Takaitaccen Tarihin Shaheed Mudassir Mustafa
SUNANSA:
Mudassir, Sunan Mahafinsa: Malam Yusuf (Bala mai hula), Sunan Mahaifiyarsa Hussaina.
Shaheed Mudassir Ya Na Daya Daga Cikin Yan uwan Da Har Zuwa Yanzu Babu Labarinsu Da Haƙiƙanin Halin Da Suke Ciki. Sanadiyar Harin Da Sojojin Nigeria Suka Kai A Husaniya Da Gidan Sheikh Zakzaky (H) Dake Gyallesu A Ranakun 12-14 Disamba A Shekarar 2015.
An haifi Shaheed Mudassir A Cikin Karamar Hukumar Kudan Dake Jahar Kaduna Ta Nigeria. Shaheed Mudassir Ya Taso Da Karatu Inda Ya Yi karatun firamare a Makarantar "Yakubu Primary School Kudan. Daga Bisani Ya Dora Da Karatunsa Gaba Da Firamare (Wato Matakin Sakandire) A Government Secondary School Kudan. Baya Ga Haka Ya Yi Karatun Al’qur’ani A Wajan Malam Abubakar Gidan Mabuga Dake Garin Kudan. Tare Da Karatun Zaure A Hannun Malam ÆŠankaka, Da Wakilin Ƴan uwa Na Kudan Malam Muhammad Junaid Sani. Daga Bisani Ya Dora Karatunsa Na Diploma A Makarantar Dar’al Thaqalain Organization, Dake Cikin Birnin Kano. Wanda Bai Samu Damar Kammalawa Ba, Sanadiyyar Rasuwar Mahaifinsa. Wannan Sanya Dole Ya Dawo Gida Domin Ci gaba Da Kula Da Mahaifiyarsa Da Sauran Yan uwansa.
Daga Bisani Sai Ya Koma Ya Ci gaba Da Karatun Zaure A Hannun Mal. Sabitu Khalid Gami Da HaÉ—awa Da Sana’ar Hannu Ta Gyaran Waya Domin Kula Da Rayuwarsa Da Ta Mahaifayarsu Da Sauran Danginsa.
MU’AMALARSA DA AL’UMMA:
Ko Da Makiyin Shaheed Zai Yi Masa Shaida Da Cewa, Mutum Ne Mai Kyakykyawar Zamantakewa Da Jama’a. Domin Hatta Yan Izalan Unguwarsu, Sun FaÉ—a Dangane Dashi A Lokacin Da Suka Sami Labarin Abinda Ya Faru Da Shi Cewa; “Wannan Yaro (Mudassir) Yaron Kirki Ne. Domin Duk Cikin Yan Shi’ar Unguwarnan, Babu Mutumin Kirki Kamar Sa.
Baya Raina Kowa Koda Kuwa Wanda Ya Ke Kasansa Ne. Sannan Ba Ya WulaÆ™anta Kowa” Sabida Kyakykyawar Zamantakewarsa. Shahid Mudassir Ba Shi Da Abokin FaÉ—a. Domin Kuwa Hatta Mahaifiyarsa Ta Shaideshi Akan Hakan Cewa; "Shi Mudassir Mutum Ne Da Ya Iya Zamantakewa Da Kowane Irin Mutum. Domin Ko A Cikin Yan uwansa Ba Za Ka TaÉ“a Samun Wani Ya Kawo Kararsa Akan Ya Yi Masa Wani Abu Mai Muniba.Tabbas Shahid Mudassir Ya Sami Yabo Ta Janibin Zamantakewa Da Al’umma Domin Kuwa Yan uwanshi Sun Shaideshi Musamman A Bangaren Sada Zumunci.
