Shahid Ammar Sani

Shahid Ammar Sani Takaitaccen Tarihin Shaheed Ammar Sani
SUNANSA:

Ammar, Sunan Mahaifinsa Muhammad Sani, Sunan Mahaifiyarsa Khadija.

Shaheed Ammar Yana Daya Daga Cikin Yan uwan Da Har Zuwa Yan Zu Ba Bu Labarinsu Sakamakon Harin Ta’addanci Da Sojoji Yan-Ina-Da-Kisa Suka Kai Husainiya Zaria, Da Gidan Shaikh Zakzaky (H) Dake Gyallesu. Karkashin Jagorancin Tukur Yusuf Burtai, Bisa Umarnin Gwamnatin Nigeria, A Ranar 12 Da 13 Ga Watan Disambar Shaikara Ta 2015.

An Haifi Shahid Ammar Dan Kimanin Shaikaru 20 Acikin Garin Kudan Dake Jahar Kaduna Ta Nigeria. Ya Yi Karantunsa Na Primary A Cikin Garin Kudan A Makarantar ‘Model Primary School Kudan. Daga Bisani Ya Dora Da Secondary School A Garin Na Kudan A Makarantar ‘Government Junior Secondary School Kudan. Shahid Ammar Ya Kammala Matakin Farko Na Karatun Secondary Ma’ana (Junior Section), Sai Dai Bai Samu Damar Dorawa Ba Zuwa Matakin Na Gaba (Senior Section) Domin a Daidai Lokacin Ne ALLAH (T) Ya Nufe Sa Da Samun Babban Rabo Na Shahada. Ta Bangaren Karatun Addini Kuwa Ya Yi Karantunsa Ne A Makarantar Fudiyyah Ta Kudan Da Kuma Wajen Mal. Sabitu Khalid Tun Daga Tasowarsa Har Zuwa Lokacin Shahadarsa.

MU’AMALAR SA DA AL’UMMA:

Ta Fannin Zamantakewa Shahid Ammar Ba Shi Da Aibu. Domin Kowa Ya Shaidesa Da Kyakkyawan Zamantakewa. Lallai Da Ace Za’ayi Koyi Da Dabi’unsa, Wajen Mu’amala, Hakika Da Al’umma Ta Zauna Lafiya. Domin Kuwa Sanin Kowane Allah (T) Ya Yi Wa Shahid Ammar Baiwar HaÆ™uri, Da HaÉ—iye Fushi, Ga Yawan Uzuri Ga Dukkanin Al’umma.
“Iya Zamantakewar Shahid Ammar Da Al’umma Ne Ya Sanya Kowa Ya Zama Nashi Maza Da Mata. Yara Da Manya, Har Wani Lokaci An Taba Tambayarsa Cewa; Kai Naga Dukkanin Jama’a Ma Kowa Naka Ne, ? Sai Yake Cewa: "To Meye Amfanin Rayuwa Alhalin Jama’a Najin Tsoronka?)” – Inji Abokinsa Mahdi Hamza.

“Ya Kasance Ko Da A Cikin Aji Ne Za Ka Samu Kowa Ma Abokin Shahid Ammar Ne Kyauta Da Yawan Hakurinsa Ne Ya Sanya ALLAH (T) Yayi Masa Farinjini. Ya Zama Na Kowa Yana Kaurar Zama Dashi A Matsayin Abokin Rayuwa” – Cewar Abokanansa.

Ga Duk WaÉ—anda Suke Mu’amala Da Shahid Ammar Sun Sani Cewa Baya Iko Da Dukkanin Abinda Ya Mallaka Yakan Saki Ne Ga Kowa. Domin Amfani Baki Daya, Wani Lokacin Ba’a Iya Gane Cewa Abu Kaza Shine Ya Mallakeshi Sai Dai Idan Wani Ne Ya Fadi Hakan Domin Kuwa Mafi Yawancin Lokuta Wasu Ne Ke Amfanuwa Da Kayansa Fiye Da Shi.

