Takaitaccen Tarihin Shaheed Akilu Aliyu
SUNANSA:
Aqeelu, Sunan Mahaifinsa Alhaji Aliyu, Sunan Mahaifiyarsa Rahinat.
Shahid Aqeel Ya Na Daya Daga Cikin Yan uwan Da Har Zuwa Yan Zu Ba Bu Labarinsu. Sanadiyyar Harin Ta’addanci Da Sojojin Nigeria Suka Kai Husainiya Zaria Da Gidan Sayyid Zakzaky (H) Dake Gyallesu Bisa Umarnin Shugaban Kasa General Muh’d Buhari, A Ranakun 12 Da 13 Ga Watan Disambar Shaikara Ta 2015.
An Haifi Shaheed Aqeel Mai Kimanin Shaikaru 19 Kafin A Cikin Garin Kudan, Dake Jahar Kaduna Ta Nigeria. Yayi Karatunsa Na Primary A Makarantar ‘Model Primary School Kudan’ Dake Cikin Garin Kudan, Daga Bisani Ya Dora Da Karatunsa Secondary A Makarantar ‘Government Junior Secondary School Kudan’ A Cikin Garin Kudan. Ta Bangaren Karatun Addini Kuwa Ya Yi Karatunsa Ne A Fudiyyah Kudan A Bangare, Qur’ani, Fiqhu Da Sauran Bangarori. Shaheed Aqeel Ya Kammala Matakin Farko Na Secondary Ma’ana (Junior Section) Yana Shirin Fara (Senior Section) Ne Kuma Sai ALLAH (T) Yayi Nufinsa Da Alkhairih.
MU’AMALAR SA DA AL’UMMA:
To, Kowa Dai Ka Tambaya Dangane Da Zamantakewansa, Sai Ka Ji Babu Abin Da Yake Fadi Sai Alkhairi Tun Daga Yara Abokanai Da Kannai Har Zuwa Kan Manyan Mutane. Domin Kuwa An Yi Shaidar Shahid Aqeel Da Kyawawan ÆŠabi’u. Ta Bangaren Zamantakewa, Da Kokarin Kyautatawa Al’umma. Gashi Mutum Ne Wanda Bai Son Yawan Surutu Koda Yaushe Zaka Sameshi Cikin Natsuwa, Hakan Ya Sanya Al’umma Ke Son Kusantarsa, Musamman Ma Kananan Yara.
SHAIDU AKAN SHAHID AQEEL:
Ko Shakka Babu Shahid Aqeel Ya Samu Kyakkyawan Shaida, Daga Bakin Al’umma. Don Kuwa Mahaifiyarsa, Ta Shaida Cewa: “Shahid Aqeel Babu Wani Abu Da Za Ka Kusa A Cikin Rayuwarsa. Ko Wane Janibi Ya Na Da Abin FaÉ—i Kyakykyawa. Hakan Ya Sanya Ba Ta Ma San Mai Za Ta Dauka Ta Fada Acikin Rayuwarsa Ba Domin Komi Nasa Abu Ne Mai Kyau”.
ÆŠan’uwansa Kuwa Baqir A Lokacin Da Aka Tambayeshi Cewa Ya Yi “A gaskiya Ni Ban San Abinda Zan FaÉ—a Dangane Da YaÆ´ana Ba, Domin Shi YaÆ´ana Mutum Ne Mai Saukin Kai Ga Wanda Ya Fahimceshi, Haka Ya Sanya Gaba Daya Rayuwarsa Ta Zamo Abin Koyi A Garemu Domin Kuwa A Duk Lokacin Dana Tuno Dashi Musamman Ta Bangaren Kyautatawa Na Kara Fahimtar Lallai Nayi Rashi”.
Abokansa Na Fudiyya Wadanda Suke Fareti Tare Cewa Sukayi Lallai An Yi Rashin Babban Jigo Wanda Ba Shi Da Kasala, Wajan Aiwatar Da Abubuwa. Gashi Mutum Ne Wanda Ba Shi Da Tsaro, Wajen Kokari Da Sadaukarwa Da Ganin An Sami Nasara Wajen Aiwatar Da Duk Wanin Aiki Na Alkhairi.
