Shahid Mal. Aminu Aliyu Magaji

Shahid Mal. Aminu Aliyu Magaji Takaitaccen Tarihin Shaheed Mal. Aminu Aliyu Magaji (Haris)
SUNANSA:

Aminu, Sunan Mahaifinsa: Aliyu (Magaji), Sunan Mahaifiyarsa: Barakah.

Malam Aminu Ya Na Ɗaya Daga Cikin Ƴan uwan Da Har Zuwa Yanzu Ba’a Sami Tabbacin Rayuwa, Ko Shahadarsu Ba. Tun Lokacin Da Sojojin Nigeria Ƴan Ina Da Kisa, Suka Kai Harin Ta’addanci A Husainiyya, Da Gidan Sheikh Zakzaky (H) Dake Gyalessu A Ranakun 12-14 Ga Watan Disambar Shekarar 2015.

An Haifi Malam Aminu Mai Kimanin Shekara Arba'in (40) A Duniya, A Cikin Garin Kudan, Dake Jahar Kaduna Ta Nigeria. Tasowarsa Ya Fara Da Karatun Allo Ne, Bisa Al’ada A Gidansu. Sannan Ya Dora Da Karatun Zaure A Hannun Wasu Malamai Dake Ciki Da Wajan Garin Kudan.

MALAM: Ya Sami Wannan Sunan Ne (Malam) Sakamakon Kasancewarsa Ɗaya Daga Cikin Malaman Fudiyya A Garin Kudan, Malami Ne Wanda Ya Ke Koyar Da Ɓangaren Karatun Al Qur’ani, A Ɓangaren Yara Da Matan Aure (Sisters).

HARIS: Ya Sami Wannan Suna Ne Sakamakon Kasancewarsa Ɗaya Daga Cikin Jagorori, Kuma Manyan Jajirtattun Harisawa Na Yankin Kudan.

MU’AMALARSA DA AL’UMMA:

Malam Aminu, Ya Sami Kyakkyawan Shaida, Daga Bakin Al’umma. Ta Fuskacin Kyakkyawan Mu’amala Da Iya Rayuwa Da Al'umma. Tun Daga Tasowarsa Har Zuwa Lokacin Shahadarsa. In Da Ya Sami Yabo Daga Bakin Mahaifiya; Iyalinsa (Mata Da Ƴaƴa) Abokanai, Dalibai, Malamansa Da Sauran Al'umma. Malam Aminu Mutum Ne Wanda Ta Fannin Mu’amala Sai Dai A Zalunce Shi Ya Yafe, Amma Ba Dai Ya Zalunci Wani Ba.Sannan Ba Ya Saɓa Al'Ƙawari, Sai Dai Shi A Sa Ɓa Masa Haka Kuma Baya Cin Zarafin Al’umma, Sannan Ya Yarda Ya Fanshi Farin Cikin Abokin Mu’amalarsa Da Nasa Farin Cikin. Ɗalibansa Kuwa Sun Yi Masa Shaida Wajen Yawan Hakuri, Uwa Uba Yawan Nasiha Musamman Akan Al’amarin Da Ya Shafi Karatu.

Malam Aminu Ya Sami Kyakkyawar Shaida Akan Iya Mu’amalarsa Da Jama’a, Tun Daga Kan Abokanansa Na Yarinta Har Zuwa Girman Sa.

SHAIDU AKAN SHAHEED MALAM AMINU:

Haƙiƙa Mallam Aminu Ya Sami Kyakkyawar Shaida Daga Bakin Al’umma, Waɗan Da Su Ka Sanshi A Rayuwarsa. Duk Da Ya Samu Yabo Da Daman Gaske, Sai Dai Za Mu Takaita Da Tsakuro Wasu Daga Cikin Shaidun Da Al’umma Suka Yi Masa A Tsawon Rayuwarsa.Malam Aminu Ya Sami Shaida Daga Bakin Mahaifiyarsa Mai Tsarki, Inda Take Cewa “Babu Abinda Zan Ce Ga Aminu, Sai Dai ALLAH (T) Ya Saka Masa Da Alkhairi, Domin Duk Cikin Ƴaƴana Ba Ni Da Tamkarshi”.

Matsarsa Ta Farko Kuwa Cewa Ta Yi “A Tsawon Shekaru Ashirin Da Biyu Da Muka Yi Da Malam Aminu, Ba Mu Taɓa Yin Faɗa Dashi Ba. Haka Ma Tsakaninsa Da Ƴaƴansa Babu Wata Matsala. Hakama Ƴan uwansa Duk Sun Yabeshi A Kan Kyakkyawar Alaka Tare Da Kau-Da-Kai Ga Duk Wani Abu. Kuma Ba Shi Da Abokin Faɗa. Hatta Makwabta Ma Sun Shaideshi Akan Yawan Hakuri Da Son Zaman Lafiya.

Shaida Daga Bakin Ɗan’uwansa Kuwa ? Cewa Ya yi “Samun Kamar Malam Aminu A Cikin Mu, Lallai Abu Ne Mai Wuya, Domin A Gaskiya Babu Wanda Zai Ji Abinda Ya Faru Da Malam Aminu Face, Ya Jajinta Kuma Ya Faɗi Kalmomi Na Yabo A Kansa”.

Abokinsa Kuwa (Malam Sabit Khalid) Cewa Ya yi “Shahadar Mallam Aminu Abin Alfaharin Mu Ne, Domin Kowa Ya Yi Masa Shaidar Cewa Ya Tsaya Ƙyam Akan Tafarkin ALLAH. ALLAH (T) Ya Karbi Shahadarsa Ya Kuma Yi Wa Zuri’arsa Albarka”.