Duk Da Kaurinsuna Da Wasu Suka Yi Na Masu Sana’a Irin Ta Shahid Mudassir Wajen Rashin Cika AlÆ™awari, A Sana’ar Gyaran Waya. Amma Tabbas Shahid Mudassir Ya Samu Kyakykyawar Yabo Daga Al’umma Wajen Cika AlÆ™awari Da RiÆ™on Amana Ga Duk Wanda Ya Bashi Aikin Gyaran Waya. HaÆ™iÆ™a Shahid Mudassir Ya RiÆ™e Sana’arsa Tsakani Da ALLAH. Hakan Ya Sanya Yake Yawan Samun Gyara Saboda RiÆ™on Amanarsa Da Cika AlÆ™awari.
Alhamdulillah Shahid Mudassir Ya Samu Kyakykyawar Shaida Daga Bakin Al’umma Ta Fuskacin Zamantakewarsa Da Al’umma.
SHAIDA AKAN SHAHID MUDASSIR DAGA BAKIN AL’UMMA:
Tabbas Shahid Mudassir Ya Sami Shaida Nagartacciya Daga Bakin Al'umma Dangane Da Halayensa. Mahafiyarsa Ta Bayyana Cewa;- “Ban Haifi Da Kamar Sa Ba Fatana Shi Ne ALLAH (T) Ya Sa Danda Aka Haifa Masa Ya Gajeshi, Sannan Ta Ce Na Yi Mafarki Da Shi Na Ganshi Cikin Kyakykyawar Yanayi. Sabida Haka Ni Na Godewa ALLAH (T) Tunda Da An Kasheshi Ne a Hanyar Addinin ALLAH (T)".
Ƴan uwansa Sun Shaidi Shahid Mudassir Da Yawan Kyauta Sannan Kuma Da Son Zumuci Wani Lokacin Akan Yi Mamakin Yadda Yake Da Yawan Kai Wa Danginsa Ziyara Domin Komai Nisan Waje, Zaka Samu Shahid Mudassir Baya Gazawa A Wajen Kai Ma Danginsa Da Abokansa Ziyara.
Abokinsa Kuwa Isma'il Yusha’u Ya Shaideshi Da Yawan Ibada, "Sallah, Azumi Da Yawaita Karatun Alqur’ani, Da Riko Da Addini" Hakan Ya Sanya Al’umma Da Yawa Suka Yi Koyi Dashi Wajen Tsaida Sallah Raka’a Hamsin Da Daya (51) A Kowace Rana.Girmama Al’umma Kuwa Ba’a Magana Domin Mutanan Unguwansu Cewa Suka Yi An Yi Rashin Yaro Mai Halin Manya. Wanda Baya Da Kyamar Kowa, Kowa Nasa Ne Bai San Wani Abu Wai Shi FaÉ—a Ko WulaÆ™anta Jama’a Ba.
Hakan Ya Sanya Ya Zama Abokin Kowa A Unguwarsu, Dama Faɗin Garin Kudan Baki Daya, Manya Da Yara, Kowa Yasan Shahid Mudassir Da Girmamawa Gami Da Bawa Kowa Haƙƙiin Sa.