SHAIDU AKAN SHAHID AMMAR:

A Maganar Gaskiya, Shaidun Da Shahid Ammar Ya Samu, Sun Fi Karfin Mu Zayyana Su A Wannan Dan Karamin Littafin. Sai Dai Mu Ambata Kadan Daga Cikin Su.

Mahaifin Shahid Ammar Muhammad Sani Ya Bayyana Mana Cewa: "Lallai Shahid Ammar Ya Samu Kalmomin Yabo Daga Bakin Al’umma Dangane Da Rayuwarsa".

ÆŠan’uwan Sa BaÆ™ir Kuwa Cewa Ya Yi “Lallai A Iya Tasowar Da Suka Yi Da Shahid Ammar Ba Shi Da Wani Abun Aibu Da Zai Iya Kiyayewa A Rayuwar Shahid Ammar, Domin Dukkanin Rayuwarsa Ta Damfaru Ne Da Kyawawan Dabi’u, Musamman Ta Fuskacin Biyayya Ga Iyaye Da Girmama Al’umma, Yara Da Manya. Domin Duk Makota Kowa Zai Yi Shaidan Hakan Akan Shahid Ammar Sani”.

“Da Ace Ko Wane Dan Fareti Zai Zamo Tamkar Shahid Ammar Wajen Dagewa Dayin Aiki Ba Tare Da Kasala Ba To Da Lallai Munfi Hakan Sosan Gaske”. Cewar Malam Aminu Ibrahim (Wanda Ke Kula Da Yan Fareti).

Sanin Kowane Dan Fareti Ne Cewa Shahid Ammar Jarumin Gaske Ne Ta Kowanne Janibi, Domin Banda Ma Fareti Ko Da Wani Aikin Ake Yi Na Jiki Zaka Same Shine A Gaba, Kwata-Kwata Bashi Da Kasala. Kokarinsa Ya Sanya Aka Sanya Shi A Gaba "Mai Rike Tuta" A Sahun Yan Fareti.

Rashin Tsoronsa Kuwa Yana Daga Cikin Dalilin Shahadarsa. Domin Kuwa, A Lokacin Da Sojoji Suka Harbi Shahid Aqeel Shine Ya Tsaya Yana Kula Dashi. Duk Da Kuwa Sauran Yan uwa Kowa Ya Tafi Ya Bar Shi A Kwance, Sakamakon Yadda Aka Ga Sojoji Suna Zuwa Wajen, Tare Da Harbin Bindiga, Amma Sai Shahid Ammar Yace “Nifa Koda Ma Meye Zai Faru, To Lallai Ba Zan Tafi Na Bar Dan uwana A Cikin Wannan Mawuyacin Halin Ba”.Wannan Itace Kalmar Karshe Da Shahid Ammar Ya Furta Ga Abokanansa Da Suke Tare Kuma Hakan Aka Yi Duk Sauran Suka Tafi Suka Bar Shi Shi Kadai Tare Da Shahid Aqeel Yana Kula Da Shi Har Sojoji Suka Karasa Inda Suke. Wanda Tun Daga Wannan Lokaci Ba’a Kara Ganin Shahid Aqeel Da Shahid Ammar Ba.

DARUSSA A RAYUWAR SHAHID AMMAR:

Bayanan Da Suka Gabata A Baya Dangane Da Shahid Sun Wadaci Mai Karatu Ya Fahimci Cewa Baki Daya Rayuwar Shahid Ammar Abin Koyine.

Kamar Yadda Mahaifinsa Yake Cewa: “Shi Shahid Ammar Zai Yi Wuya Ka Iya Taskace Rayuwarsa Kace Ga Iyakan Kyawawan Halayensa, Sai Dai Za Ka Samu Ya Fi Karfi A Wasu Bangaren".