Ɗansa (Hamza Aminu) Ya Faɗi Dangane Da Mahaifinsa Cewa:- “Shi Mahaifinmu Mutum Ne Da Ya Kasance Mai Sadaukar Da Lokacinsa Ga Harka, Sannan Duk Wani Abu Da Ace Za’ayi To Zaka Ganshi A Wajen. Domin Bada Tasa Gudummawar, Ya Na Yawan Yi Mana Nasiha, Akan Mu Dage Wajen Karatu. Sannan Ya Kan So Ya Gan Mu Ko Da Yaushe, Karatu Muka Tasa A Gabanmu. Kuma Ina Son Na Gaji Mahaifina Ta Ɓangaren Kyawawan Ɗabiu Da Sadaukarwa Ga Addini.

A Lokacin Da Labari Ya Riski Al’umma Cewa Ba’a Ga Malam Aminu Ba, Kowa Cewa Yake; Haƙiƙa An Rasa Gurbin Da Samun Makwafinsa Babban Al’amarine, Musamman Ta Ɓangaren Harisanci.

DARUSSA DAGA RAYUWAR SHAHEED AMINU:

Haƙiƙa Dukannin Rayuwar Malam Aminu Babu Abinda Yake Ba Na Koyi Bane.
Musamman Ta Ɓangaren Haƙurinsa: Matarsa Ta Biyu Ta Bayyana Cewa: "Lallai Mallam Aminu Mutum Ne Mai Yawan Hakuri, Domin Kuwa Tsawon Shekaru Sha Biyar Da Suka Yi A Rayuwarsu Ba Ta Taɓa Ganin Ɓacin Ransa Ba.

IBADARSA:
Babu Bukatar Tsawaita Dogon Zance Akan Yawaita Ibadar Malam Aminu Ga Dukkanin Wanda Ya Yi Masa Sani Na Haƙiƙa. Domin Kuwa Matarsa Ta Furta Cewa, “Kullum Akowana Dare Malam Aminu Yakan Tashi Ya Yi Ta Salloli Da Karatun Alqur’ani, Har Zuwa Asubahi. Idan Kuwa Watan Ramadan Ya Shiga, To Ya Yi Sallama Da Barci Kenan Cikin Dare. Kuma Daga Cikin Baiwar Da ALLAH (T) Ya Yi Masa Shi Ne Yana Karatun Alqur’ani Ko Addu’oi Yana Kuka, Domin Wani Lokacin Na Kanyi Tunanin Ma Ko Yana Cikin Wata Matsalar Ce.

YAWAITA KARATUN QUR’ANI:
Tabbas Ko Shakka Babu Malam Aminu Yana Da Matukar Yawaita Karatun Alqur’ani Musamman Da Watan Ramadan Dukkanin Daliban Fudiyya Zasuyi Shaida Akan Hakan Domin Ba Abu Ne Da Ya Ɓoyu Ga Kowa Ba.

SADAUKARWA GA ADDINI:
Babu Kalmar Da Za’a Yi Amfani Da Ita, Wajen Kamanta Sadukarwar Malam Aminu. Domin Kuwa In Har Al’amarine Na Aikin ALLAH (T), Sau Da Yawa Ya Kan Ajiye Uzirinsa. Domin Gabatar Da Aikin ALLAH (T) Lallai Malam Aminu Babban Abin Koyi Ne Ga Al’umma, Ta Wannan Ɓangaren.

KARFAFAWA GA NEMAN ILIMI:
Malam Aminu Baya Gazawa Wajan Yiwa Al’umma Nasiha Akan Neman llimi. Musamman Ga Yara Daliban Fudiyya Yakan Yawaita Kwadaitarwa Akan Muhimmantar Da Karatu. Domin Sayyid (H) Ya Yi Alfahari Da Mu Sannan Mu Zamo Jigon Wannan Al’umma Sannan Yakan Yawaita Tunatarwa Akan Yin Kowane Irin Aiki Domin Neman Yardar ALLAH (T).

SHAHADARSA:

Malam Aminu Ya Yi Shahada Ne A Ranar I Ga Watan Rabiyul Auwal 1436 = 12/12/2015. Kamar Yadda Muka Ambata A Baya Sakamakon Harin Ta’addancin Da Sojojin Nigeria, Ƙarƙashin Tukur Yusuf Burtai. Bisa Umarnin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Suka Kai A Husaniyya, Da Gidan Sayyid Zakzaky (H) Dake Gyallesu. Sanadiyyar Hakan Ya Sanya Tun Daga Lokacin Babu Labarin Malam Aminu Babu Tabbacin Shahada Ko Rayuwarsa.Malam Aminu Ya Yi Shahada Ya Bar Mata Biyu Hannatu Aminu, Da Rashida Aminu. Sannan Ya Bar Ƴaƴa Biyar, Maza Hudu Mace Ɗaya.

  1. Auwal
  2. Hamza
  3. Ja’afar
  4. Abu-Dalib.
  5. Narjis.

Amincin Allah (T) Ya Kara Tabbata A Gareka Ya Shahid Malam Aminu Aliyu (Magaji), Ranar Da Aka Haifeka Da Ranar Da Aka Shahadantar Da Kai Da Ranar Da Za Ka Tashi A Gaban Ubangijin Ka, Matsayin Abin Zalunta (Mazlumi) Kana Mai Arziƙi A Gareshi.

Post a Comment

0 Comments