DARUSSA A RAYUWAR SHAHID AQEEL:
Kamar Yadda Aka Ambata A Baya Cewa Gabaki Daya Rayuwar Shahid Aqeel Abin Koyi Ne Ga Al’umma Musamman Ta Fuskacin Kyautarsa Kamar Yadda Mahaifiyyarsa Ta Shaida Cewa “Lallai Shi Shahid Aqeel ALLAH (T) Ya Yi Masa Baiwar Kyauta Musamman Ma Ga Kananan Yara. Domin Wani Lokacin Ko Da Unguwa Na Je Idan Na Dawo Akan Shaida Min Cewa: Aqeel Ya Ba Wane Da Wane Kaza”.
Ta Bangaren Hakuri Kuwa Ba’a Magana, Domin ALLAH (T) Ma Shaida Ne, Akan Yawan Hakurin Shahid Aqeel. Don Kuwa So Da Yawa Akan Yi Masa Laifin Da Yana Da Damar Ramawa Ko Daukan Mataki. Amma, Kawai, Sai Ya Dauki Matakin Hakuri. Wani Lokacin Ko Da An Yi Masa Wani Laifin, Sai Dai Kawai Ya Yi Wa Mutum Murmushi Ya Wuce Ba Tare Da Ya Dauki Wani Hukunci Mai Muni Ba.
Sadaukarwarsa Kuwa Babu Bukatar A Yi Wa Al’umma Bayanin Hakan Domin Kowa Zai Yi Shaida Akan Haka. Ko Aranar Da Za Su Tafi Zaria (Ranar WaÆ™i’a) Shi Ne Ya Dunga Karfafar Abokanansa. Duk Da Kuwa A Lokacin Basu Da Wadatattun Kudin Da Zasu Shigar Dasu Zaria. Amma Haka Ya Je Gida Ya Samu Wasu Yan KuÉ—i Ya Zo Aka HarhaÉ—a Har ALLAH (T) Ya Taimakesu Suka Isa Gyallesu Gida Sayyid (H).
A Ranar Shahadarsa Ya Furta Wasu Kalmomi Masu Ratsa Jiki Da Nuna Sadaukarwa, Inda Ya Ke FaÉ—i Ga Abokansa Cewa: “Lallai Yau Ce Ranar Da Za Mu Cika Alkawari, Domin Ba Zamu Taba Kyale Wadannna Tsinannun, Su Kai Ga Shugabanmu Ba. Alhali Ruhinmu Yana Tare Da Gangar Jikin Mu”. Haka Ya Jagoranci Abokanansa, Wani Tsinanne Sojane Ya Saita Shi Da Bindiga Ya Harbe Shi A Gefen Cikin Sa.
SHAHADARSA:
Shahid Aqeel Ya yi Shahada Ne A Ranar Lahadi 13/12/2015 A Gyallesu A Gidan Sayyid Zakzaky (H). Sakamakon Harbin Bindaga Da Sojoji Suka Yi Masa A Gefen Cikinsa Ta Bangaren Dama. A Ranar Lahadi Lokacin Da Sojojin Suka Kai Harin Ta’addanci A Gidan Sheikh Zakzaky (H) Dake Gyallesu Bisa Umarnin Gwanmatin Kasa.
Shahid Aqeel Ya Yi Shahada Ya Na Dan Kimanin Shaikara 19 A Duniya, Kuma Shi Ne Da Na Uku A Wajen Mahaifansa. Sannan Ya Na Matakin Gaba Da Firamare Ne A Karatunsa.
Amincin ALLAH (T) Ya Kara Tabbata A Gareka Ya Shaheed Aqeel, Ranar Da Aka Haifeka, Ranar Da Aka Kasheka (Ranar Shahadarka) Da Ranar Da Zaka Tashi A Gaban Ubangiji Kana Mazlumi Sannan Mai Arziki A Garesa.
0 Comments