke shawarar ka fasa bi, yanzu ka zama mai sallarka.

TAMBAYA: Akramakallah, ko ya halasta mutum ya dauki dan siyasa a mashin su tafi kamfe a matsayin haya?

SHAIKH ZAKZAKY: To, shi dai da a ce misali zai dauki mutum ya kai shi wani wuri ne shi kenan, daga nan sai ya biya shi ladansa, to sai mu ce wannan babu laifi da shi. Amma idan misali in zai shiga kwararon kamfen din ne ana fantsan-fantsan a manna wa mashin din Fosta, shi kuma a rika cewa sai wane! To lallai yana kamfe ne. Kuma abin da ya same shi a tafarkin wannan kamfe din dai yana daidai da abin da ya shafi wadancan. Alal misali kila ma ya yi shahada a wannan kamfe din. Alal misali ya dauke su ne suka lika fosta din suna kamfe din su, tana iya yiwuwa 'yan adawa su far masu. To ka ga a nan ma tana iya yiwuwa wa ya yi shahada a wannan kamfen, ka ga ya yi shahadar siyasa kenan ko? Saboda haka ya danganta da yadda al'amarin yake ne. Amma in misali wannan dan siyasa ne (ya ce) ka dauke ni ka kai ni wuri kaza, kuma wurin nan za ka je ka sauke shi ne, shi kuma can za shi kamfe ne, ka ga ai wannan kai bai shafe ka ba, za ka iya yi. Kai ba kamfen kake yi ba. Amma yanzu ka dauke shi ku bi titi yana wakar jam'iyyarsa, ana haya-haya, ana yabo, ana zagi, har ma a harbo dutse, to ke ga kana cikin kamfe. Saboda haka makomarka makomarsa kenan.

TAMBAYA: Mutum zai iya canza taklidi daga Mai risala zuwa Mujtahidi?

SHAIKH ZAKZAKY: To ni ban san ma'anar Mai risala ba. Domin abin da muka sani (shi ne) ana yin taklidi da Mujtahidi ne, shi Mujtahidi ne yake rubuta Risala. Risala kamar sako ne na hukunce-hukuncen da shi Mujtahidin ya rubuta. (Saboda a nan kamar abin da ya nuna kamar Mujtahidi daban, Mai risala daban. Da ma abin da yake tambaya shi ne mutum yana iya canza taklidi daga Risalar wani Mujtahidi zuwa Risalar wani Mujtahidi, wanda yake nufin kawai daga Mujtahidi zuwa wani Mujtahidi, tambayan kenan). Sai mu ce masa, in haka nan ne daga Mujtahidi zuwa Mujtahidi yake nufi, sai mu ce eh! Amma kalmar Mai Risala, lallai ba ta da wani ma'ana a nan, don Mujtahidai ne ke rubuta Risala, kuma ba masu Risala ake ce masu ba.

TAMBAYA: Allah gafarta Malam, Ko wa za a ba khumusi?

SHAIKH ZAKZAKY: Zai bayar da shi ne ga Mujtahidi Fakihi wanda ya cika sharudda, ko Wakilinsa.

TAMBAYA: Akramakallahu, mutum ne ya sadaukar da sadakin diyarsa, wato shi zai biya sadakin sadaka, amma sai ya ki biya har lokaci mai tsawo. Ina matsayin wannan auren?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ba mu san wani abu wai shi sadaukar da sadaki ba. Abin da aka sani shi ne ana sa sadaki a biya. Wannan wani abu ne da mutane suka kirkira ma kansu, suna cewa wai sun sadaukar, har ma kuma ana ce ma diyar ma 'yar sadaka, wanda duk ba a san shi ba a shari'a. Amma abin da za mu dauka, shi wannan tun da shi ya dauka sadaki ya hau kansa ya biya sai bai biya ba, ya zama ana bin sa bashi ke nan. Amma in ya aurar da yarinyar ne a kan cewa ba sadaki, to ba ma auren.

TAMBAYA: Akramakallahu. Ina matsayin yin allura da rana a watan Ramadan?

SHAIKH ZAKZAKY: Ba laifi da shi.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, mutum ne zai yi tafiyar da ta isa kasaru a watan Ramadan, kafin ya bar gida sai ya ci abinci, sai bayan da ya fita, sai ya ji ashe ba a cin abinci sai an fara tafiya. Ina matsayin wannan azumin na wannan rana?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ya yi ganganci, don ya kamata mutum ya san hukuncin abu kafin ya aikata. Don ya ji an ce akan sha azumi in ana tafiya, to da sai ya tambaya, ya sharadin abubuwan suke? Don ba ma kawai sai zawwal ba, sai ma a tafiyar tasa ya kai haddin kasaru, in ya fita ma tafiyar, bai kai haddin da za a yi kasaru ba, lallai ma ba zai sha ba. Wato kamar yana cikin garin da zai yi tafiya din, bai riga ya fita ba, sai ya fita can bayan gari ya kai ma haddin kasaru, sannan yake iya sha. Saboda haka tunda ya yi wannan ganganci, za mu dauka bisa jahilci ne ya yi, wanda ya kamata za a yi la'akari da shi mutumin, Kaasiri ne shi, ko Mukassir. Wato wanda yana iya sani ne ya ki ya nemi ya sanin, ko kuwa ba zai yiwu ya sani ba ne; in ba zai yiwu ya sani ba ne, sai a ce ya rama, in kuwa zai yiwu ya sani ya ki sani, har kaffara sai ya yi.

Post a Comment

0 Comments