DARUSSA DAGA RAYUWAR SHAHEED MUDASSIR:
Zantukan Da Aka Ambata A Baya, Dangane Da Rayuwar Shaheed Mudassir, Sun Wadaci Mai Karatu Ya Fahimci Cewa;- "Komi Na Rayuwar Shaheed Abin Koyi Ne Ga Al’umma. Ya Samu Shaida Akan Kyawawan Dabi’u Kamar;
Yawaita Ibada:
Shaheed Mudassir Ya Samu Shaidar Cewa;- Shi Mutum Ne Mai Tsanannin Son Ibada. Hakanne Ma Ya Sanya Ya Ware Daki Guda A Cikin Gidansa Bayan Ya Yi Aure Domin Yin Ibada A Cikinsa. Sannan Ya Sami Shaidar Cewa;- Shi Mutum Ne Mai Yawan Son Azumi, Musamman Ranakun Litini Da Alhamis Da Kuma Sauran Ranaku Da Suke Da Falala. Inji Abokinsa Isma’eel Yusha’u.Kyautarsa:
Shaheed Mudassir Mutum Ne Mai Yawan Son Ya Ga Yana Farantawa Muminai Ta Hanyar Yi Musu Kyauta Domin Kuwa Babu Yadda Za’a yi Su Zauna Da Mutum Na Tsawon Wani Dan Lokaci, Ba Tare Da Ya Yi Ma Mutun Kyauta Ba.Hakurinsa:
Kowa Zai Yi Shaidar Cewa Shaheed Mudassir Mutum Ne Mai Yawan Hakuri. Kamar Yadda Muka Ruwaito Daga Wajen Mahaifiyarsa Cewa “A Gaskiya Samun Mai HaÆ™urin Shaheed Sai An Duba. Domin Kuwa Duk Gidannan Babu Mai HaÆ™urinsa”.Sadaukarwarsa Ga Addini:
Shaheed Mutum Ne Da ALLAH (T) Ya Yi Masa Baiwar Sadaukarwa Ta Kowane Janibi. Jiki, Lokaci Da Dukiya Dama Rayuwarsa. Sadaukar Da Rayuwarsa Da Ya Yi Domin Kare Jagora, Wannan Babban Misali Ne Dangane Da Sadaukarwarsa. Abokinsa (Munir Abdullahi) Cewa Ya Yi, A Lokacin Da Muke Gyallesu A Lokacin Da Komi Ya Tsananta Muna Tare Dashi Kawai Sai Yake Cemin (Shaheed Mudassir) Malam Munir Kawo Hannuka, Muyi Musabahar Karshe. Domin Kuwa Ni Zan Kutsa Cikin Wadannan La’anannun. Idan Kuwa Kaga Na Dawo To Gawata Ce Domin Kuwa Ina Ji A Jiki Na Yau Ce Ranar Cika AlÆ™awarin Da Muka Yi Wa ALLAH (T) Da Jagoranmu”. Wannan ltace Karken Ganawar Shaheed Mudassir Da Abokinsa Munir Abdullahi.SHAHADARSA:
A Ranar Asabar 12-12-2015 Da Yamma Shaheed Mudassir Ya Sami Labarin Abinda Ke Faruwa A Husainiyya. Koda Samun Labarin Sa, Bai Tsaya Wata-Wata Ba, Take Ya Shirya Ya Wuce Zaria, Shi Da Abokanansa. Zuwansu Ke Da Wuya Suka Samu Babu Hanyar Da Zata Shigar Dasu Cikin Husainiyya Domin A Lokacin Sojoji Sun Tare Dukannin Hanyoyin, Hakan Ya Sanya Suka Yi Shawarar Wucewa Gyallesu Gidan Sayyid (H). Da isarsu ba tare da dogon lokaci ba, sojoji suka iso Suka Fara Ta’adancin Su. Wanda Hakan Ya Sanya Shi Ne Sanadin Rabautar Shaheed Mudassir Da Shahada (Ko Muce Ghaiba) Ta Sanadin Azzaluman Sojojin Nigeria Bisa Umarnin Gwamnatin Buhari.
Shaheed Mudassir Ya Yi Shahada Ya Bar Mace Daya Mai Suna Hafsat, Da Yaro Daya A Cikin Cikin Mahaifiyarsa; Wanda Aka Sanya Wa Yaron Sunan Mahaifinsa Mudassir.
Fatan Mu ALLAH Ya Albarkaci Iyalinsa Ya Kuma Saka Musu, Bisa Zalumcin Da Akayi Musu, Na Rabasu Da Masoyinsu.
Amincin ALLAH (T) Ya Kara Tabbata A Gareka Ya Shaheed Mudassir, Ranar Da Aka Haifeka, Ranar Shahadarka Da Ranar Da Za Ka Tashi A Gaban Ubangijinka Kana Mazlumi, Mai Arziƙi A Gareshi.
0 Comments