Yafiyar sa:
Ta Janibin Yafiya Kuwa. Samun Mutum Tamkarsa Lallai Sai An Bincika. Don Kuwa Bana Mantawa Wata Qissa Data Faru Akansa: Akwai Wani Lokaci Da Ya Sayi Wata Waya Mai Tsadar Gaske Da Niyyar Yin Amfani Da Ita, Amma Kwata-kwata Wayar Bata Dade A Hannunsa Ba, Sai Aka Sace Masa Wayar, Sai Ya Kasance Mu Abokanansa Muna Tayasa Jaje Sannan Muna La’anta Barawon Amma Shi Shahid Ammar Kuwa Cewa Ya Yi “Ku Daina La’antarsa Don Kuwa Ni Wallahi Tausayi Ma Yake Bani (Barawon) Yanzu Ace Ya Kasa Neman Arzikinsa, Ta Hanyar Halal Sai Ta Hanyar Haram. Idan Na Tuna Da ALLAH (T) Zai Yi Masa Hukunci Sai Naji Tausayinsa A Zuciyata. Fatana Dai ALLAH (T) Ya Shiryeshi Ya Kuma Yafe Masa.

Kyautarsa:
Tabbas Shahid Ya Yi Fice Ta Wajen Yin Kyauta Da Dukkanin Abinda Ya Mallaka Domin Kuwa Rowa Bashi Daga Cikin Halayyarsa, Yakan Kyautar Da Abinshi Ga Wanda Yaga Ya Fishi Buƙata Koda Kuwa Ba Shi Da Halin Kara Siyan Wani.

Hakurinsa:
Ta Fannin Hakuri Kuwa, Duk Mutanen Gidansu Babu Wanda Ya Ke Shakkar Wannan, Domin Kuwa Hakurinsa Ne Ma Ya Sanya Bashi Da Abokin Fada A Duk Cikin Unguwa, Da Wajen Unguwarsa.

Abokanansa Za Su Yi Shaidar Cewa:
Shahid Ammar Tun Daga Tasowarsa, Ya Taso Ne Mai Tsantsar Hakuri Da Yafiya, Ga Dukkanin Laifin Da Akayi Masa. Kuma Har Zuwa Lokacin Shahadarsa Ya Tafi Ne Da Wannan Hali Na Yawan HaÆ™uri, Da Tausayi, Da Yafiya Ga Al’umma.

Sadaukarwarsa:
Idan Muka Ce Za Mu Yi Bayani Dangane Da Sadaukarwar Shahid Ammar To Lallai Littafi Guda Za Mu Rubuta Na Musamman Dake Magana Akan Wannan Bangare. Ko Da Yake Sadaukar Da Rayuwarsa Ga Addini Ma Ta Wadatu Ta Zama Hujja Akan Al’umma Cewa Shi Mai Tsantsar Sadaukarwa Ne.

Rayuwa Itace Abu Mai Tsada Ga Dukkanin Mutum Ko Aljan. Amma Duk Da Haka, Shahid Ammar Ya Dauketa Kacokam, Ya Sadaukar Da Ita Ga ALLAH (T) Domin Ya Gwammace Ya Sadu Da ALLAH (T) Cikin Aminci Akan Ya Ci gaba Da Rayuwar Da Ba Shi Da Tabbaci A Ranar Lahira.

SHAHADARSA:

Shaheed Ammar, Ya Yi Shahadane A Ranar Lahadi A Gidan Sayyeed (H) Dake Gyallesu Sakamakon Harin Ta’addanci Da Sojojin Nigeria Suka Kai Akan Yan uwa Musulmi Almajiran Sayyeed Zakzaky (H) A Husainiya Zaria Da Gidan Shaikh Zakzaky Dake Gyallesu A Ranakun 12, 13 Da 14 Ga Watan Disambar Shaikara Ta 2015.

Amincin Allah (T) Ya Kara Tabbata A Gare Ka Ya Shahid Ammar, Ranar Da Aka Haifeka Da Ranar Da Kayi Shahada, Da Ranar Da Za Ka Tashi A Gaban Ubangijnka Kana Matsayin Mazlumi Mai Arziki A Garesa.

Post a Comment

0 Comments